2023: Kwankwaso ba barazana ba ne ga APC -- Lukman 

2023: Kwankwaso ba barazana ba ne ga APC -- Lukman 

2023: Kwankwaso ba barazana ba ne ga APC -- Lukman 

Jam'iyar APC mai mulki ta bayyana cewa ɗan takarar shugabancin ƙasa a jam'iyar NNPP, Rabi'u Musa Kwankwaso ba ya gaban ta a zaɓen 2023.

Dakta Salihu Lukman, mataimakin shugaban jam’iyyar APC na kasa, shiyyar Arewa-maso-Yamma, ya kuma ce jam’iyyar NNPP  ba barazana ce ga APC ba a zaɓen 2023.

Lukman, wanda kuma tsohon Darakta-Janar ne na Kungiyar Gwamnonin APC, PFG ya bayyana haka lokacin da ya ke zantawa da manema labarai a jiya Talata a Abuja.

Sai dai ya ce jam’iyyar APC za ta yi aiki tukuru don ganin ta samu nasara a zaɓen na 2023 domin ba ta daukar wani abu da wasa.

Lukman ya ƙara da cewa bambancin da ke tsakanin APC da PDP da sauran jam’iyyun siyasa shi ne yadda jam’iyyar ke da ɗumbin mabiya a tsakanin al’umma.

“Ta bayyana karara cewa banbancin da ke tsakanin APC a 2015 da Kwankwaso a 2023 shi ne cewa APC ta shiga zuƙatan mutane.

“Kuna iya gani da kanku, amma a ɓangaren sauran jam’iyyu, ciki har da PDP, suna fata kuma suna jiran mu samu wani naƙasu sai su yi amfani da wannan dama.
 
“Yanzu, gaskiyar magana ita ce, ba mu ɗaukar komai da wasa, ba ma korar mutane kuma za mu yi aiki tukuru,” inji shi.