Sanata Ya Nuna Farincikinsa Kan Buhari Bai Sanyawa Dokar Kato Bayan Kato Hannu Ba

Sanata Ya  Nuna Farincikinsa  Kan Buhari Bai Sanyawa Dokar Kato Bayan Kato Hannu  Ba

Sanata Abdullahi Adamu mai wakiltar Nasarawa ta Yamma a majalisar dattija a wannan Laraba ya nuna farincikinsa kan shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya ki sanya hanna ga sabuwar dokar zabe da aka yi wa gyaran fuska, wadda za ta sa a yi zaben kato bayan kato.

Adamu ya fadawa manema labarai a Keffi cewa majalisar dokoki ta tarayya  ba ta da wani muhalli na samar da doka kan yanda jam'iyyu za su yi zaben fitar da 'yan takararsu.

"Ina kallon hakan bai dace ba a samar da dokar da za ta tsarawa jam'iyyu yanda za su yi zabensu.

"Ina goyon bayan shugaban kasa kan kin saka hannu, mun godewa Buhari kan hobbasar, mutum ne da ya san abin da yake yi," A cewarsa.

Abdullahi wanda shi ne shugaban kwamitin harkokin gona a majalisa ya ce ya aminta da hujjojin da shugaban kasa ya zayyano da suka hana shi sanya hannu.

Ya ce da yawan mutane sun gano gaskiya kan haka zai sa da wuya a samu biyu bisa ukun 'yan majalisa da za su amince a tabbatar da dokar in aka dawo hutu.

"Jam'iyyu na da ka'idoji da sharuddansu da mambobin jam'iyya suka aminta da su"

A cewarsa rashhin adalci ne kai ba dan jam'iyya ba amma kuma za ka kawo mata ka'idojin gudanarwa.