Bai dace a dinga ɓata sunan Fulani ba  – Gwamna Yusuf

Bai dace a dinga ɓata sunan Fulani ba  – Gwamna Yusuf

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ce ɓatanci da ake yi wa Fulani a fadin kasar bai dace ba.

Gwamnan ya bayyana hakan ne lokacin da ya karbi bakuncin tawagar kungiyar Tabital Fulaku  ta reshen Kano.

Gwamnan, wanda ya samu wakilcin, Mataimakinsa , Aminu Abdussalam Gwarzo, ya sake tabbatar da kudirin gwamnatin jihar na mara wa kungiyar Tabital Fulaku  baya wajen hada kan al’ummar Fulani a fadin kasa.

Haka kuma, ya yi kira ga shugabannin Fulani su ci gaba da jajircewa wajen bai wa matasa jagoranci mai kyau, tare da jaddada muhimmancin goyon bayansu da jagorancin su ga al’umma.

Gwarzo ya nuna damuwa kan batanci da ake yi wa Fulani a wasu kafafen yada labarai, duk da irin gudunmawar da suke bayarwa wajen ci gaban Najeriya.