ƘADDARA TA: Fita Ta Shida
ƘADDARA TA:
Na
*Jiddah S Mapi*
*Chapter 6*
~Har aka fara shirye shiryen bikin babu wanda ya kara ɗago maganan, aneeta kam batama fita su zauna bale magana yayi nisa, kwance take akan gado dare ne kowa na bacci banda ita da take da tarin tambayoyi dayawa a kanta amma ta rasa wa zata yiwa, minat bata bata amsa koda ta mata tanbayan, shiru tayi sanye take da kayan bacci me kyau dogon riga silk, kasancewar silk yasa yake mannewa a jikinta sosai duk shape nata suka bayyana, net ne a wuyan rigan hakan yasa saman kirjinta da yake fari tas ya fito sosai, gashinta dake cikin net ta cire net ɗin sabida zafi sosai takeji, ishi ma ta fara ji, a hankali ta kunna wutan ɗakin ta sauke fararen santala santalan kafafunta, fita tayi daga ɗakin tana hamma ga bacci a idonta amma ta kasa yinshi ga ishi har gani take kamar ba zata isa wajen fridge ɗin tasha ruwa ba, wutan a kashe yake, sauka tayi ta buɗe fridge ɗin bayan ta kunna wutan, kashe wutan tayi ta haura stair ta buɗe ruwan zata fara sha, ji tayi an fizge goran, ihu zatayi ya toshe bakinta ya mannata da jikin bangon, idanunta kamar zasu zubo tsaban firgita, bakinshi yasa a wuyanta yayi mata sassanyar kiss, ta hanyan numfashinshi ta gane shi, ajiyan zuciya ta sauke, hanunta ya rike yana murzawa a hankali kuma yake kissing wuyanta, tureshi tayi tace "ka tsorata ni yarima"
murmushi me sauti yayi sannan ya kara mannata jikin bangon ta yadda ba zata iya kwacewa ba, jin kiss ɗin yayi yawa tace "sakeni bacci nakeji"
kin sakinta yayi, hanu taji yana sawa ta kasan riganta da sauri tace "kai yarima ka kyaleni"
bakinshi ya haɗa da nata ta yadda ba zatayi magana ba, yadda yaso yakeyi da jikinta sai numfashi yake saukewa a hankali yana samun wani kyakkyawan nutsuwan da rabonshi dashi ya jima, idan yana tare da ita ji yake kamar ya mallaki komai na duniya na jin daɗi, tafiya take da imaninshi musamman idan tasa kayan da yake kama jikinta, hanunshi taji a bayanta yana pressing duk yadda tayi ta kwace ya hanata saima kara mannata yake da bangon kamar zai shige jikinta, so much pleasure yake samu idan yana taɓa jikinta, kaseem da ya tashi cikin bacci sabida ishi ya buɗe fridge nashi baiga ruwa ba sai drinks tsaki yaja yasa slippers ɗinshi ya fita, kunna wutan yayi zai sauka ya gansu, da sauri hameed ya saketa, kamar zatayi kuka ganin ya kaseem a ranta tace "na shiga uku nikam asirina ya gama tonuwa a wajen ya kaseem"
hararan hameed tayi sannan ta juya kamar munafuka ta wuce ɗaki da goran ruwan a hanunta, kallonshi yayi baiyi magana ba ya wuce ya ɗau ruwan ya buɗe yana sha, har yanzu yana tsaye a wajen yana wasa da yatsunshi kanshi a kasa kamar munafuki, aje sauran ruwan yayi ya kama hanya kawai zai tafi, rike hanunshi yayi ya juyo yana kallonshi, hanu biyu yasa ya rike kunnenshi kanshi kasa alaman sorry, tsaki kawai yaja yace "wuce kaje ka kwanta"
a hankali ya tafi zuwa ɗaki, kaseem ɗinne ya rufe mishi kofa yace "bad boy"
Aneeta saida tayi hawayen kunya share hawayen tayi tace "yanzu zai rinka min wani kallo ko?"
da kanta take tambayan kanta, tace "ba zan kara fita ba wallahi bale na haɗa ido da ya kaseem"
da kyar ta samu tayi bacci.
washe gari kin fitowa tayi tana kwance a ɗaki, jin hayaniya a waje yasa tayi saurin tashi domin leka meke faruwa, gani tayi wasu ƴammata guda biyu sun shigo da trolley ɗinsu, sunyi masifan kyau suna kama da alama yaya da kanwa ne, murmushi tayi jin ammi tace "oyoyo yarana yaushe a kasa?"
karamar tace "jiya muka dawo momy tace mana auren ya hameed jibi shiyasa mukazo sai an gama zamu koma school next week"
cikin jin daɗi minat ta rungumesu tace "gaskiya aurennan zaimin daɗi tunda kuna nan, muje ciki"
ammi sai farin ciki take, dakinsu suka shiga tana ganinsu ta fara murmushi kamar ta sansu, ɗayar tace "itace amaryar ya hameed?"
minat tace "yes itace"
murmushi tayi tace "wow she's beautiful"
minat tace "unty Aneeta waɗannan yaran kanwar momy ne amma ta rasu tun da jimawa a hanun dadynsu suke suna karatu a kasar cyprus yanzu ma hutu suka samu ya haɗu da aurenku"
murmushi tayi ta buɗe musu hanu suka rungumeta tace "ya sunanku?"
karamar tace "ni sunana Amnah ita kuma Amrah"
tace "masha Allah sannunku da zuwa"
sakin jiki sukayi suka fara hira kamar dama sun san juna, zuwa sukayi suka gaida me martaba sannan suka dawo suka zauna a falon, ganin babu aneeta minat taje ta kirata fitowa tayi ba dan taso ba suka fara hiran tare, sultan ne ya shigo tareda fadeel da gudu sukaje suka rungumesu cikin jin daɗin ganinsu yace "amnah da Amrah yaushe kukazo?"
sukace "ɗazu"
zama sukayi a falon suka suka fara hira, aneeta ma tana ɗan hira itama tare da ita suke yi, kaseem ne ya shigo da uniform a jikinshi yace "suwa nakejin muryansu kamar ƴan kauyen nan"
dariya sukayi shima sukayi hugging nashi, Aneeta sunkuyar da kanta tayi tana jin mugun kunyanshi, murmushi yayi yace "Amarya harda ke aketa surutun?"
a hankali tace "eh"
janta yayi da hira har ta saki jiki.
hameed bacci yake a ɗaki sai can ya tashi yana sanye da jallabiya ya fito yana murza ido yana yatsine fuska tareda turo bakinshi cikin shagwaɓan ɗaya same mishi jiki, ganinsu Amrah yayi musu smiling sannan ya musu alaman welcome, shi tsoronshi suke shiyasa basa sakewa sosai idan yana waje, kallon Aneeta yayi tayi saurin ɗauke kai tana tuna abinda yayi mata ranan, smiling me kyau yayi sannan ya kalli ya kaseem dake danna waya, ji yayi hankalinshi ya kwanta ganin ya kaseem lafiya lau yana smiling da alama abinda yake a waya me muhimmanci ne.
Minat tace "unty aneeta zamu gyara miki kanki ko?"
gyaɗa kai tayi, tace "muje to sabida me lalle zatazo da dare tayi miki"
tashi tayi jikinta dama ba a sake ba ta bita suka nufi ɗaki, gyara mata tulin gashin tayi sannan da dare akazo aka mata lalle me kyau.
kaya ammi ta siyo mata masu tsada da yawa da kuma kyau sannan ya kaseem yasa aka sauya ɗakin hameed aka kara ƙawatawa da kayan adonsu na sarauta, rana bata karya kamar yadda Abi yasa yaune auren yarima hameed da kuma Aneeta, gidan ya zama busy sai gudanar da biki ake tun yanzu da safe kafin ma a ɗaura, Aneeta tana ɗaki banda kuka babu abinda take yi, saida minat tayi da gaske kafin ta yadda tayi wanka ta fito akayi mata kwalliya me kyau, leshi fari da golding me masifan kyau tasa, fited gown ne ya kama jikinta sosai hakan yasa tasa babban mayafi, mutane sai shigowa suke suna tayata murna, ɓuya tayi dan batason mutane sosai, Amrah wacce take yawan rike waya tace "unty amarya kafin musa kayanmu kizo nayi miki hoto"
murmushi tayi tace "a,a ban iya hoto ba"
tace "please unty"
a hankali ta gyara mayafin ta tsaya me kyau tayi mata hoton, tace "wow kinyi bala'in kyau"
sawa tayi a status sannan ta kashe data a ranta tace "sai anjima zanga comment na mutane akan kyakkyawar matar yayana"
shiryawa suka fara saida sukayi kyau kafin suka fara hotuna duk a wayan Amrah.
Amrah ta zauna a bakin gadon kafin ta canja wani kayan tace bari ta duba watsapp, saura awa ɗaya a ɗaura aure domin an tafi sallan juma'a, message ta gani ya shigo mata voice ne amma da tsayi jin hayaniya a ɗakin yasa ta tashi ta shiga toilet playing tayi tana ji, jikinta ne ya fara rawa ta kara sawa a kunne tana ji ta kara maimaitawa, wayan Amnah ta kira kusan sau biyar bata ɗauka ba sai kuma ta kira wayan minat itama bata ɗauka ba, tsaban rawan da jikinta yake yi ta kasa fita a toilet ɗin, ji tayi ɗakin yayi shiru, fitowa tayi da kyar ta buɗe kofan ta tsaya tana kallon Aneeta wacce take kallonta tana murmushi tayi kyau cikin shaddan data sauya, gani tayi babu kowa a ɗakin sai ita tace "inasu... minat?"
taɓe baki tayi tace "sun fita ammi ta kirasu"
hanyan fita ta kama da sauri ta tsaya a gabanta, gabanta yana faɗuwa tace "meyasa kika tsaya a gabana? ki matsa min na wuce"
murmushin gefen baki tayi tace "naga kinamin wani kallo kin sanni ne?"
tace "ban sanki ba ki matsamin na wuce"
dariya tayi me sauti sannan ta kalli wayan dake hanunta, nuna kanta tayi tace "ANEETA LAWAN LAMBA nice nasan shine abinda aka faɗa miki kike ɓoyewa kinaso kije ki faɗawa su minat ko?"
jikinta yana rawa tace "meyasa kike shirin auren ya hameed?"
dariya tayi sosai sannan ta takaita dariyan fuskanta kamar wacce bata taɓa koda murmushi ba tace "zaki iya zuwa ki faɗawa kowa kamar yadda kikayi niyan tonamin asiri"
juyawa tayi zata fita saida ta bari ta kai bakin kofa kafin tasa igiyan dake gefenta ta harɗe kafanta dashi, waro ido tayi ta zube a kasa, baki ta buɗe zata kwala ihun azaba da raɗaɗi tanada tabbacin ta samu karaya a jikinta, toshe bakinta tayi tace "kina tsammanin bana ankare da ke ne? to ai tunda naga kin ɗaukeni hoto kinsa a status nasan akwai abinda zai faru, kuka naga kin shiga toilet ai nasan da akwai wata a kasa, inaso ki sani aneeta ba sakara bace ta san me takeyi kuma tasan takunta, ki sani wannan auren na shafe shekaru masu yawa ina neman hayan da zan samu a yishi bayan burina ya kusa cika baki isa ki rusamin arana ɗaya ba, da ki tonamin asiri gara na kasheki"
hanu ta haɗa tana rokonta alaman dan Allah ta kyaleta ba zata faɗawa kowa, bakinta ta ɗaure sannan ta sauko da sabon akwatin ta juye kayan a kasa, sata tayi cikin akwatin bayan ta rufe hancinta da bakinta ta ɗaureta ta kulle akwatin ta yadda ko motsi ba zata iya ba bale asan akwai mutum, kallon kofan bayan tayi sannan ta fara jan akwatin, zata fita dashi taji karan kafan mutum, da sauri ta saki akwatin ta kwanta a gado kamar me bacci, minat ce ta shigo tana cewa "laaa unty Aneeta bacci yanzu? ki tashi dan Allah an ɗaura aure yanzu ki fito ayi hotuna gasu Abi a falo"
kamar me bacci taki tashi, bubbugata tayi da sauri ta buɗe ido aɗan firgice tace "na'am"
dariya tayi tace "amarya amma tana bacci ran aurenta? kizo muje ayi hoto"
murza ido tayi sannan tace "to"
sauka zatayi a gadon tace "tsaya na gyara miki makeup ɗin"
gyara mata tayi sannan ta kara mata sabon ɗauri suka fita tare, juyowa tayi ta kalli akwatin sannan ta tura kofan gau, Amrah ta kasa motsi tana jinsu amma babu halin magana, tun tana iya numfashi da kyar har numfashin yazo ya gagareta.
hotuna suka fara Amnah wacce tayi kyau da ankon da sukayi da Amrah ta tsaya a gefen Aneeta akayi hoton tace "ina Amrah ne? tazo ayi hoto"
meenat tace "wallahi ban ganta ba may be ta fita"
Amnah tace "no babu inda taje kin san Amrah bata son yawo"
meenat tace "eh kuma fa hakane bari na dubata a ɗakin Ammi ko tana can"
dubata tayi bata ganta ba ta dawo tace "babu ita muyi hoton may be tana shiri"
cigaba sukayi da hotonsu, har yamma ya fara babu Amrah, amnah zuciyanta ya fara tsinkewa domin wayan Amrah akwai caji kuma ta kira taji a kashe, meenat tace "ki kwantar da hankalinki kin san da ba zata ɓata a wannan fadan ba ko?"
Aneeta fakan idonsu tayi ta koma ɗakin taja akwatin ta fita dashi, jim kaɗan ta dawo tana gyara mayafin tace "naje fesa turare"
Amnah wacce ta damu sosai tace "gaskiya na tsorata amrah bata yawo kuma wayanta a kashe bayan tasa caji?"
meenat ma ta fara damuwa, Ammi data zo yanzu daga fada fuskanta da yanayin damuwa tace "wallahi babu ita nasa an duba ko ina"
Amnah ta ɗaura hanu aka tace "na shiga uku na lalace ina Amrah ta shiga?"
Aneeta ta rike ta tace "karki damu za'a ganta"
hameed wanda ya shigo cikin damuwa tareda su sultan fuskokinsu kaɗai ya isa ya nuna halin da suke ciki, ammi tace "an ganta?"
duk sukace "A,a"
itama ammi zuwa yanzu ta gama tsorata tace "na shiga uku Amrah ina kike?"
kafin ta rufe baki sukaji faɗowan abu daga saman silin, a mugun tsorace sukayi baya ganin Amrah ce ta faɗo kasa kan tiles, jini ne ya fara bin tiles ɗin bakinta ɗaure da ɗankwalin kanta hanunta ma a ɗaure idonta a rufe alaman bata raye tun da jimawa.
Ammi duhu take gani ta zama kamar makauniya sai tattaɓa hanya take, zubewa kasa tayi, da rarrafe ta isa wajen zata taɓata ya kaseem yace "dakata ammi kar kiyi saurin taɓata bari a kira police, a rufe gidan babu me fita sai an gwada hanun kowa"
gaban aneeta yayi wani irin mummunan faɗuwa ji tayi kirjinta kamar zai fashe tsaban tsinkewan rai, ganin kowa ya tsaya babu wanda ya taɓa gawan an fara rufe kofofin gidan ta kalli Amrah dake kwance sannan ta rufe ido, faɗuwa tayi a kanta kamar ta suma, ganin haka kaseem ya dafa kai yace "wayyo Allah shikenan aneeta ta taɓa ta"
Ammi ganin haka ta rungume Amrah kawai ta fara ihu, Amnah kam tana tsaye tana bin kowa da kallo, da masu ihu da masu kuka ita kam batasan ma me take yi ba, tasan dai kawai ta kasa ɗauke idonta daga kan ƴar uwarta abin alfaharinta wato Amrah.
_Jiddah Ce....
08144818849
managarciya