DUHU DA HASKE: Fita Ta 28
DUHU DA HASKE
Na
*Jiddah S mapi*
*Chapter 28*
~Ammi tayi shiru a hankali ameesha tace "meyasa man zai kashe mama? me tayi mishi? dama bai dawo sabida Allah ba ya dawo ne sabida ya aikata wannan mummunan laifin, ko a mafarki banson kara ganin fuskan man"
duk sukayi shiru tana magana tana kuka, yazeed yace "sorry meesha ki daina kukan haka"
tace "ya yazeed mamana fa, mamana ce"
tana kuka tana magana, duk wajen sai share hawaye suke.
haka har akayi kwana bakwai kullum sai yazeed da Abba sunzo momy da hana already suna nan, saida aka shafe addu'a akayi sadaka sannan Abba ya shigo ya zauna akan kujera yana kallon ameesha da take sanye da hijabi kanta kasa tana hawaye, yace "ameesha?"
a hankali tace "na'am Abba"
yace "duk me rai mamaci ne lokaci kawai muke jira, sannan duk wanda ya mutu Allah ya rubuta abinda zai zamo ajalinshi, a kullum cikin wannan duniyan sai anyi mutuwa ko munaso ko bama so sai anyi mutuwa haka kuma sai an haihu, Allah da kanshi yace kowa zai mutu idan lokacinshi yayi kinga babu wanda ya isa ya hana faruwan hakan, ina me baki hakuri da rashin mama da kikayi, amma inaso ki sani kuka ba shine mafita ba a duk lokacin da mutum ya kwanta ya mutu addu'a kawai yake buƙata, mama yanzu addu'a take bukata kukanki zai iya sata cikin matsala"
tace "to baba"
yace "sai magana na biyu bindigan da akayi amfani dashi wajen kasheta kuyi hakuri da abinda zakuji tabbas Abdulrahman ɗan uwanku ne amma da shine ya siyi bindigan yanzu police suka faɗamin sannan sunce zasu kawo receipt da komai na bindigan wanda sunan Abdulrahman ne akai"
kukan ameesha ya karu lokacin da taji wannan maganan, Imran yace "Innalillahi wa inna ilaihiraji'un"
fahad yace "gaskiya ban yadda ba, wallahi ya man ba zai iya kashe mama ba sharri ne wan..."
kafin ya karasa ameesha ta lalumo roban dake gefenta ta wurga mishi, dafa kai yayi "Auchhh kaina"
cikin masifa da ɓacin rai tace "idan ka sake wannan maganan saina ɓata maka rai"
shiru yayi Imran yana kallonta yadda take huci kasan tana cike, a hankali ta tashi tace "ba komai Abba mu koma gida, zan tsaya akan wannan case ɗin har sai an hukunta man akan laifin daya aikata shima ba zai zauna a raye ba"
tare suka fita dasu momy da Abba da hanan da kuma yazeed sun bar baba da ammi Imran da kuma fahad, a hanya sai sharan hawaye take ta kuduri aniyan tsayawa akan wannan maganan da iya karfinta har sai tayi nasara taga an aika man prison anyi mishi ɗaurin rai da rai.
tana zaune akan kujera taga kiran waya a hankali ta ɗauka tace "faruk? ya aikin?"
cikin sanyin murya tayi maganan, yace "madam wai abinda muke gani a tv gaskiya ne an kama Abdool?"
tace "kwarai faruk nima haka nake gani.."
kuka ta fashe dashi faruk yace "kiyi shiru insha Allah komai zai daidaita"
ya katse wayan, murmushi tayi tana share hawayen ta zubawa system nata ido tana kallon Abdool daya haɗa kai da gwiwa yayi shiru sanye da uniform na prisoners blue, tace "sorry sweetheart banso mu kai haka ba amma na rasa yadda zanyi da soyayyanka da yake azalzalan zuciyata, idan na barka watarana zaka gudu ka barni amma idan kana prison zan rinƙa zuwa na sameka mu zauna, hasalima zan iya aikata laifi dan a kaini prison matukar zan zauna da kai, ko a wuya ko a daɗi inason naga kana kusa dani.
washe gari ameesha ta shirya zuwa police station inda abdool yake, tayi kyau sosai cikin atamfa dogon riga da kayan lawyer a jikinta tasa hulan a saman kanta sai tafiya take cike da nutsuwa fuskanta babu annuri ko kaɗan hanunta rike da wani kyakkyawan karamin flask, suna ganinta da uniform suka mata iso, tana shiga ta zauna tace "yallaɓai yaushe za'a tura case ɗin zuwa kotu?"
yace "sai nan da wata ɗaya"
murmushi tayi tace "tom shikenan zan iya shiga na ganshi?"
yace "zaki iya bari wani yayi miki iso, Bala"
bala yazo da sauri
yace "kaita prison wajen Abdool"
binshi take a baya yana gaba suna tafiya sai kallon side na prison ɗin take, ɗakin da abdool yake ya kaita ya buɗe mata ta shiga, abdool yana zaune a kasa ya haɗa kai da gwiwa, a gaba ta zauna kusa dashi cikin sanyin murya tace "man"
kamar a mafarki yaji muryanta, da sauri ya ɗago kai faɗan irin yanayin da yake ciki ma ba zaiyi ba, ya zama kamar ba man ba, murmushi tayi sannan ta share mishi hawayen dake idonshi ta buɗe flask ɗin ta ɗau spoon a jakanta ta ciro ruwa da drink ta aje, ɗibo abincin tayi ta kai bakinshi, a hankali ya karɓa yana ci yana kallonta wasu zafafan hawaye suka fara wanke mishi fuska, kaɗan yaci cikin muryanshi daya dishe yace "na koshi"
tasan man baya jure wahala ko rashin lafiya yake na kwana ɗaya zai zama abin tausayi bale nan prison babu komai banda zafi da sauro da kuma wari, drink ɗin ta buɗe da ruwa ta fara bashi ruwa yasha sosai kafin ta bashi drink ɗin yasha, murmushi tayi mishi ta rufe flask ɗin sannan ta maida goran cikin jakanta duka biyu tace "kasan meyasa nazo har na baka abinci?"
girgiza kai yayi, tace "sabida inaso ka faɗamin gaskiya me mama tayi maka ka kasheta"
da mugun mamaki yake kallonta tace "man na haɗaka da Allah da manzonsa ka taimaki rayuwata kaga ni marainiya ce tun ina karama nake fama da rayuwa ka faɗamin me tayi maka ka kasheta? kaga har chocolate na kawo maka"
buɗe jakan tayi ta ciro mishi babban chocolate tace "ka gani? yazeed ne ya siyamin amma na ɓoye saboda na kawo maka, ka faɗamin me mama tayi maka kaji?"
cikin tsawa yace "wai kinyi hauka ne? bakida hankali ne? taya zan kashe matar data raineni fiyeda yadda uwata ta raineni? taya zan kashe matar da ƴarta take matsayin babbar ƙawata? taya ma zan iya kashe ta?"
cikin ihu tace "bindigan ai sunanka ne akai kaine ka siya sannan voice ɗin da aka turamin ya tabbar kaine"
rasa abinda zaice mata yayi, yace "kin yadda kenan na kasheta?"
tace "na yadda"
yace "shikenan tunda kin yadda"
tace "kuma na rantse da ubangijin annabi adam wannan uniform ɗin dake jikina sai nayi amfani dashi anyi maka hukunci daidai da abinda ka aikata, kasan me man? ada babu wanda nakeso naga fuskanshi kamar kai, amma yanzu babu wanda na tsani ganin fuskanshi kamar kai, kuma inaso ka sani wannan shine karshen abincin da zakaci a rayuwarka"
fita tayi daga wajen kanshi a gwiwa bai kalleta ba amma yana sauraren duk abinda take faɗa mishi masu sa zuciyarshi tana zafi, tana fita ta ciro rapa ɗin dubu ɗaya ta aje akan desk gaban ogansu tace "inaso a hana kowa kawo mishi abinci duk wanda ya kawo kada a bashi, daga yau har ranan da zamuje kotu kada abashi abinci a barshi da yunwa, sai ruwa kawai shima kaɗan zaku bashi, sannan inaso ku hanashi zaman lafiya a kowane mintuna ku rinƙa dukanshi kada ku bari yaji daɗin zama ko kaɗan, yana cikin bacci ku watsa mishi ruwan sanyi kuyi mishi hukuncin da ko munje kotu ba lalle kowa ya ganeshi ba"
tana magana tana hawaye yace "an gama hajiya"
wayarta ta bashi yasa mata number ɗinshi ta kira tace "kayi saving duk sanda kake bukatan wani abu kamin magana"
yace "to hajiya an gama"
fita tayi daga wajen, bata tsaya ko ina ba sai gida.
kusan sati biyu da faruwan hakan bataje gidansu ammi ba, yau kawai ta yanke shawaran zuwa gidansu kafin ta tafi gida, driving take a hankali fuskanta babu walwala gaba ɗaya ta zama shiru shiru, a kofan gidansu ammi ta tsaya ta fito da manyan leda a hanunta, shiga tayi Imran dake kwance yana kallon sama alaman tunani ya tashi a hankali ya karɓa mata ledan, sakin fuska tayi tace "Imran ya kake?"
yace "lafiya ƙalau"
gani tayi ya rame sosai da alama yana yawan tunani ɗauke kai tayi tace "ina mutanen gidan?"
fahad ne ya fito kamar mara lafiya data ganshi saida gabanta ya faɗi, tace "bakada lafiya ne?"
yace "lafiya ƙalau"
ammi da taji muryanta ta turo wheelchair ɗinta ta fito, da sauri ameesha taje wajenta tana taɓa jikinta tace "bakida lafiya ne ammi?"
girgiza kai tayi, zama ameesha tayi akan kujeran tace "wai me yake damunku ne gaba ɗaya kun fita hayyacinku kamar marasa lafiya?"
duk sukayi shiru suna tsoron faɗa sabida sun san halinta tanada hakuri amma idan ranta ya ɓaci batada sauki, Baba daya dawo daga masallaci sanye da jallabiya me kyau yace "ina zaki gansu lafiya tunda sukaje duba Abdoolrahman da abinci aka hanasu shiga sukaki cin abinci, harda uwar tasu taki cin komai sai damuwa sai kuka, duk yadda zanyi dasu suci abinci basa yadda, kawai na hakura nima na daina ci"
kallonshi tayi shima ya rame, kasa ta durkusa tace "ina wuni baba"
yace "lafiya ƙalau tashi ki zauna"
zama tayi, yace "yau sati uku babu me cin abinci a cikinsu munje duba Abdulrahman suka hanamu shiga wani ma a cikinsu cewa yayi ana hana kowa zuwa wajenshi"
ta tsinci kanta da yi musu karya tace "karya ne ko jiyama saida na kai mishi abinci"
a tare suka kalleta, sai taga duk sun fara murna fahad yace "da gaske?"
tace "karya zan maka?"
duk suka fara murna fahad da kanshi ya shiga kitchen ya dafa musu indomie sannan ya juye a babban plate ya kawo musu tsakiyan ɗakin harda Abba suka sauke ammi tare suka fara ci, kallonsu take idonta yana cika da hawaye a ranta tace "kuyi hakuri nayi muku karya amma ban kai komai ba kuma na hana a bashi komai dole saiya fuskanci hukuncin abinda ya aikata"
ledan ta kai musu suka buɗe fruits ne dayawa fahad ne ya yayyanka suka sha dayawa, sai yau suka koshi dam, tace "ammi harda ke a rashin cin abinci?"
murmushi ammi tayi, ita ammi ta gane karya ameesha takeyi kawai ta biyewa su Imran ne sabida kada su kara shiga damuwa, tana gidan har yamma likis kafin ta tafi, a gidan TV aka sanar da ranan zuwa kotu ya kama ranan litinin saura kwana shida kenan, ameesha tana shirya duk wani shaida da tasan bama zata gaji ba idan taje kotu zasu mishi hukunci.
Manal tayi kyau sosai cikin riga da wando na suit tasa farin siririn mayafi a kanta ta fito daga motarta fari dal tana sanye da farin glass, kayan ma fari ne tasa farin takalmi, wayarta ce a hanunta da makullin motan tana tafiya tana hura whistle da bakinta har ta shiga ciki, cire glass ɗin tace tazo wajen abdool, ganin babu abinci a hanunta suka barta ta shiga dan tace musu ita matarshi ce, tana shiga da whistle ɗin bata tsaya da hurawa ba, yana jin haka yasan itace domin itace take yawan hurawa idan tana tafiya, hakan yasa bai ɗago kanshi ba daga kwancen da yake, durkusawa tayi a gabanshi tace "my Abdool"
a hankali ya tashi, saida gabanta ya faɗi ganin yadda ya rame ya fita a hayyacinshi kana ganinshi kasan akwai yunwa a jikinshi, ga azaban da yake sha, idanunshi basa buɗuwa da kyau, cikin yanayin tausayi tace "sorry my abdool kayi hakuri kaji?"
a hankali ya kalleta sai kuma ya rufe ido, rungumeshi tayi tace "sorry my Abdool"
bai mata magana ba dan baida karfin yin magana a wannan lokacin ji yake kamar ana zare mishi rai, kuka ta fashe dashi duk yadda taso yayi magana yaki yi, da haka har ta cinye time ɗinta akace ta tafi, tafiya tayi tana kuka tace "karka damu nima zan aikata laifi saina dawo nan da zama"
da wannan tunanin ta dawo gida,
bayan kwana biyu saura kwana huɗu kenan a shiga kotu tana zaune a gida taji ana knocking, da kanta taje ta buɗe police ta gani tsaye ya bata takadda, ta buɗe taga sammaci daga kotu, gabanta yana faɗuwa tace "me nayi?"
police yace "abdool ya ambato sunanki yace ke yake zargin kin kashe maman ameesha sabida haka kema ana nemanki a kotu zaki iya nemo lawyer sannan ki sani idan baki zo ba har gida zamuzo mu kamaki, idan kuma kika gudu hotonki zaku baza a duniya wanted"
shiru tayi ya hau mashin nashi ya tafi, murmushi tayi tace "nasan dole zai kira sunana amma ai nikam inada lawyer shi kuma fa? waye zai zama mishi lawyer bayan wacce zata iya kareshi itace take tuhumanshi da laifi"
murmushi tayi tace "oh my abdool dole ne kayi rayuwa da manal koda baka so"
kiran barrister fadeel tayi ta mishi bayanin abinda take so da yadda zai kareta a kotu, ya amsa mata da an gama.
Ameesha tana rike da laptop a cinya tana falo hankalinta duk akan laptop ɗin bata kallon kowa da yake wucewa, yazeed ne yazo ya zauna yana kallonta, tace "ya akayi ne?"
yace "ya kika gane nine bacin baki kalleni ba?"
tace "kamshinka da kuma yanayin tafiyanka da kakeyi a natse"
murmushi yayi yace "shiyasa kika ganeni?"
tace "yes" tana magana tana cigaba da abinda take yi, yace "me kikeyi ne yau haka kin zama busy?"
tace "ina son na adana wannan voice ɗinne sannan ta shirya duk shaidu na kafin gobe mu shiga kotu"
shiru yayi yana ganin yadda ta zama wani kala, yace "to Allah ya bada sa'a"
tace "ameen"
momy tazo da cup cike da yellow juice tace "ameesha tun ɗazu bakici komai ba ya kamata kisha koda juice ne"
girgiza kai tayi "momy bana jin...."
sa mata tayi a baki kawai ta fara sha ba dan taso ba, saida ta shanye tas kafin ta cire cup ɗin tace "ban taɓa ganin inda ake aiki ba'aci komai ba"
zama tayi tana kallon laptop ɗin yadda take yin komai, ganin sunan manal tace "ya naga kinsa sunan manal harda itane a case ɗin?"
gyaɗa kai tayi tace "kwarai itama kotu sun kirata da ita za'ayi zaman wai man yace itace ta siyi bindiga da sunanshi, kuma nasan ko karen hauka ne ya cijeshi ba zai taɓa yadda ta siyi bindiga da sunanshi ba, so yake kawai na fara zargin itace ta kashe mama"
momy tace "amma kince tana iya yin komai bakya tunanin ko itace tayi wannan...."
da sauri tace "dan Allah momy kiyi shiru banson wannan maganan kaina zai rabu kashi biyu, nafi son na kai shaiduna kotu babu wani mistake, tunda bindiga da sunanshi shi aka yiwa register babu wanda za'a zarga sai shi"
momy tace "to shikenan Allah ya bada sa'a"
a takaice tace "ameen"
yazeed kam sai kallonta yake.
washe gari da wuri suka shirya domin ameesha ta riga kowa shiri tafiya kotu ne kawai ya rage sai kallon lokaci take, saida taga time yayi tace "muje"
tare duk suka tafi banda momy wacce batada lafiya ciwon ciki, Abba yace ta zauna kawai a gida, a kofan gidansu Imran suka tsaya ta fito sanye da kayan lawyer sannan ta shiga fuska babu annuri ko kaɗan, ammi ta fara gani tayi murmushi kaɗan kawai tace "ina kwana ammi"
gani tayi ammi tana ta kallonta, ɗauke kai tayi, ammi ta ɗaga hanu ta taɓa uniform nata tana murmushi, ta lura a duk lokacin da ammi ta ganta da uniform saita rinƙa taɓawa tana murmushi ta kasa gane me dalilin haka, tana zaune har su Imran suka fito, duk jikinsu babu karfi, suka gaisheta ta amsa sannan tace "zan haɗaku da girman Allah a kotu duk abinda aka tambayeku kada kuyi karya, zan tsayawa mama sai naga an yiwa man hukunci hankalina zai iya kwanciya, kumin alƙawari ba zakuyi karya ba"
sukace "munyi alkwari"
murmushi tayi ta share hawaye tace "dole sai mun karɓi ƙaddara a duk yadda yazo mana"
suma hawaye suke sharewa dan sun san yau shikenan ya man zai barsu, sun san ameesha idan ta dage akan abu saita tabbatar tayi nasara take bari, ammi tana ganin suna kuka ta rinƙa girgiza musu kai alaman su daina kuka, tace "ina baba?"
Imran ne yayi karfin halin cewa "yace zai samemu acan"
ta rike hanunsu tace "muje"
kallon ammi tayi tace "kimin addu'an nasara"
ammi ta gyaɗa mata kai kawai suka fita, motan suka shiga a hankali suka gaida Abba, cikin tausayawa ya amsa yana basu hakuri tareda musu nasiha.
suna shiga kotu ana shigowa da man, duk suka fito suka jera suna tafiya, man layi yake tsaban yunwa da galabaita kana ganinshi zaka san baida lafiya, ya rame sosai yana tafiya da kyar, ɗauke kai ameesha tayi, da zasu shiga ciki kamar zai faɗi da gudu Imran yayi yunkurin tareshi ameesha ta rike hanunshi gam ta yadda ba zai taimaka mishi ba, shiru yayi ya tsaya yana kallon man ɗin har ya faɗi police ne suka ɗagashi suka shiga dashi, fahad kasa daurewa yayi kawai ya fashe da kuka, wani kallo data aika mishi yasa yayi shiru.
Manal itama tayi parking da tsadadden motarta, ta fito cikin material yana jan kasa da takalmi me tsayi, tasa glass nata yau a saman veil nata, tana ganin ameesha tayi wani murmushi me sanyi sannan ta shiga cikin kotu, duk suka shiga, alkali ya shigo barrister fadeel ne ya tashi yace "nine lawyer ɗin manal umar maidawa wacce akayi zarginta"
ameesha ta tashi tace "sunana barrister ameesha nice lawyer ɗin kaina nice na kawo kara"
duk kowa ya kalleta ta koma ta zauna, alkali yace "ina lawyer ɗin wanda ake kara?"
shiru babu magana, ya kara maimaitawa a karo na biyu, shiru babu wanda ya amsa, fara karanta laifin yayi sannan aka fara shari'a, ameesha ce a gaba tana tsaye wajen man wanda ya galabaita tace "voice na wacce ka kashe yana nan za'a sa kotu kowa yaji sannan bindigan da akayi aiki dashi da sunanshi akayi register"
da kyar ya buɗe baki yace "ba nine na siyi bindiga ba"
cikin rashin damuwa tace "to waye ya siyi bindiga da sunanka malam Abdulrahman?"
yace "manal ce"
barrister fadeel yace "ban yadda ba an yiwa wacce nake karewa sharri"
manal tana tsaye itama a wajen tambayoyi fadeel ya fara mata tambaya
"shin zaki iya gaya mana ta ya za'ayi ki siyi bindiga da sunan wani?"
girgiza kai tayi tace "wallahi ban siyi komai ba, hasalima ina rufawa abdool asiri amma kullum sai naji yana waya yana cewa idan taki magana ku kasheta, ku tambayeshi sau uku ina tambayanshi waye kake cewa a kashe, sai yace babu ruwana idan na kara magana ma zai min abinda ba zan taɓa mantawa ba"
Abdool kallonta yake yadda take hawaye tana bada shaida, alkali yace "to ashe barazana kake mata"
girgiza kai yayi yace "wallahi tallahi..."
Ameesha tace "ya mai girma me shari'a bamu zo wannan kotu me albarka domin jin rantse tantse ba munzo ne domin a hukunta wanda yayi laifi tunda an kamashi da hannu dumu dumu"
alkali yace "duba da laifukan da Abdulrahman ya aikata kotu ta yanke mishi hukuncin......"
"A dakata ya mai girma me shari'a"
duk sukayi shiru suka juyo suna kallonshi, baba ne ya shigo rike da takaddu da kuma wani jaka yana rataye dashi a gefen hammata, me shari'a yace "kai kuma waye da zaka shigo mana kotu ka dakatar damu muna tsaka da shari'a?"
baba cikin girmamawa yace "nine baban Abdulrahman wanda ake tuhuma da aikata laifi sannan nine baban ameesha wacce ta kawo kara"
duk kotu akayi shiru sai kallon kallo ake, tarin shaidu ya mikawa alkali yace "wannan sune shaidun da zasu tabbatar Abdulrahman bai aikata komai ba sharri akayi mishi"
Ameesha tana kallon baba yaki kallonta, ya kalli manal da jikinta ya fara rawa, yace "Abdulrahman bai aikata komai ba wannan shaiɗaniyar yarinyar manal itace ta aikata komai kuma ita ya kamata a hukunta ku duba komai yana ciki"
barrister fadeel a fusace ya tashi yace "ya mai girma me shari'a bai kamata abar wani ya shigo kai tsaye ya mika shaidu ba tareda lawyer ba kuma yazo yana kiran manal da sunan shaiɗaniya wannan zafi ne da cin fuska a idon jama'a"
baba yace "ta aikata komai"
dubawa alkali yayi, nan take ya bawa wani ya fara karanta duk abinda yake cikin takaddan harma da karamin memory wanda akayi recording da muryoyin manal, jikinta ya fara rawa amma tana kokarin dannewa, fuskanta ya fara zufa, wani mugun kallo ta fara aikawa baba, baba yace "bayan duk waɗannan laifukan data aikata mafi muninshi shine kashe mahaifinta da tayi wato Alhaji umar maidawa, kuma ta zubar da cikin jikin matarshi Hajiya salma"
fadeel yace "wannan zargi ne tunda bakada shaida"
baba yace "inada shaida sannan nazo wa Abdulrahman da lawyer ina fatan kotu zata bani dama na gabatar da shaida da kuma lawyer"
alkali yace "kotu ta baka dama"
fadeel yace "waye shaidanka?"
cikin zazzaƙan muryanta wanda rabon da suji tayi magana tun ranan da manal ta turata akan stair tace "nice shaidanshi sannan nice lawyer ɗin Abdool"
a mugun firgice manal ta kalleta, tayi kyau cikin uniform na lawyer tasa hulan a kanta ya zauna me kyau, sannan tasa takalmi baƙi tayi kyau sosai, bakinta yana rawa tace "Am...Am...Ammi"
murmushi tayi mata lokacin data karaso ciki tace "kinyi mamakin ganina ko manal umar maidawa? bakiyi tsammanin ganin ina tafiya kamar kowa sannan ina magana ba ko?"
murmushi tayi ganin jikin manal yana rawa sosai yanzu kowa yana gani, tace "hmm manal kenan ai tun ranan da kika turana daga stair dana farfaɗo da kaina nacewa dr yace miki bana magana kuma na samu ciwo a bayana, tun daga ranan na fara bibiyan duk wani abinda kikeyi sannan ina tabbatar da duk abinda nake bibiya ina samun shaida, ban nunawa kowa ina lafiya ba ciki harda ƴata ameesha wacce take zuwa kullum da kuka tafi kasar libya tana dubani, a lokacin da naga kina yiwa Abdool sharri sai banyi mamaki ba, yarinyar data kashe mahaifinta sannan ta zubar da cikin mahaifiyarta me ba zata iya ba?"
sai kuma ta kalli manal ɗin tace "koda shike dama ance tsintacciyar mage bata mage"
a mugun firgice ta kalli ammi da dara daran idanunta tace "me...me..kike nufi?"
tace "ina nufin kin tuna watarana da kika fita bayan kin dawo kikace yara suna kiranki da mahaukaciya a wani unguwa? sannan kin tuna watarana da kuka dawo keda abdool kina kuka kikace wasu sunce miki balarabiyan mahaukaciya? to kin san wacece wannan balarabiyan mahaukaciyar?"
jikinta yana rawa ta girgiza kai, ammi tace "itace mahaifiyar ki, a titi muka tsinceki akan bola dani da Alhaji umar maidawa mijina daya taimaka miki muka girmar dake muka baki rayuwa me kyau amma daga karshe mu kika fara cutarwa, kika kashe shi sabida kin ganshi da karuwa ko Allah baice a kashe mutum dan an ganshi da karuwa ba, Allah yace saika kamasu ido da ido sannan kanada shaidu har guda uku, a hakan ma idan me aure shine za'a jefesu idan marasa aure kuma sai ayi musu bulala tamanin tamanin, amma kika kasheshi sannan kika zubar da cikin da mukayi shekara da shekaru muna nemanshi, kika zamar dani mara amfani a duniya"
kuka ammi takeyi sosai, tace "abdool ne yazo yana kula dani, shima ba dan yana sonki ba sai dan rashin lafiyan da kike fama dashi na kansan zuciya, ya yadda ya aureki ne sabida dr yace saura miki shekara huɗu a duniya, a kullum sai yayi kuka saiya tuna da ameesha da kannenshi, a kullum idan bakya kusa dashi baida aiki sai kuka yana cewa ammi ya zanyi?
ya bar gidansu dabida tausayinki ya bar kawarshi da suka tashi tare sabida ke, ya yadda da sharrin da kika yiwa kaninshi sabida yaga kin mutu kina farin ciki amma daga karshe me kika saka mishi dashi?
ki duna abdool manal duk rayuwarshi babu daɗi yayi rayuwa dake dan dole ba dan yana sonki koda kaɗan a ranshi ba, ya kai ki kasar libya sabida ki samu magani anyi miki aiki kin samu sauki sabida yace zai koma wajen ameesha wacce suka taso tare da kaninshi wanda kika yiwa sharri da kaninshi fahad shiyasa kikayi mishi wannan sharrin? me yasa sai waɗanda suka taimakeki kike cutarwa anya ke ƴar halak ce kuwa"
girgiza kai tayi tace "tabbas ke ba ƴar halak bace domin akan bola aka haifeki, akan bolan ma ba asan waye mahaifinki ba, abba tunda yaga manal ya turawa momy sako _duk abinda kikeyi ki bari kizo kotu_
ta jima da zuwa tunda ammi ta fara magana take bakin kofan tana jinsu, manal tace "kina nufin ba kece kika haifeni ba?"
tace "Auzubillahi minki ina neman tsari daga Allah ya tsareni da haihuwan yarinya kamar ke manal, da Allah ya bani haihuwan irinki gara Allah ya barni haka babu haihuwa harna koma gareshi, manal ke annobace, ke cuta ce, ke masifa ce, manal ke bala'i ce, duk wanda kika shiga rayuwarshi sai kin tarwatsa, Allah ya tsare kowa dake"
tana hawaye tace "ni ƴar waye to idan bake ba?"
momy ce ta shigo tace "ke ƴata ce"
duk suka juyo suna kallonta, sai yanzu yazeed da sauran mutanen da kuma su abdool suke ganin tsananin kama kamar an tsaga kara, manal cikin hawaye tace "kunce ni ƴar mahaukaciya ce to ya akayi naga me kama dani wacce naji jikina ya bani itace ta haifeni da lafiya?"
ammi cikin shock ta kalli momy, da yatsa ta nunata tace "ke.ke.kece asibitin well care"
cikin hawaye tace "ɗaki me number biyar"
waro ido ammi ta kara yi tace "tabbas kece muka bige sannan mukaje mukayi ta nemanki bamu sameki ba sai ƴarki muka samu, wannan itace ƴar da kika haifa"
toshe kunne tayi ta rufe ido ta juya baya tace "ko a mafarki nayi mafarkin na haifi wannan annobar to wallahi idan na tashi sai nayi sadaka, manal bs ƴata bace ameesha ce da hanan ƴaƴana"
Abba ya tashi yana kallon Ammi yace "nine na bigeta a mota saina ɗaukota na kawota gidana, ameesha da hanan ne suka taimaka mata tayi wanka, sannan suka hanata tafiya sabida tace musu batada kowa, ganin tanada hankali yasa sukace saina aureta, batasan tanada ƴa bama ashe ta haihu cikin haukan"
_Duhu da haske is ₦400 via 8144818849 hauwa shuaibu mapi opay, evidence via 08144818849_
Jiddah ce.....
managarciya