WATA UNGUWA: Fita Ta 30

WATA UNGUWA: Fita Ta 30

BABI NA TALATIN

A cikin yanayin jimami da rashin makama, Biba ta gama tattare yan tsumokaranta tsaf, ta ja akwatinta ta fita tana karatun wasiƙar Jaki.

'Yanzu ina na nufa? Zuwa gidan yaya Hanne dai kamar tsautsayi ne, zuwa gidan Baba kuwa ƙaddara ce da rabon wahala.'

A haka ta nufi hanyar titi a ranta tana faɗar 'Shi tsautsayi idan ya tashi zuwa ba a san taya zai zo ba, amma ƙaddara bata da makawa, wahala kuwa ta ɗan lokaci ce, koma miye na san dai dole Abbanmu ya bar ni da numfashina.'

Da wannan zancen zucin ta ƙarasa titi ta tare abin hawa sai unguwarsu.

Ko da ta je gidan ta yi Sa'a Abbansu baya nan, shi ya sa ma har ta samu sararin zama ta huta ba tare da wani tashin hankali ko damuwa sun biyo baya ba.

Bayan dawowar Abban nasu da ya tarad da ita gida, bai kawo komai ba a ransa suka gaisa ya shige ɗakin Zaliha.

Daga can ciki ya ja wani malalacin tsaki, "mtsw! Gaskiya Zali kina da matsala, dubi ɗakin nan naki sai kace makwanci Jakuna. Banda kazanta irin taki ma me ya kawo Kifi da takalmi saman gado."

"Haba Alhj Ajiye wa fa na yi kafin na zo.!"

"Allah Ya waddan naka ya lalace, da ana gado bata hanyar haɗa jini ba da sai na ce wannan yarinyar Habiba ke ta gado a gun ƙazanta."

A haka yata bam-baminsa, sai dai ita Inna Zali ko a kwalar rigarta, sabgogin gabanta ma take. A ranta tana faɗar 'Ka ji da shi ciwon ajali a ɗan yatsa.'

Bai bar gidan ba, sai ga da Magariba, bayan ya yi sallar Magariba ya dawo a nan ya tarad da Biba.

Ya kalle ta "Ke Habiba me kike jira ne da har yanzu baki koma ɗakinki ba?" Nan fa ta shiga rarraba ido tamkar ɗan sane a gaban jami'an tsaro sai daman sosa ƙeya take.

Inna Jimmai ce ta kalle ta "Ai sai ki kora masa bayanin da kika koro mini."

Ya tsare ta da ido yana jiran jawabinta.

Da ta ga babu sarki sai Allah, sai ta sunkuyar da kai "Abba da ma Habibu ne ya ƙara sakina."

Dattijon ya ɗago a razane "Me kika ce? To garin ya haka ta faru?"

Ta yi shiru tana ƙara sunkuyar da kai kamar zata yi kuka.

"Ki yi magana wane laifi kika aikata masa? Don ni na san ruwa baya tsami banza."

"Wallahi ban sani ba Baba."

"To na ji, bari zan neme shi. Ina Salamatu? Ban ga motsinta ba tun ɗazu."

"Mun tashi da ita ba lafiya shi ne ya dauke ta zuwa asibiti tun lokacin ban ƙara ganinta ba, shi kaɗai ya dawo kuma a lokacin ya sake Ni."

"Tabbas da wata a ƙasa, Allah Ya sa ba halin ballagazancin naki ne ya janyo wata matsalar ba."

Ta yi sum-sum ta wuce ɗakin ummanta.

A nan Baba ya ɗaga waya ya kira Habibu ya ce ya zo ya same shi.

Bayan ya zo gidan, a gaban iyayen Alh Sule ya zaunar da Biba da Habibu don yin sulhu.

Take a wurin Habibu ya kwashe komai dake faruwa tun bayan auren su kawo izuwa yanzu da abinda ya sami Salma.

Nan fa gurin ya hargitse da sallallami.

Alhaji Sule ya ɗago ya kalli Jimmala "To kin ji ko? Da ma na nasa hakan a raina da ganin yadda take yi ita ce bata da gaskiya. Don na fi yarda da Habibu a kanta."

Biba da sai a lokacin ta ji abin da ya sami Yarta ta fashe da kuka "Wayyo Allahna na shiga uku ni Biba... Wannan bawan Ya cuce ni ya lalata mini rayuwar yata tilo a duniya Allah Ya...."

Bata ƙarasa rufe bakinta ba, Abba ya bige mata baki da hannunsa.

"Rufa mini baki ballagazar banza shashasha, ai ke ya fi dacewa a jawa Allah ya isa, ɓace mini daga nan."

Ta miƙe dafe da baki tana gunjin kuka, kafin ta ƙarasa ɗakinsu ta jiyo sautin muryar Habibu yana faɗar

"A gafarce ni da abin da zan faɗa Abba, amma zama tsakanina da Biba ya ƙare. Allah ya gani na ɗaga mata ƙafa iya ɗagawa amma bata daina abubuwan da take ba."

Abba ya girgiza kai, "Bakomai Habibu ai ka kyauta, zama da wacce bata san ciwon kanta ba ba abinda zai kare ka da shi sai tashin hankali da taɓarɓarewar iyali. Jeka Allah Ya maka albarka ya zaunar da kai lafiya da amaryarka."

Ya yi godiya ya miƙe har zai tafi Abba ya ya ce "Wace asibitin ce? Insha Allah gobe zamu shigo duba jikin Salmar."

A nan Habibu ya yi masa bayani sannan ya masu sallama ya tafi.

Tun daga ranar da ya taka ƙafa Ya bar gidan bai sake waiwayar Biba ba.

Haka ta ci gaba da rayuwa a gidan cikin tsana da tsangwama, ƙannenta duk suka rainata.

Duk wani aikin gida Abba ya tattare ya mai da kan Biba, wahala har wacce bata yi a farkon zamanta gida ba yanzu duk yi take yi.

Rayuwa ta yi mata atishawar tsaki. Bayan ta yaye yaronta Habibu ya zo ya karɓe dansa ya haɗa da Salmar ya damƙa amanarsu a hannun amaryarsa. Suka ci gaba da rayuwa ƙarƙashin kulawar amintacciyar matar uba da tafi masu mahaifiyarsu.