ZOBEN WUTA: Labari Mai Ban Mamaki da Tausayi, Fita Ta 5

ZOBEN WUTA: Labari Mai Ban Mamaki da Tausayi, Fita Ta 5


  ZOBEN WUTA


   By
_Jiddah S Mapi_

*Chapter 5*

_Ba zanyi free pages dayawa ba a page 9 zan tsaya da free pages_


                      ~Few days later madina ce a cikin mota tana sanye da uniform na school nasu wando blue da riga daidai gwiwa da blue dark sai hijabi fari guntu "janan!! janan!! ki fito mana zamuyi late fa"
janan daga ciki tana shiri cikin sauri, mufeeda taɗau jaka ta fita da gudu tana cewa "idan baki fito da wuri mu mun san halin sani driver wallahi tafiya yake ya barmu kuma saide muyi tafiya da kafa dan Abba ya hanamu driving"
da gudu ta fita, janan idonta ya cika da hawaye tasa riga da wando duka amma gashinta yaki kamuwa kuma school ɗin basa son suga alaman acuci a kan mutum, ko ribbon kwacewa suke sabida akwai boko akwai kuma Arabic duk a haɗe, jakanta na baya fari me kyau ta ɗauka sannan tasa canvas ɗinta ta ɗau hijabin har yanzu hanunta a kanta ta fita, zuwa yanzu hawayen ya fara wanke mata fuska, ko kaɗan bataso ta rasa zuwa school koda na kwana ɗaya ne, domin karatun da ake musu yana shiga kanta sosai, dana boko dana kur'ani yanzu hadda suke na izu biyar yau zasu shiga izu goma, tun daga kan stair yake kallonta ta juya baya batasan yana gida bama, yayi matukar kyau cikin orange na riga da wando jinx da polo, yasa picap orange, yana kamshin turare me daɗi da sanyaya zuciya, har ya sauko bata sani ba, kuka take tana cigaba da kame tulin gashin kanta me tsantsi da tsayi gashi baƙi ƙirin, yarinyar nan da alama ta haɗa jini da larabawa ko kuma mamanta India ko babanta akwai ɗaya, haka ya faɗa a ranshi, gyaran murya yayi da sauri ta juyo ta zuba mishi manya manyan idanunta da suke tsuma zuƙatan duk wani namiji daya kallesu, bama namiji ba har mace idan taga idon janan saita kara kallo sau biyu, share mata hawayen yayi da tafin hanunshi kana yace "kukan me?"
taɓe baki tayi cikin shagwaɓan daya zame mata jiki tace "gashin yaki kamuwa"
dariya yayi dan yadda tayi magana zaka san tana cikin damuwa, jin karan hon da sani yake mata kamar zai fasa musu kunne tace "zan tafi kawai haka amma zasu dakeni a school kuma banason bulala"
yace "sojoji ne suke bulalan?"
girgiza kai tayi
yace "to me na tsoro ni kinsan lokacin da nake zuwa school idan nayi laifi Abba sawa yake sojoji sumin duka?"
da sauri ta kalleshi da mamaki tace "meyasa?"
yace "sabida shi soja ne"
tace "sorry kaji?"
yace "juya na kama miki gashin"
tace "zasu tafi su barni"
ganin zata kwasa da gudu yace "wait barsu su tafi zan kaiki"
wani murmushin da yake burin gani a koda yaushe kan fuskarta shi tayi mishi, a duk lokacin da tayi wannan murmushin sai yaji wani sanyi a ranshi, yatsa yasa ya lakace dimple nata sannan yace "kinada kyau"
tace "ban kaika kyau ba"
yace "kin fini"
tace "A,a sabida ni fara ce shiyasa zaka ga na fika amma kai ba karamin kyakkyawa bane dama ace an bani skin ɗinka kai kuma an baka nawa zanso"
"to sannu me wayo, juya na gyara miki"
juyawa tayi ya kame mata gida biyu, kallon yadda gashin ya sauka har zuwa hips nata yayi, a hankali ya janye idanunshi daga hips nata yace "Auzubillahi minashaiɗanirrajeem"
tace "laa ya maheer ka iya kama kai"
gira ɗaya ya ɗaga mata yace "yes ina kamawa su mufeeda muje kar muyi late"
momy saida taga zasu fita tace "janan tsaya"
tsayawa tayi tanasa hijabinta, bayan tasa ta kalli momy wacce take rike da leda tace "gashi wannan banaso kina zama da yunwa"
karɓa tayi ta buɗe ledan, ganin cake ta daka tsalle ta rungume momy, kiss tayi mata a gefen kumatu tace "thank you momy I love you"
momy haka kawai take jin yarinyar har cikin ranta, tace "i love you too"
yana kallonsu har tace "muje ya maheer"
jerawa sukayi har suka fita tana murna, motarshi kiran benz ya shiga itama ta shiga, jan motar yayi suka fita, saida suka hau titi tace "ya maheer na tambayeka?"
gyaɗa kai yayi
tace "ba zaka min faɗa ba?"
girgiza kai yayi, ba zato ba tsammani yaji tace "meyasa ake yin s*x?"
saida yaji kan motan yana neman kwace mishi daga hanu, da sauri ya kalleta, sannan ya kuma kallonta, da kyar ya saita kan motar yaci gaba da tafiya akan titi, bai bata amsa ba itama bata kara tambayanshi ba, har suka isa kofan school nasu, school ne me kyau wanda alama yaran masu hanu da shuni ne a ciki, a hankali ta ɗau ledanta dake kan cinyarta tasa a jaka, buɗe marfin motan tayi zata fita, juyawa tayi ta saci kallonshi, kallonta shima yake da sauri ta dukar da kai ta fita, rufe motan tayi yana kallonta harta shiga school, meyasa tayi mishi wannan tambayan? ko lokacin da akayi mata fyaɗe batayi mishi wannan tambayan ba sai yanzu, ko dai batasan meya faru da ita bane a lokacin? to me ya kawo wannan maganan? me take tunawa harta tambaye shi?"
driving ya fara jikinshi a sanyaye, ita kuma tana shiga school taji dama batayi mishi wannan tambayan ba, yau duk karatun da akayi baya shiga kanta sosai, kunyan haɗuwa da maheer take, koda aka tashi madina tace "meyasa bakizo class namu a break ba?"
cikin sanyin jiki kamar me zazzaɓi tace "babu kawai"
mufeeda tace "kawai me? yawwa ya maheer ne ya kawoki ɗazu?"
gyaɗa kai tayi "shine"
"kinji daɗi mukam barinmu yake mu taka da kafa idan sani driver ya tafi"
murmushi kawai tayi, sun kyaleta sabida basason taƙura mata da surutu, da haka suka koma gida tunda sukaci abinci ta shiga ɗaki bata kara yadda ta fito ba, har mangrib har Isha tana kunshe a ɗaki batason haɗuwa da maheer, koda ya dawo a gajiye yaje ya canja kaya, fitowa yayi yaga kowa a zaune hadda Abba suna dinner amma babu Janan, yace "madina where...."
tace "tana ɗaki tun ɗazu taki fitowa"
ya gane meyasa taki fitowa kawai yayi murmushi ya ɗau plate zaisa abinci yace "tafi abinci?"
girgiza kai madina tayi tace "bataci ba na rana ma kaɗan taci cake da momy ta bata ma kaɗan taci tabar sauran a jaka"
ya ɗau plate me ɗan faɗi yasa abincin dayawa akai, spoon biyu ya ɗauka da cup biyu da ruwan gora, ɗakinsu ya nufa madina ta kalli mufeeda itama ta kalleta, rufe baki mufeeda tayi madina ta kauda kai, momy na kallonsu batace komai ba, knocking yayi cikin sanyin murya tace "yees"
dariya yaji amma ya dake baiyi ba, shiga yayi batasan shi bane, tana kwance rub da ciki tayi shiru, riga da wando ne a jikinta wandon gajere sosai sai rigan shima ba tsayi har cibiyanta a waje, gashinta ne ya rufe bayanta da yake a bayyane musamman hips nata da wandon ya bayyana juya baya yayi sannan yayi gyaran murya, da sauri taja bargo ta rufa har kanta, saida ya ɗan jima kafin ya juyo, ganin ta rufe kanta a bargo yace "tashi muci abinci"
kamar zatayi kuka tace "na koshi"
yace "me kikaci kika koshi?"
tace "babu"
yace "before I count three ki tashi, one....two"
tashi tayi ta yaye bargon, sauka tayi a gadon ya ɗauke kai, yace "sa dogon riga"
kallon jikinta tayi tabbas wannan ya kama jikinta amma ai shi yayanta ne kuma shi yace duk abinda su mufeeda zasuyi itama zata iya yi sabida itama kanwarshi ce, wandon da kaɗan ya wuce cinyarta, rigan kuma cibiyanta a waje, bata musa ba taje ta ɗau dogon riga after dress tasa, batasa bottle ɗin ba ta zauna a gabanshi kanta a kasa tayi shiru tana wasa da yatsunta, abincin ya matso dashi gabanta, yace "oya ci"
ci ta fara shima yana ci saide hawaye take yi, ganin tana hawaye yace "na kara miki?"
gyaɗa kai tayi cikin kukan tace "eh"
dariya yayi wallahi janan idan tayi wani abin kamar karamar yarinya, yace "to"
kara mata yaje yayi sannan ya dawo, taci ta koshi kafin tace "na gode"
ido ya zuba mata, tasan ita yake kallo shiyasa taki kallonshi, a hankali yace "meyasa kike jin kunya na?"
girgiza kai tayi alaman ba komai, yace "haka kawai kike jin kunya na?"
ta gyaɗa kai, yace "ko dan tambayan da kimanin ɗazu?"
shiru tayi, yace "kinsan meyasa ban baki amsa ba?"
girgiza kai tayi, yace "sabida nima inaso na tambayeki"
shiru tayi, yace "kin san meyasa mutum yake zama da ilimi sosai?"
girgiza kai ta kuma
yace "sabida yawan tambaya, duk me yawan tambaya yana zama da ilimi, to amma meyasa kikamin wannan tambayan?"
shiru tayi, ganin batada alaman magana yace "kin ɗauke ni matsayin yayan da kuka fito ciki ɗaya?"
jijjiga kai tayi yace "to ki ɗago ki kalleni kimin magana idan ba haka ba raina zai ɓaci kuma zan daina miki magana"
da sauri ta ɗago tace "dan Allah kada ka daina min magana"
yace "to ki bani amsa meyasa kika tambayeni?"
murza yatsun hanunta tayi a hankali cikin muryanta me daɗin sauraro tace "naji ana magananshi ne"
yace "Aina kika ji?"
cikin sanyin murya tace "a wajen ƴan class namu
shine na tambayesu suka ki bani amsa"
yace "okay shekarunki nawa?"
a hankali tace "goma sha tara"
yace "to ki bari sai kin kai 20 zan faɗa miki kinji?"
a hankali tace "to"
yace "kuma kimin alkawari ba zaki kara yin irin wannan tambayan wa kowa ba, daga ni sai ni"
tace "nayi alkawari"
yace "good girl yanzu ki daina jin kunya mu dawo kamar da"
tace "toh"
yace "ya karatun me akayi muku yau?"
nan ta saki jiki ta fara bashi labarin karatun da sukayi a school yau, ya rinƙa gyara mata inda akwai gyara, saida yaga ta sake dashi kafin yace "zanje nayi aikina saida safe"
tashi tayi tace "zanje wajen momy"
yace "okay"
tare suka fita, tana rike da plate ɗin da sukaci abincin, tana zuwa taga momy akan sofa da sauri ta faɗa kanta, momy tace "zaki karasa ni"
dariya tayi ta kwantar da kanta jikin momy tace "momy cake naki yayi daɗi nima na fara koyan yadda akeyi"
momy tace "ai cake sai lokacin da nake barrack kinsan abbanku shine babban soja a cikin barikin hakan yasa duk suke zuwa siyan cake a wajena, duk sun sanshi kuma yana da sakin fuska da son mutane, duk masu birthday a wajena suke zuwa ina musu cake, tace "nima shaida ce Abba baida matsala da wani ne nazo gidannan ba zai yadda na zauna ba, amma shi ba damu yasan daga ina nake ba, baiji tsoron ko zan iya cutar dashi ba.."
momy tace "kinga zaki fara kukan naki ko? get up nayi miki kitso"
tashi tayi ta zauna a gaban momy ta kwantar da kanta akan cinyarta, momy tace "madina ɗauko man kitso"
turo baki tayi tace "haba momy itace fa za'awa kitson kuma nice zan ɗauko mai? bacin ni ko zan mutu ba yadda kike kimin ba"
momy tace "zaki tashi ne ko saina saɓa miki?"
tashi tayi suka haɗa ido da janan, gwalo tayi mata, cikin masifa tace "momy kinga tana min gwalo ba?"
momy tace "karka kike janan ba zata miki gwalo ba neman rikici kawai kike"
kamar zatayi kuka taje ta ɗauko man ta dire a gefen momy, yana kallonta har time data yiwa madina gwalo ya ganta, yayi shiru a bakin kofarshi ya kasa ɗauke idonshi a kanta, mufeeda ce tazo wucewa ganin ya zubawa waje ɗaya ido ta kalli wajen, da sauri tace "yaya me kake kallo?"
hararanta yayi sannan ya basar ya shiga ɗaki, taga janan yake kallo sauda dama tana kamashi yana kallonta shine bai sani ba, momy tana mata kitso tana bata labarin zamansu da sukayi a barrack, na dariya tayi dariya na bakin ciki kuma ta taya momy, da haka har suka gama kitson, godiya tayi ta kalli mufeeda da madeena sai bacci suke, sun saba bacci da wuri, tashinsu tayi tace "ku tashi mu tafi ɗaki"
dukkansu baccin yayi nisa, momy tace "nikam saida safe"
tace "good night momy"
momy tace "good night my daughter"
tafiya momy tayi, rike kwankwaso tayi tana kallon sama tana tuna abinda zatayi musu su tashi, dariya tayi ta zauna tayi kallon wani film da yake mata daɗi saida aka gama na yau kafin ta kashe tv, tashi tayi taje wajen frij ta buɗe, ruwa me sanyi ta ɗauko ta tsitsaya dayawa a cup, a hankali take tafiya sabida kada ruwan ya zube, jikinsu dake sanye da rigan bacci ta ɗaga cup ɗin ta watsa musu, atare suka tashi a firgice 
"waye?"
cewar madina, rike ciki tayi tana dariya kamar zata faɗi kasa, madeena dirowa tayi daga kan kujeran taje frij ta ɗau goran ruwa, da gudu tabi bayanta itama gudun take tana cewa "dan Allah karki watsamin please and please"
sanin cewar madina batada hakuri kawai tayi ɗakin maheer da gudu ta faɗa kan gadonshi da yake kwance yana bacci, shiga cikin blanket nashi tayi ta kankameshi tana "dan Allah, dan Allah"
cikin bacci yaji muryanta kuma yaji an rikeshi, da sauri ya tashi yana kwacewa yace "janan meya sameki? waya shigo gidan?"
a tsorace yake tambaya, janye blanket ɗin tayi a hankali take leka madina, ganin tana tsaye har yanzu a bakin kofa da roban ruwa tace "madina ce zata watsamin ruwan sanyi"
tsaki yaja yace "kunada hankali kuwa? kunsan karfe nawa yanzu?"
a hankali ta fito daga blanket ɗin ta sauka a gadon tace "kayi hakuri"
yace "oya jeki kwanta dare yayi"
fita tayi tana lekawa, tana fita ta kuma dawowa a guje ta faɗa gadon, runtse ido yayi sam bayason bacci ya yanke mishi, yace "madina idan baki kyaleta ba na fita zan ɓata miki rai"
jin tayi shiru ya rike hanun janan yace "muje"
tana rakuɓe a bayanshi har zuwa ɗakinsu, ruwan madina ta watsa ta zaci janan ce a farko, da sauri ta waro ido tace "yaya dan girman Allah kayi hakuri ban san kai bane"
yace "shikenan kin rama?"
tace "kayi hakuri"
yace "tunda kin rama ki barta ta kwanta kada na kara jin komai idan kika kara saina saɓa miki wallahi"
jin ya rantse tace "to ba zan kara ba"
hawa gadon janan tayi yana kallonta ta rungume mufeeda wacce tun ɗazu take bacci, tace "saida safe"
yace "Allah kaimu"
madina a cike fam ta kwanta, saida ta kashe wuta janan tace "good night"
jin batayi magana ba tace "good night unty madina mara hakuri"
shiru tayi mata, ganin haka ta tashi cikin sanɗa ta cakuli madina, nanfa madina ta danneta akan gadon tace "wallahi saina rama"
ihu ta fara tana kiran Ammi, kallon agogo yayi, jin bata daina ihun ba ya tashi ya tafi ɗakinsu, kunna wutan yayi nan yaga madina ta danneta ita kuma sai harba kafa take, yace "madeena wai kunsan karfe nawa ne yanzu?"
sauka madina tayi daga kanta tace "wallahi itace ta tsokaneni yaya"
yana ganin idon janan yasa batada gaskiya, yace "sauko"
saukowa tayi ya rike hanunta suka fita, ɗakin momy yaje da ita yayi knocking kafin ya shiga, momy cikin bacci tace "maya faru?"
yace "momy ta kwana anan itada madina basa sanin dare yayi"
nuna mata gefen momy yayi yace "saura naji kin koma can"
da sauri ta hau gadon ta rungume momy dama abinda take so kenan, ya lura da hakan, ji yayi tace "saida safe"
bai amsa mata ba, tayi shiru a bayan momy, momy taji son yarinyar ya kara shiga ranta, tana rungume da ita har bacci ya ɗauke ta.
ɗakinshi ya koma ya kwanta, tunani ya fara saide duk tunanin akan janan ne, duk yadda yaso ya kawar da tunaninta ya kasa, da kyar ya samu bacci ya ɗaukeshi, a cikin baccin ma mafarkinta yake.

washe gari weekend ne, dama ranan weekend yana kaisu shopping, yadda ya fito bai shirya ba kawai jallabiya a jikinshi momy tace "meya faru bakayi bacci bane?"
yace "nayi amma ba sosai ba inaso idan nayi breakfast na koma nayi kaɗan, kunyi waya da Abba?"
tace "wallahi munyi waya amma yana sauri zasu shiga aiki"
yace "okay Allah yasa ya dawo gobe"
tace "insha Allah gobe ɗin nema"
zama yayi ya zuba tea me zafi, lemon tsami ya matsa a ciki dayawa momy ta kalleshi bataso tana yawan mishi tambaya hakan yasa tayi shiru, madina ce ta kasa yin shiru tace "yaya kaida baka son lemon tsami yau kaine da zubawa dayawa a tea?"
lumshe ido yayi a wahalce yace "haka naga dama yau ko zaki hanani sha?"
tsit tayi, janan tayi shiru tana shan shayi, kallonta yayi suna haɗa ido ta sakar mishi murmushin data saba, murtuƙe fuska yayi yace "baki iya gaisuwa bane?"
da sauri tace "laa yaya good morning"
bai amsa ba yaci gaba da shan tea, saida ya shanye tas ya tashi yayi mika yace "momy zan koma na kwanta su shirya kafin 11 zanzo na kaisu shopping"
janan tace "hadda ni?"
gyaɗa mata kai yayi, cikin jin daɗi tace "na gode"
komawa yayi ya kamata, tunda yasha shayin yaji sauƙin abinda yake damumshi, bacci me daɗi ya dauke shi, shine bai tashi ba sai karfe sha ɗaya da rabi, da sauri ya shiga yayi wanka yasa kananan kaya sabida bayason taƙura, yayi kyau sosai yana zuba kamshi ya fito, tunda taji kamshin turarenshi ta ɗago kai tana kallon inda tasan zai fito, a ranshi yace "masha Allah"
kyau tayi sosai cikin bakin dress ɗin da momy ta zaɓa mata, tashi tayi momy tana gyara mata zip ɗin rigan, tace "momy thank you"
momy tace "kinyi kyau sosai ƴata"
rigan yana jan kasa, daga sama kuma kitson da tayi mata ta kame mata sannan tasa mayafin ta ɗan ja gaban ta yadda kitson zai bayyana, kwalliya tayi mata me kyau tasa takalmi me tsayi kaɗan sannan ta bata jaka, turare ta fesa mata me kamshi, momy tana kallon maheer wanda ya kasa ɗauke idonshi akan janan, madeena da mufeeda sunyi ankon atamfa ɗinkin dogon riga me kyau, sunyi kyau sosai suma, momy tace "masha Allah ku siya min abu me daɗi"
janan tace "to momy me kikeso? inada dubu biyar saina siya miki"
murmushi momy tayi tace "koma me kika siyamin janan zan karɓa"
tace "momy inaso naga kina farin ciki"
momy ta rike hanunta tace "janan kimin alkawari ba zaki bar family ɗinmu ba, zaki zauna damu har a bada"
a hankali tace "insha Allah"
yace "muje"
mufeeda tayi saurin rike hanun madeena suka jera suna tafiya, shi kuma yana tsaye a baya da janan ya kasa rikewa a ranshi yace "kinyi kyau"
tace "sosai?"
a hankali yace "eh mana sosai ma kamar sarauniya"
tace "ko ɓarauniya ba?"
dariya yayi yace "me kika sace?"
tace "na sace kyawunka"
yace "umm na yadda ke SARAUNIYA KO ƁARAUNIYA  duk biyu, kin sace momy a wajena kuma kinyi kyau kamar sarauniya"
tace "ni dai ban sace ta ba"
yace "kin sace"
shagwaɓe fuska tayi tace "um um"
wannan shagwaɓa a jininta yake bata ma sanin tayi, shiga mota sukayi taga fadeela da mufeeda a baya alama sun bar mata gaba ta zauna, zama tayi ta juyo ta kallesu duk hankalinsu akan waya, shiru tayi har suka fita, a hanya ganin tayi shiru ba waya a hanunta yace "kinason waƙa?"
da sauri tace "eh"
yace "wani kala?"
tace "na soyayya"
murmushi yayi sannan yace "kinason soyayya ne?"
rufe fuska tayi alaman taji kunya, ya kunna mata wakan umar m sharif"
a hankali ya lumshe ido ya fara bin wakan "nayi gamo da soyayya ce, da wata ɗiya me kyau ce"
har zuwa inda ake cewa "masoyiyata kyakkyawa ce, sannan a fuska me yawan fara'a ce"
wani smiling da tayi daidai wannan lokacin saida yaji kamar ya tsaida motan yayi ta kallonta, itama ji yayi ta fara bin wakan a hankali, rage muryan yayi yana saurarenta, baisan time ɗin da yace muryanki da daɗi ba
madeena da take cikin watsapp ta turawa mufeeda text 
"ke kinga wani soyayya kamar a Indian film?"
mufeedah tana karantawa ta tura mata "aiko ina gani sufa yanzu basu san soyayya suke ba, ya maheer fa ya shiga hannu"
dariya tayi sai a sannan janan ta juyo tace "madina nima ki nuna min abinda kike kallo kikayi dariya"
aikinta kenan idan sunyi dariya a waya tace su nuna mata abinda suka kalla, ko kuma ta kwanta kusa da madina tana kallon chat nata, madina tace "ai na riga na wuce"
mufeeda tayi shiru kamar bata san komai ba, turo baki tayi taci gaba da bin wakan, a kofan babban ShopRite ys tsaya da motar, tare suka fito su duka, shiga sukayi ta rinƙa bin wajen da kallo, ya mata kyau sosai, maheer yace "ƴammata muje mana kin tsaya kina kallo"
tace "wajen yamin kyau"
yace "zaki sha ice cream?"
tace "eh"
madina da mufida har sun shiga sun fara ɗaukan abinda suke so, wajen saida ice cream ya kaita aka bata akan tsinke tana murna ta karɓa tana sha, ganin yana kallonta baya sha ta mika mishi nata tace "gashi"
buɗe baki yayi, tasa mishi tana murmushinta me sanyi, saida yasha yace "thank you"
yace "muje mu samu su mufida"
tafiya zasuyi tace "wait saura na momy"
yana kallonta har taje ta siya na momy aka sa mata a leda, ji yayi ta kara shiga ranshi domin ko shi dasu madina basa tuna siyawa momy ice cream Idan sunzo, tazo tace "muje"
shiga ciki sukayi mufida ta cika basket, madina kuma tana tura musu, can ta hango katon teddy tana tsoron teddy sosai hakan yasa tayi gefe tana kallon madina da mufida suna zaɓa, a cikin kunnuwanta taji ance "JAAN"
a mugun firgice ta juyo idanunta suka kara girma, wani kyakkyawan saurayi me tsananin kama da ita ne yake tsaye a gabanta yana mata murmushi sak yadda take murmushi haka shima yake yi, atake ta fara ja da baya bakinta yana rawa, matsowa ya fara kusa da ita yana cigaba da murmushi, saida ta mannu da bango tasa hanu tana kare fuskanta daga kallonshi, matsowa yayi sosai yace "jaan nayi kewarki bakiyi kewan yayanki bane?"
a mugun firgice tace "help!!! help!!! help please"
maheer dake tsaye a gefe yana kallonsu da mamaki akan fuskanshi, tunda yaga yaron farkon shigowansu yaga sunyi kama da janan kamar an tsaga kara, yana shirin faɗa mata sai kuma ya juya bai ganshi ba, a yanzu daya gansu tare yayi zaton zatayi farin ciki da murna sai kuma yaga saɓanin haka, a ruɗe take sosai, bai taɓa ganinta cikin wannan ruɗewan ba sai ranan da yayi mata tsawa, hanu yasa ya cire hanunta da take kare fuskanta dashi yace "tsoron me kike?"
tureshi ta fara tana cewa "taimako jama'a"
da sauri maheer yazo ya tsaya a gabanshi ya cire hanunshi daga nata, wani irin kankame maheer tayi ta baya ta ɗaura fuskanta a bayanshi, ganin yadda ta rike cikinshi kamar zata shiga jikinshi, ya kalli wanda yake tsaye a gabansu yace "waye kai?"
kallon rainin hankali yayi mishi kana yace "kana ganina ai kasan waye ni, kaine dai zan tambaya waye kai sabida na ganka da kanwata"
gaba ɗaya maheer ya rasa abin cewa domin kuwa gaskiya yake faɗa kana ganin wannan kasan jinin janan ne, yace "matsa zan tafi da kanwata"
cikin tsananin tsoro ta kuma kankame maheer tana girgiza kai, rawan da jikinta yake yi kaɗai ya isa ya tabbatar da halin da take ciki, maheer yace "janan zaki bishi?"
girgiza kai tayi cikin muryanta daya gama cika da tsoro tace "ka taimakamin kasheni zaiyi wallahi yana kisa"
gabanshi yayi mummunan faɗuwa jin abinda ya faɗa, yace "kin sanshi ne?"
da kyar tace "ya NABEEL ne, ka fita dani anan"
ganin zai taɓata maheer ya dakatar dashi yace "karka sake kasa hanunka a jikinta"
yace "ko kuma me zakayi?"
buɗe murya yayi yace "security? security?"
baya yayi yace "yau ta tsira amma ka sani kaima ka shiga gonan da ba naka bane kuma zakayi nadama"
tafiya yayi yabar wajen, a hankali yace "Janan? janan?"
jin tayi shiru kuma tayi nauyi a bayanshi ya juyo da ita, ganin wuyanta ya faɗi yace "janan buɗe ido"
madina dake tsaye ledan hanunta ya jima da faɗuwa tace "ta suma"
ɗaga ta yayi yace "mu tafi"
tare suka tafi, ya sata a mota duk suka shiga, direct gida ya nufa, da sauri ya fito da ita ya shiga ciki, momy dake kallo a falo ta tashi da sauri tace "meya faru?"
kwantar da ita yayi akan sofa yace "suma tayi"
tace "meya sameta?"
madina zatayi magana yayi sauri yace "haka kawai ta faɗi a ShopRite"
kallonshi sukayi jin yayi karya, daga nan sukayi shiru, ruwa ya ɗibo ya fara shafa mata a fuska, da kyar ya samu ta farfaɗo.


*Jiddah Ce...
08144818849