ƘADDARA TA: Fita Ta Huɗu

yace "no kema kamar ƴa kike a gidannan bada sonki kikazo ba, kuma ke marainiya ce gaba da baya insha Allah zakiyi zama kamar kowa a gidannan ki zama me ƴanci ba baiwa ba" tace "to idan ba zaiyi na zama baiwar ba ko ƴar aiki zan zama"

ƘADDARA TA: Fita Ta Huɗu

ƘADDARA TA: Fita Ta Huɗu


        Na
*Jiddah S Mapi**

Chapter 4*


                  ~Har dare tana bacci babu wanda ya tasheta, sultan dake zaune a dinning suna cikin abinci tare yace "minat ya akayi bata tashi ba har yanzu? ko dai ta mutu ne itama?"
hameed wanda yasa abinci a baki kwarewa yayi jin abinda sultan ya faɗa, ruwa kaseem ya mika mishi, karɓa yayi yasha sannan yace "sultan ka rinƙa faɗan alkhairi ko kuma kayi shiru"
yace "to yaya"
a hankali take takowa tana rike karfen gam gam da iya karfinta, rufe ido tayi sabida tana tsoron abin sosai, minat data kula da ita da sauri ta tashi, missing step tayi zata faɗi duk suka waro ido a tsorace harda me martaba, minat ce tayi gudu ta riketa, kankame minat ɗin tayi sosai taki buɗe ido, karasa sauka sukayi tare, a hankali ta buɗe idon ta sauke akan hameed dake rike da spoon cike da abinci har yanzu yana kallonta, murmushi tayi mishi me sanyi, sunkuyar da kai yayi yaci gaba da cin abincin, minat taja mata kujera ɗaya tace "ki zauna"
kin zama tayi ta durkusa kasa ta gaida Abi, cikin kulawa ya amsa sannan yayi mata ya hakurin rashi, ta amsa da Alhmdllh, yace "tashi ki zauna ki saki jikinki ki ɗauka nan gidanku ne"
shiru tayi tana durkushe, yace "tashi mana"
cikin sanyin muryanta tace "zaifi kama na zama baiwa a gidannan banida matsayin zama ƴa"
da mamaki abi yace "baiwa kuma?"
tace "eh"
yace "no kema kamar ƴa kike a gidannan bada sonki kikazo ba, kuma ke marainiya ce gaba da baya insha Allah zakiyi zama kamar kowa a gidannan ki zama me ƴanci ba baiwa ba"
tace "to idan ba zaiyi na zama baiwar ba ko ƴar aiki zan zama"
murmushi yayi yace "tashi ki zauna ko ɗaya ba zaki zama ba"
a hankali ta fara kuka, yace "share hawayenki kema ƴa ce a gidannan tashi ki zauna"
ganin dogari ya shigo kuma da bulala a hanunshi shine yayi mata tsawa ɗazu tayi saurin tashi a tsorace ta zauna tana kallonshi da manyan idanunta, abinci minat tasa mata tace "kici sai kisha magani"
ta fara ci kamar bata son ci, sultan yace "ni sunana sultan shi kuma wannan sunanshi fadeel, wannan shine babban yayanmu ya kaseem, shi kuma wannan shine yarima hameed shine magajin sarki"
kallonshi tayi ya ɓata rai yana cin abinci, saida gabanta ya faɗi ganin yadda ya ɓata rai, a hankali tace "ni sunana Aneeta"
yace "nice name unty aneeta"
abincin taci kaɗan sannan ta karɓi maganin tasha, Ammi tace "sannu Allah baki lafiya"
tace "ameen"
Abi yace "gobe za'a naɗawa hameed rawanin yarima"
tsit wajen ya zama babu wanda ya kara magana ko motsin kirki, yace "kwarai gobe zai zama cikakken yarima"
ammi jikinta ya fara rawa, tayi karfin halin dannewa tace "Allah ya kaimu"
sultan kallon kaseem yayi saide kaseem hankalinshi akan abinci ya ɗago yace "Allah ya kaimu"
kallon Ammi aneeta tayi tana ganin yadda take danne halin da take ciki, da mamaki take kallonta to ba itace ta haifeshi ba?
sultan yace "na manta ban faɗa miki ba wannan itace ammi itace ta haifemu duka banda wannan iyayenshi sun rasu ɗan kanin abi ne"
ya nuna fadeel, murmushi tayi mishi tace "sannu"
yace "yawwa"
da haka suka gama cin abincin kowa ya watse, ɗakin ta koma itada minat taga minat tana karatu murmushi tayi tace "zaki rinƙa koyamin karatu?"
tace "eh me zai hana?"
tace "na gode"
kwanciya tayi amma bacci yaki ɗaukanta sai tunani kala kala take a cikin ranta da kyar baccin ya ɗauketa.

hameed yana zaune a bakin gado yayi tagumi, turo kofan kaseem yayi a tsorace ya kalleshi sabida yasan allura zaiyi mishi, murmushi yayi yace "sannu hameed"
ɓata rai yayi dan fa shi ya tsani wannan alluran, zama yayi kusa dashi ya mika mishi hanu suka gaisa yace "congratulations in advance"
taɓe baki yayi alaman for what?
yace "zaka zama cikakken yarima gobe duk ranan da babu Abi ina alfaharin zamanka sarki"
ɓata rai yayi, yace "ka daina ɓata rai sabida Allah ne ya baka wannan matsayin"
alluran ya ɗauka yace "time for injection"
hawaye ne ya taru a idonshi ya fara girgiza kai, cikin tausaya mishi yace "sorry bro ba zaiyi zafi ba i promise"
hanu ya mika mishi alaman yayi alƙawari, sarke hanun yayi cikin nashi yace "promise"
a hankali ya tashi da kanshi yayi kasa da wandon aka mishi alluran baiyi zafi sosai ba, yace "kwanta to"
kwanciya yayi akan gadon kamar kullum shafa lallausan gashinshi ya fara har yayi bacci kafin yayi mishi kiss a forehead ya fita, ɗakinshi yaje ya zauna akan sofa yayi shiru yana tunani idonshi a rufe kamar me bacci, ajiyan zuciya ya sauke ya fesar da iskan bakinshi.

Fadeel ne kwance akan gado ya ɗaura kanshi a kafar sultan dake waya, yana jinshi yadda yake hira kamar wani babba, saida ya gama yace "sultan"
yace "yes bro"
yace "meyasa ya hameed baison zama yarima?"
taɓe baki yayi yace "kuma dole zai zama ba?"
yace "to idan baya so kada a bashi mana aba ya kaseem"
sultan pillow ya janyo ya ɗaura kanshi yace "ka samu Abi ka faɗa masa"
tsaki fadeel yaja yace "kai sai ana magana ka sakowa mutane shirme"
yace "good night"
bacci ya fara shi kuma fadeel tunani yake meyasa zasu bashi bayan ya nuna bayaso? kuma ga ya kaseem shine babba meyasa basu bashi ba? sai wanda bayaso za'a bawa?"
da wannan tunanin yayi bacci.
washe gari shirye shirye ake a gidan sarkin duk bayin gidan suna girki saura suna shirya babban wajen da ake taro a gidan, komai ya zama daidai akan tsari ga kujerun manyan bakin da za'ayi ciki harda governor, wajen zaman yarima kusa dana sarki, ciki kuma kaseem ne yake shirya hameed wanda yaki yin komai tunda yayi wanka yake zaune yaki yin komai, da faɗa kaseem ɗin ya fara shiryashi, tsadadden alkyabban da Abi ya bashi yasa mishi akan shaddan jikinshi me tsada, murmushi yayi ganin yadda golding na alkyabban yayi mishi kyau sosai, hulan sarautan yasa mishi sannan ya bashi mafici irin na sarkin, durkusawa yayi kasa yana sa mishi takalmin da yake irin alkyabban, ido ya zubawa ya kaseem ɗin yana jin sonshi har cikin ranshi, a hankali ya ɗago ya kalleshi, yace "kanina kayi kyau sosai"
a hankali ya tashi ya rungume kaseem ɗin, shiru sukayi, kaseem yaji baida niyan sakinshi janye jikinshi ya fara sai kara kanƙameshi yake, da kyar ya janye yana kallon kyakkyawan fuskanshi da yake hawaye, share mishi hawayen yayi yace "yau ranarka ce bai kamata kayi kuka ba, idan Abi ya gani ranshi zai ɓaci"
sunkuyar da kanshi yayi, sandan sarauta me tsada da kyau ya mika mishi ya karɓa, nan take wankan ya kara mishi bala'in kyau, turare me kanshi ya fesa mishi sannan yace "masha Allah kanina kayi kyau sosai"
knocking akayi yace "yes"
Ammi ce ta shigo sanye da alkyabban da bayan yake jan kasa, tasa hulan alkyabban akan gashinta da yasha gyara sannan tasa ɗankunne da abin goshi na gold, rike take da plate na flower a hanunta, saide fa fuskanta babu annuri ko kaɗan babu alaman murmushi, kaseem kallo ɗaya yayi mata ya kauda kai, hameed kuma ya zuba mata ido har ta karaso, tace "mai martaba yace mu fito tare an gama shirya komai kuma baƙi sun hallara"
kaseem yayi saurin sa kayanshi shadda maroon me masifan kyau, ya fesa turare sannan yasa hula maroon ya riko hanun hameed ɗin yace "muje"
tana bayansu suna gaba da plate ɗin flower a hanunta, suna fita su sultan da sukayi anko cikin maroon na shadda irin na ya kaseem ɗin suka zo suna mishi sannu, murmushin karfin hali kawai yake musu, minat da gudu ta sauko daga stair ɗin ɗakinsu tayi bala'in kyau cikin baƙin shadda irin wanda ammi tasa kafin tasa alkyabban, dogon riga ne fited gown sai red veil da tasa a gefen wuyanta, tace "wow yaya yarima kayi kyau"
murmushi yayi mata sannan ya fara kallon sama inda yake kin karan takalmi da kamshin turare, aneeta ce take takowa cikin tsoro ta damƙe karfen stair masha Allah tayi bala'in kyau cikin baƙin shadda, itama irin ɗinkin minat ne amma ya kama jikinta sosai hakan yasa take rufewa da red veil ɗin sabida bata saba sa kaya masu kama jiki ba, bata mantawa kullum mama cewa take kada ta rinƙa sa kaya masu kama jiki domin yanayin jikinta mai ɗaukan hankali ne, ya kasa ɗauke idonshi a kanta, kaseem da yake mishi magana yaga yana kallon waje ɗaya shima ya kalli inda yake kallo, murmushi yayi ya zuba mishi ido, har saida ta sauko kafin ya kauda kai daga kallonta, sai a lokacin ya kalli kaseem, da sauri ya sunkuyar da kai sabida kunyan kashe mishi ido da kaseem ɗin yayi, durkusawa tayi ta gaida kaseem ɗin tareda hameed ɗin, bai amsa ba ya ɗauke kai, ya kaseem ne ya amsa, ta gaida ammi ta amsa ba yabo ba fallasa, hanunta minat ta rike, kaseem da hameed ne a gaba su kuma suna bayansu, suna fita a falon suka fara taka red carpet ɗin da aka shimfiɗa me matukar kyau, duk bayi da dogarai suna tsaye a gefe gefe sun sasu a tsakiya kan red carpet ɗin, ammi ta mikawa ɗaya daga cikin bayin plate ɗin sannan ta fara watsa mishi flower, algaita ake hurawa tareda busa sarewa, masu kiɗin garaya suka fara, ana mishi kirari, da haka har suka isa inda zasuyi taron, makil mutane suka cika wajen, manya manyan mutane ne harma da kanana, mutanen gari dana nesa dana kusa duk sun hallara, tun daga nesa mai martaba ya fara murmushi ganin kyaun da hameed yayi, hankalinshi kwance yake idan ya mutu ya bar hameed ne zaiyi gadon sarauta hakan yasa yake gaggawan bashi wannan matsayin na yarima, har ya karaso ya durkusa kasa ya yiwa abi alaman gaisuwa, ɗagashi yayi ya zaunar dashi akan kujeran, flower aka watsa sannan aka tafa mishi domin ya zauna a kujeran yarima, su kaseem dasu ammi suna kujeran gaba gaba, gomna aka bawa waje ya fara jawabi, daga nan Abi yayi magana cikin nutsuwa, karɓan sandan hanunshi yayi ya aje a gefe sannan ya kalli sabon sandan da aka bawa gomna wanda dashi zasuyi amfani wajen mikawa hameed wannan girman na yarima, ɓare tsadadden sandan gomna yayi a leda sannan yazo gaban hameed ya tsaya Abi ya tashi shima yasa hanu akan sandan zasu mika mishi, hameed ganin baiwa rike da plate da kuma wuta kaɗan akai, ya zuba mata ido, jikinshi ne ya fara rawa, Abi ganin haka yace "relax hameed babu abinda zai sameka"
baya baya ya fara yana waro manyan idanunshi, girgiza kai ya fara kamar sabon mahaukaci, da sauri ya bige sandan zai gudu, ya kaseem dake zaune da gudu ya tashi yazo ya rikeshi, a kunnenshi yace "hameed ka nutsu cikin mutane muke"
girgiza kai ya fara yana kwace jikinshi daga na kaseem ɗin, fizge fizge ya fara yana nuna wutan, mutanen wajen kowa ya fara tsorata ganin halin daya shiga, take zufa ya jiƙa goshinshi, ya kaseem ya kankameshi sosai yana hanashi fizgewan, Aneeta da mamaki take kallonsu sai kuma ta kalli minat tace "me yake faruwa dashi haka?"
share hawaye minat tayi tace "baya son ganin wuta ko kaɗan ne, kuma...."
kuka ne yaci karfinta ta kasa karasa maganan, a hankali ta janyota jiki tana shafa bayanta alaman tayi hakuri, idonta akan hameed daya kasa nutsuwa zuwa yanzu kaseem yanaso ya gagara control nashi, ga mutane da suka fara tashi zasu tafi sabida abin ya fara worst, a hankali ta saki minat ɗin ta tashi, wajen taje zuwa yanzu ya fara kaiwa kaseem duka a kirji, cikin sanyinta ta rike hanunshi dake dukan kaseem ɗin, ɗago jajayen idanunshi yayi yana kallonta, addu'a ta fara yi mishi a hanun, ji yayi jikinshi yayi nauyi, kaseem ganin ya ɗan nutsu ya fara sauke ajiyan zuciya, cikin sanyinta take addu'a tana tofa mishi, a hankali kaseem ya sakeshi tana rike da hanunshi, ji tayi ya faɗa jikinta ya kanƙameta kamar zai maidata cikinshi, bata damu ba taci gaba da karanta addu'o'i masu karfi tana tofa mishi a kunne da kuma kanshi, saida yayi shiru kamar wanda yayi bacci kafin ta tofa addu'a a hanu sannan ta zameshi daga jikinta ta shafa mishi a fuska, kallon baiwar dake rike da plate da wuta a kai wanda ta zuba turaren wuta tayi, da hanu tayi mata alaman ta tafi da wutan a wajen, tafiya tayi da wutan, a hankali ya dawo hayyacinshi ya kalli inda wutan yake yaga babu, kallonta yayi tayi mishi murmushi tace "babu wuta ka koma ka zauna"
a hankali ya koma ya zauna yana kallonta, ya kaseem ya share zufa yace "ya Allah"
gomna wanda ya ɓuya a bayan kujera ganin ya daina abinda yake ya fito yana neman sandan daya wurgar a gefe, ɗauka yayi yazo sarki ya tashi ya rike shima har idonshi yayi ja saboda halin da ɗanshi ya shiga, bashi sandan sukayi sannan sarki yace "YARIMA HAMEED"
tafi akayi kowa yana murna, murmushi jabeer yayi yana tafa mishi, kowa ya shaida shine yarima, hulan kanshi aka cire sannan gomna ya ɗaura mishi rawanin sarauta nan take ya kara zama me kwarjini na musamman, tafa mishi ammi sukayi, da haka aka gama taron.

kowa sai zuwa yake yana gaisawa da hameed tareda mishi congratulations, saide yayi murmushi ya gyaɗa kai da haka har taro ya watse, cikin gida suka koma su duka, kaseem wanda jininshi yake tafasa yana kallonsu da tsananin ɓacin rai akan fuskanshi yace "wallahi ban taɓa rantsuwan karya ba wannan abinda ya faru set up ne"
Ammi wacce take huci tace "set up kamar yaya kaseem? baka ganin turaren wuta ta kawo?"
idonshi sunyi jajur yace "turaren wuta? waya sata? dama ana kawo turaren wuta wajen naɗi ne?"
tace "to kaseem wa kake zargi?"
itama tayi maganan ranta yana tafasa kamat idanunta zasu zubo waje, kallonta yake babu ko kyaftawa yace "koma wa nake zargi babu ruwanki kuma na rantse idan har na tabbatar da wanda ya shirya wannan abin wallahi sai na hukunta meshi koma waye shi"
da ihu yake maganan kamar zai fasa gidan, fita yayi daga ɗakin, hameed ya zube kan kujera yana rike kanshi ya tsani tashin hankali, ya tsani ihu jininshi hawa yake idan ana hakan, babu jimawa kaseem ya shigo hanunshi rike dana baiwar data kai wutan wajen yana janta kamar zai cire hanunta daga jikinta, wurgi yayi da ita a falon ya nunata da yatsa, jijiyoyin kanshi sun tashi yace "na rantse da Allah, na rantse da ubangijin daya halicci sammai da kassai idan har baki gayamin waye ya saki wannan aikin ba saina kasheki"
Aneeta dafa kirji tayi jin abinda ya faɗa tayi baya a tsorace, bakin baiwar ya fara rawa, ya taka hanunta dake kasa yace "zaki gayamin ko ba zaki faɗa ba?"
rufe ido ammi dasu minat sukayi ganin yadda ya taka hanun babu tausayi, ihu tayi ya sauke mata marin da yasa tayi shiru sabida azaba ya kara taka hanun wannan karon idanunsa kamar zasu zubo kasa yace "zaki faɗa ko saina kashe ki?"
jikinta yana rawa ta kalli Ammi, da sauri Ammi ta juya baya, ya kalli inda take kallo ya kara taka hanunta wannan karon saida ya fara jini yace "zaki faɗa ko kuma?"
ganin ba zata faɗa ba ya cire kafanshi daga hanunta a fusace ya haura stair da mugun gudu ɗakinshi ya shiga babu jimawa ya fito da bindiga karami a hanunshi, waro ido hameed yayi, sultan ya ɗaura hanu aka zaiyi ihu yasa hanu a baki ya toshe, Aneeta fitsari ne kawai bata yi ba, duk hantar cikinta ya kaɗa, batasan time ɗin data kankame hanun minat ba, tunda take bata taɓa ganin me zuciya idan ranshi ya ɓaci kamar kaseem ba, nunata yayi da bindigan yace "idan na irga uku baki faɗa ba wallahi saina harbeki"
jikinta yana rawa tace "zan faɗa"
duk suka kalleta a tsorace kenan da gaske sata akayi?
yace "ɗaya...biyu...."
tace "A..."
kafin ta karasa ammi ganin yace "three"
taje da gudu zata buge bindigan ba tareda ya cire hanu ba bindigan ya tashi take goshin baiwar ya fashe da bullet ɗin daya fasa mata har ƙwaƙwalwa, tsit ɗakin yayi babu wanda ya kara koda numfashi me kyau, bindigan rike a hanunshi ita kuma ammi tasa hanu a baki ta rufe idanunta a waje, Aneeta kuma fitsarin da take rikewa ji tayi kamar ma ya zubo, minat kuma tasa hanu aka ta kasa fasa ihun, hameed rufe ido yayi tareda kunnenshi ya toshe, Abi daya shigo yanzu ya kasa maida kofan ya rufe, jikin hameed ya fara rawa ganin ya jabeer baiyi dana sanin abinda yayi ba domin ko gezau baiyi ba bale yaje ya duba ko tana raye ko ta mutu, sunfi minti goma sha biyar a haka, da kyar ammi taja kafarta da yayi nauyi taje inda take kwance tana kiran sunanta "A'isha? Aisha?"
da ihu kamar zata fasa gidan tace "A'ishaaaa?"
kanta ta ɗaura akan ruwan cikinta tana kuka, ɗago jajayen idanunta tayi tana kallon kaseem da har yanzu yake rike da bindiga, cikin ihu tace "meyasa ka kashe ta?"
murmushin gefen baki yayi yace "na kasheta? ko kuma kika kashe ta ba? ai da gangan kikazo kika bige bindigan sabida nayi harbi ban saniba"
tana kallonshi da mugun mamaki har ta karaso wajenshi, hanu tasa ta shaƙe wuyanshi tace "akan me zan kasheta? me zaisa na kasheta?"
tureta yayi yace "sabida bakyaso ta faɗi wanda ya sata"
tace "kana nufin ni kake zargin na sata taje da wuta wajen naɗin hameed ɗana sabida ya fita hayyacinshi? ɗana dana san ganin wuta yana iyasa ya rasa rayuwarshi?"
yace "kin damu da rayuwarshi ko mutuwanshi ne?"
kara shake wuyanshi tayi tace "kaseem kana nufin nice nasa taje da wuta?"
yace "idan bake bace me yasa kika kashe ta? sannan kalman A ba Ammi yake nufi ba?"
tureshi tayi ta kwala ihu cikin tashin hankali tace "kaseem ni kaɗai ce me farin suna da A a wannnan gidan? ni kaɗaice?"

Juya baya yayi yace "ke take nufi"
cikin zafi da raɗaɗin rai tace "Abi shine sarki Abdallah ba A bane? Aminat itace minat ba A bace? Abdulhameed shima ba A bane? ko kuma wannan bakuwar da kuka kawo itama ba Aneeta bace A ce ko ba A ba?"
da ihu tace "kaima ba A bane? ko ka manta asalin sunanka Alkaseem ne?"
shima da ihun kamar zai fasa ɗakin yace "sunana ba Alkaseem bane sunana kaseem ne"
tana kallon cikin idonshi tace "ba zaka taɓa canjawa tuwo suna ba kaseem sunanka na gaskiya shine Alkaseem"
jikinshi yana rawa yace "karki kara kirana da Alkaseem"
tana huci tace "idan kuma na kara fa me zakayi? me zakayi Alkaseem"
ganin yana nufota Abi wanda ya gama sankarewa a wajen yace "kaseem!!!"
tsayawa yayi yana huci, yace "ko taku ɗaya idan ka kara zan tsine maka"
bai kara ko taku ɗaya ba kawai ya juya baya, ammi tana kuka tace "kowa ya manta da baya, nice kaɗai ake ganin laifina kowa ya manta da abinda ya aikata a baya, wallahi tallahi saina tona"
sultan yace "please ammi dan Allah kiyi shiru"
tace "nayi shiru sultan? nayi shiru ana zargina? bayan kowa abin zargi ne a gidannan, har an manta farin sunan kowa nice kaɗai aka tuna nawa? ko kun manta wanda yake kulle a bayan gidannan shima ba A....."
kujeran da hameed yake zaune akai ya ɗaga da karfi ya buga da kasa jin abinda ya faɗa, duk suka kalleshi a firgice, huci yake yi jikinshi yana wani irin rawa yana kallon ammi da idanunshi da suka rikiɗe suka koma jajur, take ya canja daga hameed ya koma asalin Abdulhameed, ammi ɓuya tayi a bayan sultan ganin yadda kujaran ya karye ga kuma hanunshi daya dunƙule yana huci sosai kamar zaki.

_Jiddah Ce..._
 08144818849