MAGEN KULU: Labarin HIKAYA Fita Ta 2
Na
Hauwa'u Salisu (Haupha)
Sai mutane suka ci gaba da kallon-kallo kowa hankalinsa a tashe. Zuwa yanzu babu sauran fusatar dake kwance a kan fuskokinsu sai wani munafikin tsoro daya bayyana muraran kan fuskar duk wanda ke gun.
"HAUWA MAI ƘOSAI ! Ita ce kalmar da manyan ciki ke ambata kamar su watsa da gudu.
Wata irin ƙara ta cika gun marar daɗin saurare wadda tilas suka saka hannuwa suka toshe kunnuwansu saboda yadda take barazanar kashe ma su dodon kunnuwa. Sautin maganar da babu tantama da maganar fatalwa tai kama ta ci gaba da cewa cikin amon muryarta marar daɗin saurare.
"HAUWA MAI ƘOSAI dai nake magana kanta wadda kuka halaka tare da magenta ta hanyar rufe su da ransu. Don haka kowa ya shirya domin tilas ku biya zunubin da kuka aikata."
Tsit wajen yayi komi ya koma kamar yadda yake.
Mai gari ya dubi mutanensa ya ga yadda baki ɗaya suka razana sai ya samu kanshi da fi su razana musamman daya tuna furucin da yayi wa KULU da Magenta.
Ba wanda ya ce wani ya zauna kawai ganin dacewar zaman nasu su kai don neman mafita a gare su baki ɗaya.
Wani dattijo ne ya yi gyaran murya ya fara magana.
"Tabbas muna cikin mugun mawuyacin hali a wannan gari namu, ku sani ba kowa ba ce MAGEN KULU illa HAUWA MAI ƘOSAI da Magenta, sai yanzu na fahimci hakan.
Nasan wasu ba su san wace ce HAUWA MAI ƘOSAI ba don haka ku saurara da kyau zan baku labarin ko wace ce ita.
"Shekaru ɗari da biyar da suka wuce, wannan garin mai suna Zabuwa yana zaune cikin kwanciyar hankali da lumana tare da wadatar arziƙin noma.
A wancan lokacin Sarki Yakubu ke mulkin garin nan ya kasance mutum marar kirki na gaske sai dai yana da yaro guda mai suna Muhammad wanda shi kuma yaro ne amma mai tausayi da jin ƙai na talakawa.
A kwai wata kyakkyawar yarinya mai suna Hauwa wadda babu macen da ta kai ta kyau da haiba duk cikar garin Zabuwa da kewayensa. Hauwa marainiya ce iyayenta duk sun rasu tana zaune gun Kakarta Jiddo wadda ita ce ta ci sunanta, kasancewar Jiddo bata gani yasa Hauwa tun tana ƙarama take saida ƙosai ƙofar gidansu, wanda duk garin Zabuwa kowa ke mamakin yadda yarinya ƙarama kamar Hauwa ke sarrafa ƙosai ya fi na kowa.
A nan wajen sana'ar ne Yarima Muhammad ya zo wucewa ya ga yadda mutane suka cika gun ya dakata don ganin abin da ke faruwa. Lokacin da ya ga yarinya ce ƙarama ke toya ƙosai mutane haɗa na wajen gari ke rubibin siye sai mamaki ya kama shi, don haka sai ya isa gun don da nan aka dare fadawa na yi ma shi kirari har ya isa gaban Hauwa ita kam sai aniyar tuya ƙosan take ga wata farar mage a kusa da ita sai cin ƙosan take hankali kwance.
Hauwa ta dubi Yarima ta ci gaba da abin da take sai da ta tsame ta zuba a leda ta miƙa ma ɗaya daga cikin bafadensa ta ci gaba da toya ƙosai bata ce ma shi ƙala ba.
Yarima yabar gun yana yaba yadda Allah ya yi wa yarinyar kyau a ransa.
Ko da ya isa gida ƙosan ya fara ci ba ƙaramin mamaki yayi ba jin yadda ƙosan ke da daɗi na daban.
Ɗaya daga cikin fadawan ya tambaya yarinya mai ƙosai, da ya ji labarin marainiya ce Kakarta Jiddo kuma bata gani sai ya ji ya ƙara tausayawa yarinyar ta wani gefen kuma ta birgeshi yadda tana ƙarama amma ta zaɓi ta yi sana'a don kare mutunci da martabar ta .
Daga ranar kullum sai Yarima ya je da kansa ya amso ƙosai amma kalma guda bata taɓa haɗa shi da Hauwa ba.
Labari ya iske mahaifinsa don haka ya kira shi ya zazzage shi ya tabbatar ma shi da duk sanda ya sake zuwa gun yarinya mai toya ƙosai sai ransa ya ɓaci.
Sai dai Yarima ya kasa jurewa dole ya take umarnin mahaifinsa ya sake zuwa gun Hauwa mai ƙosai sai dai ya sauya dabara ya je shi kaɗai kuma da wuri ya iske ta ita kaɗai da magenta tana ta aikin hura wutar toya ƙosan bai damu ba ya shiga taya ta magenta na gefe tana ta tsalle, shi kanshi Magen tana birgeshi duk sadda ya zo gun har ya tafi rabin kallonsa gun magen ya ke da mai Magen .
Yau dai Hauwa har gaida Yarima ta yi abin da ya dasa wata sabuwar ƙaunarta a zuciyarsa kenan.
Kaskon farko ya ɗauka zata zuba ma shi amma sai ya ga ta juye shi duka cikin wani tire Magen nan ta fara ci bata damu da ko zafin ƙosan ba.
Sosai yayi mamaki yadda ta juyema Mage kaskon farko duka amma sai ya share har ta soya na biyu ta zuba ma shi ya amsa ya tafi yana jin farin ciki.
Kowa yasan yadda Hauwa ke son Magenta a garin domin duk inda zata je da Magenta take tafiya ba wanda ya taɓa ganinta babu Magen duk inda ta saka ƙafa Magen zata maye da nata ƙafafun.
Kowa yasan idanun Mage kala guda ne amma ita Magen Hauwa idonta kowane da kalarsa haka su ke ɗaya fari ɗaya ruwan ƙasa, tun mutane na maganar idanun Magen har suka gaji suka daina domin dai haka suke dare da rana idanunta.
Sannan bata yadda da kowa Magen idan ba Hauwa ba sai daga baya ne ma aka ga ta fara yadda Yarima na taɓa ta har tana hawan jikinsa tana wasa.
Lokacin da labari ya iske Sarki Yarima bai daina zuwa gun Hauwa mai ƙosai ba sai ransa ya ɓaci nan take yasa aka kamo ma shi Hauwa da Jiddo zuwa fadarsa, yayi ma su wulaƙanci sosai ya ce ya ba Shafi'u mai rake auren Hauwa nan da sati guda.
Hauwa taita kuka ta kamo Jiddo suka dawo gidansu Magenta nata kallonsu kamar wata mutum tana son yin magana.
Yarima Muhammad da labarin ya iske shi sai ya kwanta rashin lafiya, a duniya kuma babu wanda Sarki ke so irin Muhammad don haka sai ya sake jin tsanar Hauwa sosai ya kudurce sai ya nuna mata mulki ba wasa bane haka jinin sarauta ya fi karfin jinin matsiyaci.
Shafi'u mai rake kuwa sai washe baki yake domin dai ko banza ya ci tuta har biyu na farko ya samu macen da babu kamar ta duk garin sannan yayi takara da Yarima ya buge shi.
Duk da Yarima bai zuwa haka Hauwa ke zuba ƙosai a leda ta ba Magenta ta kaima Yarima kullum tun ba a lura ba har mutane suka ankara sai labari ya fara tashi na Magen Hauwa fa ba Mage bace kawai domin Mage bata abubuwan da take.
Ranar Asabar aka ɗaura auren Shafi'u mai rake da Hauwa wanda baƙin ciki yasa Jiddo ta haɗiye zuciya ta mace a ranar bata ga auren Hauwa ba.
Ranar ma anga abin mamaki domin Magen ta haye gawar Jiddo tana kwararar hawaye kamar mutum.
Wani tashin hankalin kuma Sarki ya ce Hauwa ta ci gaba da zama gidansu da Jiddo babu inda za a kaita kuma ko haki bai bata ba.
Tun a ranar Shafi'u mai rake ya fara tsegumi akan MAGEN HAUWA abin da yasa Hauwa ta ce ma shi ita da Magenta mutu ka raba ba zata taɓa rabuwa da magenta ba.
Sannan ba zata daina sana'ar ƙosai ba har abada domin Magenta ƙosai kawai take ci take rayuwa.
Shi kuma Shafi'u babu abin daya tsana sama da MAGEN HAUWA don haka ya fara bin mutane yana cewa Magen Hauwa ta tsafi ce.
Yarima Muhammad kuwa yana kwance bai iya cin komai bai iya komai abu guda yake iya ci shi ne ƙosan Hauwa da kullum MAGEN HAUWA ke kawo ma shi.
Ranar da Sarki ya yi ido biyu da Magen a ranar ya tuna wani tsohon mafarkinsa akan MAGE mai ido kala biyu ɗaya fari ɗaya ruwan ƙasa.
To fa ! Wane mafarki ne wannan?
Yarima Muhammad na warkewa kuwa ?
Ya zaman Hauwa da Shafi'u zai kasance ?
Me ya sa MAGEN HAUWA ke da kala biyu a idonta ?