Ina Baiwa Samari Da 'Yan Mata Shawara Su Mallaki Littafan A'isha Ahali-- Sheikh Ibrahim Khalil

Ina Baiwa Samari Da 'Yan Mata Shawara Su Mallaki Littafan A'isha Ahali-- Sheikh Ibrahim Khalil

 

Daga Ibrahim Hamisu, Kano

 

A ranar Lahadi da ta gabata ne aka kaddamar da littafai biyu, Sirrin kwanciyar Hankali (Mijinki a jakarki/ Matarka a aljihunka) da Mace- Macen Aure a Ƙasar Hausa wake da laifi? na A'isha Aminu Ahali ya gudana a makarantar Kwalejin Shari'ar da addinin Musulunci (Legal) da ke Kano.

 
Tun da farko a jawabinsa, mai sharhin littafin, Sheikh Ibrahim Khalil ya ce  hakika wadannan littafai ne masu muhimmanci, wadanda bukatar su ga al'umma ba zai ƙare ba har tashin alƙiyama, saboda suna magana ne akan zamantakewa aure, shi kuma aure yana nan har tashin alƙiyama.
 
Sheikh Ibrahim Khalil ya ƙara da cewa "samari da ƴan mata ya na da  muhimmanci su mallaki littafan su karanta har su haddace su, kuma idan za su kwanta bacci  ma su karanta su.
 
"Kuma ina shawartar Kowane Uba da uwa ya sayawa ƴaƴansu domin karanta littafan muhimmin abu ne a cikin al'umma" 
 
Sannan ya shawarci marubuciyar da ta dora littafin a (Cloud) ta yadda za'a a iya karanta shi ta online.
 
Littafan biyu dai sun  samu sanya albarka ga malamai da masana ilimin zamantakewa da Likitoci.
 
Taron dai ya samu halartar manyan baƙi kamar su Dr. Bala Muhammad daga Jami'ar Bayero da Ado Ahmad Gidan-Dabino wanda shi ne shugaban kwamitin kaddamarwa da manyan ƴan kasuwa irinsu Alhaji Munzali Muhammad da Alhaji Sani Isa Abubakar da wakiliyar Kwamishiniyar harkokin mata da Wakilin Arewa Alhaji Sayyadi Muhd. Yola da Sheikh Shehu Mansur Dala, da al'umma maza da mata.