ZAMAN JIRA: Fita Ta Biyu

ZAMAN JIRA: Fita Ta Biyu

ZAMAN JIRA


               *NA*
*HAUWA'U SALISU (HAUPHA)*


( _Book 1_

                           Page  2


Ganin bata da mafita yasa ta ja ƙafa ta nufi ƙofar gidan, ba irin hangen da ba tai ba amma bata ga komai kama da Asiya ba, don haka jiki a sanyaye ta ja ƙofar ta rufe tana jin sabon zazzaɓi na sauko mata. Baƙin ciki fal ranta haka ta koma ɗakin, sarkin ya cire kayansa ya yi shame-shame yana jan wani nishin iskanci, hannu ya miƙo mata, bata san zuwa har ƙasan ranta amma sai ta samu kanta da miƙa mai nata hannun ta faɗa jikinsa. Bai jira komai ba ya fara yamutsata ta ko'ina yana sinsina ta. Hawaye suka zubo mata yana jin saukar su ya tashi zaune a razane ya juyo da fuskarta dai-dai saitin tashi fuskar ya ce,   "Madam kuka kike akan me? So kike ki shiga tsakanina da samun natsuwata ne, anya kuwa kin yi min adalci a matsayina na wanda ke fafutukar nema maki natsuwa a kodayaushe ke? Shin kin san kuwa yadda na ci burin zuwa duniyar sama a daren nan saboda yadda ki ke kaini sama ta bakwai ba ƙarya? Ki sani idan ina cikin alherinki ban ji ban gani, haka ban sanin cewa akwai wata mace mai alherin da ya kai naki daɗi da zumar lasa mai tsayawa a rai. Don Allah ki dinga yi min adalci kamar yadda nake maki kin ji Madam ɗina?" Jiki a sanyaye ta ɗaga mai kanta, amma saboda tsabar mugunta irinta na Nafi'u sai ya ce, "Madam na lura baki cikin farin ciki bari na je wani gun gobe mun haɗe." Kafin ta samu damar cewa wani abu har ya buɗe ɗakin ya fice ya barta zaune baki buɗe. 
Bata taɓa jin takaicin rashin waya ba sai yau, da ace tana da waya yau da ta huce rabi da kwatar baƙin cikin da Nafi'u ya jefa ta ciki. Tsabar rashin adalci da cusa takaici sai da ya kori yarinya cikin dare sannan kuma ya dube ta ya gaya mata cewar zai je wani gun har ma ya kwana can. Tabbas Nafi'u mugu ne na bugawa a Jarida kuma tantirin marar mutunci ne, amma ta rasa ya akai bata iya yi mai musu balle rashin kunya, duk yadda zai ci mata mutunci ya yi mata rashin daraja bata iya buɗe baki ta gaya mai baƙar magana ko magana marar daɗi, haka duk wahala duk takaicinsa da take ciki bata iya ma shi musu akan abin da yake so tai mai ko da kuwa tana ji a ranta idan ta aikata abin za ta iya mutuwa ne to sai ta aikata shi. 
Ba yadda ba tai ba akan ya barta ta riƙe waya ba, ya ce mata ko a mafarki ya ga matarsa da waya yasan ya zama ƙaton banza, babu matar da zai aura ya kawo ta gidansa ya aje yana jibga mata abinci yana narka mata zumar daɗi kowace rana kuma ta dinga amfani da waya, salon wani ƙaton ya yi mai bazata ya taya shi zuwa duniyar sama bai sani ba yana nan sake da baki kamar gaula.
Yadda ta ga dare haka ta ga safiya, ga zazzaɓi ga damuwa ga tana tunanin yadda Asiya ta isa gida. 

Washegari shiru-shiru bata ga Nafi'u ba, haka ba wanda ya zo daga gidansu, hakan na nufin sun yi fushi da korar Asiya da Nafi'u ya yi jiya kenan cikin dare. Ganin ba wata mafita, sai ta tashi ta nufi haɗa masu kalaci (breakfast) domin kar da maigidan ya zo ya iske ba tai komai ba wani bala'in ya sameta kuma. Tana gamawa kuwa yana shigowa sai wata gyatsa yake yana cewa, "Kwanta fadamar rake, kwanta cakwaikwailar daɗi."  Ta san sarai abin da yake nufi amma bata isa ta furta ko da kalma guda ba, sai ma samun kanta da zuwa yi mai barka da dawowa da tambayar a haɗa mai ruwan wanka ko sai ya gama karyawa zai wankan? Yana shafa ƙaton cikinsa da ya baje kamar takalmin Falke ya ce, "Anya kuwa duk don yanzu zan iya saka wani abinci a bakina bayan yanzun nan na sauko daga duniyar sama? Kodayake haƙƙina ne kawo min na ɗora kan gyaran safiyar nan da aka ban,ai na yi kwanan daɗi ba ƙarya."  Bata ce komai ba ita dai ta jera mai komai ta wuce ɗaki tana jin tashin zuciya kamar za tai amai.  Ya ci ya ƙoshi ya kama buga gyatsa ya nufi ɗakin ya ce ta kai ma shi ruwan wanka. 
Bayan ya fito daga wanka ta je gabansa ta duƙa tace, "Don Allah ka taimaka ka kaini gidanmu, saboda na ga ba wanda ya zo kasan fushi su kai da tafiyar jiya da Asiya tai cikin dare."  Shafa gefen fuskarta ya yi ya ce, "An gama Madam amma sai na fara kai ki asibiti an ida tabbatar min da ƙwazona ya sauka sannan na kai ki gidan naku masu gida."
Bata da yadda za  tai dole ta shirya suka tafi.


                       ***************

                               GIDAN JABEER 


"Hehehe duniya juyi-juyi kwaɗo da ya faɗa ruwan zafi. Kai yanzu Jabeer ban da samun wuri gaɗa a silma ina kai ina cewa kai ne mijina a tsakiyar titi, wallahi wannan ya zama na ƙarshe idan ba haka ba tsab zan maka rashin dajarar da za kai mamakin ta a bayyane." Cikin natsuwa da murmushi ya ce, "Ki yi haƙuri Hajiyata hakan ba zai sake faruwa ba, shi ma wannan kuskure ne ban zaci ran Hajiyar tawa zai ɓaci har haka ba. Amma in sha Allah daga yau ɗin nan ba zan sake gangancin ganin wannan kyakkyawar matar tawa ba na ce tawace a kan titi ba kamar yadda ta umarce ni." Wani wawan tsaki ta saki ta shige ɗaki, domin shigowar ta kenan gidan ta hau shi da bala'in akan me zai ganta a hanya ya nuna ya santa har ma da nuna ta a matsayin matarsa ga wasu banzanyen abokansa. Nusaiba kenan matar Jabeer.
Tana shiga ɗakin ba jimawa ya shigo, ko kallo bai ishe ta ba, ga alama ma bata ji daɗin shigowar shi ɗakin ba, don haka ba tai ƙasa a gwiwa ba ta dube shi a sheƙe tace, "Oga a ɗan fitar min ɗaki zan yi sirri, koma ba sirri zan ba ai ya kamata a dinga ba mutum iska yana sakata yana walawa a cikin ɗakin da aka taru a kai mai fin ƙarfin masifa aka kawo ni cikinsa ba da amincewa ta ko amincewar Gyatuma ta ba, amma hakan ba matsala ba ne ba, domin nasan yadda mutum ya sa ni zaman jira shima haka zai kasance cikin zaman jiran da zai mutu bai ƙare zaman jiransa na gawun shanu ba."  Ya isa inda take kwance ya kama hannunta ya riƙe ya ce, "Allah Ya baki haƙuri, dama na zo ne naji ko kina buƙatar wanka ko dai wani abu daga gareni." Taɓe ƙaramin bakinta ta yi bata ce komai ba. Ganin haka shi kuma ya ci-gaba da murza mata hannun a hankali ya fara matsa mata jikinta. Nan da nan labarin ya sauya ta manta duniyar da take ciki ta fara maida ma shi martani mai zafi. 
Duk yadda Jabeer yake damuwa da halayen Nusaiba yana jin daɗin zama da ita a fannin auratayya, nan ne kawai inda yake cin karensa babu babbaka kasancewar Nusaiba ajin farko ce a fagen , don shi kanshi wani lokacin sai tayi kamar ta kai shi ƙasa sai ya nuna mata ruwa ba sa'ar kwando ba ne, bai yiyuwa ta kowane fanni ace ita ce ke riƙe da karagar shi. Kuma ya lura da gaske hakan na yi mata daɗi, domin duk inda take idan ƙararrawar ta kiɗa sai ta dawo gida a fujajan gun shi, idan kau bai gida ta ci-gaba da kiransa a waya kenan tana ihu ya zo kar ta mutu tana zaman jiran shi. To shi kuma da ya ga hakan sai ya dage ya riƙe kambun kodayaushe da kalar fasahar da yake zuwa mata da ita idan sun tafi duniyarsu. 
Bayan komai ya kammala ya shiga ya haɗa mata ruwan wanka, ya dube ta yana gyara tsayuwa ya ce, "Hajiyata ko akwai sauran arnan da ban kashe ba ne na dawo fagen fama yanzun?" 
Tasan halinsa sarai duk jarabarta shi ne ubanta idan za su yini kashe arna ba abin da ya dame shi sai ma sake style kawai da zai dinga yi yana bijiro da sabbin arnakun yana sheƙewa. Sai dai wannan shi ne kawai abin da take so a gun Jabeer daga shi fa sai ɗan kyan da yake da shi ba laifi da ace bai da kyau tabbas da sai dai Gyatumi ya tsine mata albarka amma ba za tai auren muni da talauci ba tana kyakkyawar gaske ajin farko ga wayewa ace ta auri mai fuska kamar an mari dawo ba. Ganin kamar ta yi nisa a tunani ya isa inda take ya shafa fuskarta, "Hajiyata ya dai, ko dai ban kashe arnan nan da kyau ba ne yanzu na saka rigar siliki na koma fagen daga kai tsaye?"  Ba dan taso ba kawai murmushin mamayarta ya yi da bata sake shi ya fita ba. Amma sai ta share ta yi juyi tare da miƙa ta miƙa mai hannu alamar ya tada ta tsaye. Haka akai kau, daga nan ta faɗa toilet yana bin shi da harara ta ƙasa -ƙasa ganin da gaske yake a koma duniyar sama bai gaji ba ga zahiri nan ta gani. Ba kuwa za ta biye mai ya ƙwaƙule komai ba, domin akwai wadda ke jiranta za ta saka ta cikin alherinta, shi ma kawai ta ba shi ne domin tasan idan ta fice sai dare zata dawo gidan, kuma yasan makaman da yake amfani da su ko bata shirya zuwa fagen kashe arnan ba dole ta je.

Bayan ta fito ta tsala kwalliyar gaske, ta dube shi ya tsare ta da idanu kamar sabon maye ta ɗan ja ƙaramin tsaki ta ce, "Ogan kallo ban key ɗinka domin ba da motata  zan fita ba."    Sosa kansa ya yi, "Sai dai babu mai sosai a cikinta gaskiya."  Tsaki ta ja, "Kai dai ka sani, ni miye damuwata da hakan indai zai kai ni gidan mai na zuba? Kodayake kamar ma akwai mai a motana, mu je ka zubamin shi."  Tana gaba yana baya suka fice zuwa gun motocin, ya buɗe ya ɗauko man fetur a jikin jarka a cike ya zuba kwata zai rufe tace ya cika tankin kawai, ya kalle ta zai magana ta maka mai harara, bai ce komai ba ya bi umarni.  Yana gamawa ta faɗa motar bata ce komai ba ta fara bata wuta, ganin haka ya je ya buɗe mata gate yana adawo lafiya amma ko ta kalli inda yake balle ta ga me yake yi ma.

Kai tsaye titi ta harba kan motar, sai da tayi tafiya mai nisan gaske sannan ta shiga wani lungu ta kira waya, ba a jima ba aka ɗauka tace, "Yanzu haka ina inda ki kai min kwatance a tsaye." Ta kashe wayar ta sake gyara baƙin gilashin dake fuskarta, ta ɗauko turare daga cikin jakarta tafesa ta ɗauko wani ƙaramar kwalba ta buɗe bakinta ta fesa a ciki, ta sake buɗe wata sweet ta jefa a bakinta.  Jin ana ƙwanƙwasa mata ƙofa yasa ya buɗe su kai ido huɗu da wadda ta zo gun. Cike da yauƙi da yanga ta sauko daga cikin motar suna jifar juna da murmushi, ɗan rumgume juna su kai irin na gaisuwar nan sannan suka juya suka koma motar ta nuna mata wani ƙaton gida dake buɗe tace su isa can. Ko a motar hannun Nusaiba na cikin na matar wadda kallo guda zaka gane ta kusa haihuwar Nusaibar ma. 
Suna shiga ta kashe motar matar da kanta ta je ta rufe gate ɗin gidan ta dawo ta ja hannun Nusaiba suka nufi cikin gidan tana shafa Nusaibar.
Wani kyakkyawan ɗaki suka shiga sai ƙamshi yake ya sha gyara ta ko'ina, kai tsaye gado suka nufa suka faɗa suna maida numfashi kamar waɗanda suka sha uban gudu. Nusaiba ta dubi matar fuska cike da fara'a tace, "Ban taɓa tsammanin zan ga wannan ranar ba, saboda yadda Besty ta kankane komai ta hana ko gaisawa mu dinga yi sama-sama ba, na rasa baƙin cikin da take min na shan wannan garar ba, amma yanzu ai ga shi bata san zan buge wannan kaya ba cikin sauƙi da shauƙin da ko ita bata taɓa tsinkayar sa ba. Suka sake rungume juna suna sakin murmushi na musamman. Nusaiba ta gyara gashin matar da ya zubo mata a fuska tace, "Yanzu a cikinmu ya kamata a fitar da mata a fitar da mijin, amma kamar a ban mijin domin ina ga kamar zan fi ki ƙwazo wajen nemowa da miƙawa." Ita ma ta ƙara shigewa jikin Nusaibar tace, "Ban yadda ba, sai dai idan yanzu an gwada an ga wanda ya fi juriya sai ya ɗauki kanbum, amma yanzu a haka ai ba za a iya gane maci tuwon ba. Ya kina shan kayan ruwa ko kanki a rufe yake ta nan wajen ?" Nusaiba ta bushe da dariyar farin ciki tace, "Anya kuwa kin san wacece Nusaiba, to da kika ganni nan babu ruwan da ban afawa na afa na lungu ma balle na sarari. Mu je mu fara da can sai mu dawo nan sai lamarin ya fi tafiya cikin armashi ma." Baki ɗaya suka miƙe suka nufi wani ɗaki dake jikin ɗakin kujeru ne jere amma sai Nusaiba ta baje kan carpet  tana lumshe idanu, domin har ga Allah ta ƙagara tai abin da ya kawo ta, akwai inda za ta je daga nan ba iyakar tafiyar nan ba. 
Sun jima suna bankar kayan maye, sai da su kai makas ba tare da sun koma ɗakin ba suka faɗa ma juna kamar wasu karnukan farauta... Sun jima suna aikata abin da suke da muradi sai dai sun gane dukkan su ba kanwar lasa ba ne ba a fagen hakan ya faranta masu rai ya ƙara masu kusanci da juna sosai. Sai a lokacin Nusaiba ta dubi matar tace, "Besty bata taɓa gaya min sunanki ba sai dai labarinki kawai take ban, wanda yanzu sai dai na ba wani, don haka faɗa min sunanki, ni dai Nusaiba sunana amma da Nunu duniya ke kirana yanzu haka."  Ita ma tai dariyar nishaɗi tana lashe leɓenta tace, "Sunana Ruƙayya amma da Ruky duniya ke kirana, sai dai ke ban amince ki kirani da ko ɗaya ba a ciki sai dai ki ban naki sunan daidai da duniyarmu ni da ke."   Nusaiba ta yi ɗan gyaran murya tace, "Ba abin wahala ba ne samar maki da suna ba yanzun nan, don haka ki zaɓa a cikin ukun da zan lissafo nasan tabbas za ki dace da daidai ke a ciki." Ruky ta zuba ma Nusaiba ido tana jin tamkar su sake komawa don wani sabon salo ke bijiro mata yanzu haka, ta daure tace, "Kunnuwana biyu amma na ƙara maki guda don jin sunayen."  Nusaiba ta sake muskutawa tace, " Na farko 'Banda', na biyu 'Tawa' na uku 'Ƙarshe' domin ke ɗin ƙarshe ce a duniyar ruwa wallahi." Su duka suka bushe da dariya. Ruky tace, 'Na zaɓi Banda saboda kifin a kwai farin jini kuma ya iya suka idan zai sama cikinsa." 

Haka suka dinga fira cike da nishaɗi da jin daɗi tamkar wasu mace da namiji ƙarshe Nusaiba ta amshi kambun miji Ruky ta zama matar. Da zata tafi Ruky duk ta ruɗe ta rasa me za ta ba Nusaiba komi ta jajibo tasa mata a leda sai da tai mata leda uku manya na kayayyaki wasu na gyaran jiki wasu na mata ne da turaruka da atamfofi da lesuka sai da Nusaibar tace sun mata yawa sannan ta dakata. Nan take Nusaiba ta ji alert a wayarta tana dubawa taga wasu masu zafi ne Ruky ta tura mata, tai murmushi ta rungume Bandar tata suka kwashi kayan suka nufi mota. 

Tana shiga mota ta duba wayarta, miss call ɗin Alhaji Mannir ta gani har guda biyar, ta ja tsaki ta tada motar suna ɗaga ma juna hannu ta buɗe mata gate ta fice daga gidan.

Wayar ce dai ta ci-gaba da ringing shi ne dai yake kiranta, har a ranta bata jin daɗin mu'amala da Alh. Mannir kawai kuɗaɗen da yake bata ne take jin daɗin su amma shi sam bai iya tafiya da mace ba ta fannin soyayya ba, sai dai ya yi kwance tiƙeƙe ki yi ta wahala kina kai da kawowa ke kaɗai ya saki uban tumbi kamar banten sakarai yana wani gurnani mai kama da kukan jaki wai shi ala dole kukan daɗi yake ya hau network mai sarvice. Sai da taga bai da niyyar daina kiran ta amsa murya ba yabo ba fallasa.

Nusaiba, "Ina jinka, lafiya kake ta kirana ba ƙaƙƙautawa?"

Alh. Mannir,  "Ina fa lafiya tun jiya nake mafarki dake na rasa sukuni har irin kallon nan da kika turamin a waya duk na kalla amma sai gaba abu yake maimakon baya."

Nusaiba bayan ta ja tsaki,  "Ni kam na shiga uku da kai Alh. shike nan kuma babu wata macen da zaka nemo sai ni kamar ni kaɗai ke baje maka kana ci, ban san tsinanniyar takura wallahi haba !

Alh. Mannir cikin muryar ban tausai,  "Ki yi haƙuri wallahi ban taɓa haɗuwa da macen da take saka ni manta kaina ba irin ki, kin san duk wata makamar kai mutum sama ta bakwai ne Nunu."

Nusaiba ta sake jan tsaki da ƙarfi,    "Gaskiya ka nemi wata ni yanzu a cike nake ban buƙata... Ta kashe wayar ta jefar saman kujerar mai zaman banza.

Alh. Mannir jin ta kashe mai waya, ya dafe kansa, can kuma ya miƙe tsaye ya fara kai da kawowa. Tun da ya haɗu da Nunu ya daina shaida daɗin kowace mace a harkar sama, hatta iyalinsa bai gane inda suka dosa kawai dai yana yi ne ba don yana gamsuwa ba. Ita kuma ya lura duk kashe mata kuɗaɗen da yake, duk bajintar da yake mata sam ba shi ne a gabanta ba. Duk lokacin da zai haɗu da ita sai ya yi fama da ciwon kai wani lokacin har zuciyar shi tai kamar ta fashe don tashin hankali, saboda sai ta gama buga mai kai jikin duwatsu kafin ya samo kanta. Da farko kuɗaɗen da yake bata suna taimaka mai wajen shawo kanta da sauƙi amma yanzu ya lura ko su ba wani damuwa tai da su ba daga gare shi duk kuwa nauyinsu idan ya bata ko a fuska bata nuna ya yi mata bajinta ko ta nuna ta ji daɗin su. Yanzu ya zai yi kenan, abin da kawai ke damunsa kenan ya rasa mafita. 
Sake kiranta ya yi amma ta ƙi amsawa, ya koma ya tura mata kuɗi masu sunan kuɗi sannan ya sake kiranta amma sai ma ta danna ma kiransa busy, zufa ta cigaba da wanke shi duk da AC da fankar da ke aiki a ɗakin jikinsa bai san suna yi  ba.

Ƙarar hon ɗin mota ya ji a ƙofar gidan, ya leƙa ta window domin yaga waye, shi dai a saninsa bai ba kowa damar zuwa ya gan shi a wannan gidan ba. Mamaki ya cika shi ganin bai ma san motar ba, ya koma ya ɗauki waya ya dawo wajen window ɗin domin ya kira maigadin ya ce ko waye ya koma. karkarwa hannunsa ya kama ganin wadda ta fito daga cikin motar, Nunu ce ta ci ɗan bala'in wanka. Daɓas ya faɗi zaune yana jin kamar an yi mai gafarar zunubansa. 

Har ta shigo inda yake bai samu ya motsa ba sai da ta manna mai kiss a kumatu sannan ya dawo hayyacinsa. 
Tana karairaya ta zauna gefensa sai kuma ta zame ta ɗora kanta bisa cinyarsa tace, "Kana damuna wallahi baka da haƙuri indai a har kan ansar lamari ne wallahi Alh." 
Ya wangale bakinsa duka ya yi ajiyar zuciya ya ce, "Ke ce daɗinki ya yi yawa wallahi, kin riga kin amshe na kowace mace kin ƙara da naki ina naga ta haƙuri kau?" 

Murmushin jin daɗin yabon da yake mata ya ƙwace mata, ta lumshe idonta ta buɗe su ta watsa mai su nan take ta ida rikita shi ya ida sauka layin network ɗin baki ɗaya.
Ita kam dama da gaske ba wani buƙata take ba, kamar yadda tace ta riga ta kai geji amma da yake tasan ba wani abin kirki yake iyawa ba yasa ta zo, domin a ƙa'idarta dama sai ta kai geji take zuwa gun sa domin nan da nan yake sauka daga network ya koma gefe yai ta sheƙa barci yana sakin tusa. Bata taɓa manta ranar da ya nemi ya maida ta mahaukaciyar ƙarfi da yaji ba,ita bata san bai da ƙarfin network ba sai da suka hau network ɗin faka-faka taga ya sauka bata ankara ba ta ji tashin minsharinsa tana ƙoƙarin tada shi kawai ta ji ƙarar wata uwar tusa, wadda shi kan shi sai da ya juya dan azabar ƙarar sautinta. 
Ga shi ya riga ya kunna mata network har ita kuma ta kunna data amma kuma sai ya koma ya noƙe ya yanke service ɗin kai tsaye. Ganin ta rasa mafita yasa ta fice a hargitse ta koma gidanta nan ma ta iske Jabeer bai nan ta kira wayarsa ta ƙi tafiya, ta kuma san a yanayin nan da take cikin ƙarfin network ga datar ta a kunne babu wanda zai iya da ita sai Jabeer sauran duk kame-kame ne. Kawai kuka ta fashe da shi ta shige toilet ta dinga watsa ma jikinta ruwa, amma dai network madadin ya sauka sai ƙara samun wadatar sarvice yake. Hankali tashe ta fito ta sake ɗaukar wayar ta kira Jabeer cikin sa'ar gaske kiran ya shiga yana ɗauka ta fashe da kuka ta kasa cewa komai. Daga can hankalinsa ya tashi ya dinga tambayar tana ina, da ƙyar tace tana gida ta kashe wayar. Sai a lokacin ta samu sukuni tasan cewa yanzu datar ta za tai mata amfani tai downloading har ta gaji. 

Bawan Allah hankali a tashe ya shigo gidan, ko gani bai yi ya isko ta ɗakin yana tambayar ta abin da ya same ta kawai ta faɗa jikinsa ta haɗe bakinsu waje guda ta fara ƙoƙarin cire mai kaya. Nan take ya fahimci karatun don haka sai ya samu natsuwar taimaka mata cire kayan suka faɗa duniyar da take mata daɗi fiye da kowace...
Jin hannun Alh. Mannir cikin rigarta yasa ta dawo daga tunanin da take, ta dube shi ta narke fuska tace, "Ban da mota fa yanzu, baka ga aron ta Jabeer na yi ba na fito?"  Bai fasa abin da yake ba ya bata amsar, "Na lura yanzu ban cikin natsuwa ne idan kin dawo min da ita sai mu yi maganar duk da ta zo cikin sauƙi motocina sabbi na tafe da na sai ma matana guda biyu kawai sai ki ɗauki guda na ɗauki guda."  Murmushin jin daɗi ya ƙwace mata, daga nan ta ci-gaba da ɗora Alh. Mannir bisa network ɗin da bai sanin inda take samo datar kunna shi. 
Kamar yadda tace bata jima ba ta gamsar da shi, ta shige toilet ta watsa ruwa ta fito ta jawo jakarta ta sake caba kwalliya ta dube shi tace,  "Zan wuce, amma ka dinga ɗaga min ƙafa ban san zafin kiran nan naka don ma Jabeer ba wani damuwa yake da kiran da ake min ba ko wanda nake yi ba ai da ka dinga ja min masifa a gidana."
Yamutse fuska ya yi, "Ni fa da kin kashe wannan auren kin zo mun yi aure da ya fi wallahi, kuma na yi maki alƙawarin zan ba ki duk abin da kike buƙata zan fifita ki akan sauran matana indai kika amince."
Kallon baka da hankali tai min bata ce komai ba ta juya tana taku ɗaiɗai tace, "Ka saka min kuɗi a ɗayan account ɗina ba wanda kasa ɗazun ba." Har rawa muryarsa ke yi wajen amsa mata da "An gama ranki ya daɗe yadda kike so haka za ai maki."
Ita dai ko waigen shi ba tai ba ta fice ta barshi da ƙamshin turarenta.

Lokacin data koma gida, Jabeer na zaune yana karatun Alƙur'ani ta taɓe baki ta wuce shi sallamar da tai niyyar yi ma sai ta fasa ta jefa mai key ɗin motarsa ta wuce ɗakinta.

Gado ta faɗa don ba ƙarya yau ta amshi network mai kyau don Jabeer ba kanwar lasa ba ne haka ma Bandarta ba kanwar lasa ba ce bata saka Alh. Mannir a cikin waɗanda ta gani ma yau ita sam.  Nan da nan barci ya kashe ta ko takalmin ƙafarta bata cire ba.

Jabeer yana gama karatun ya shigo ya dube ta ya girgiza kai, ya rasa me yasa Nusaiba take da gandar gaske kanta ma bata iya yi wa abu, waje guda take da auki shi ne a shimfiɗa amma daga nan ba sai fagen masifa wannan kam ko da wa za ta iya karawa kuma ta ci shi da bakinta. Cikin natsuwa ya isa ya cire mata takalman ya zuge mata zif ɗin rigar ya ɓalle mata bra ɗin ta sake juyawa ya ida cire mata ya saka mata marar nauyi ya kwashe wadda ya cire ya adana ya haye gadon sosai ya janyo ta jikinsa sosai suka kwanta tare. 
Duk laifin da Nusaiba tai ma Jabeer da sun kwanta haka yake nemansa ya rasa, ya riga ya yi imani da cewa duk daren daɗewa zai mallaki zuciyar Nusaiba kamar yadda ya mallaki gangar jikinta, don haka bai damu da zaman jiran da yake na wayar gari da zuciyarta a hannunsa ba.

Ɗaya daga wayarta ne tai haske alamar saƙo ya shigo, kamar kodayaushe ya kauda kansa sai kuma ya jawo wayar ta notification yaga ashe alert ne, bai san lokacin da ya miƙe zaune ba ganin saukar miliyan biyar a cikin account ɗin Nusaiba ba. 

Hannu yasa domin ya tada ta daga barci ta faɗa mai inda ta samu waɗannan kuɗaɗe haka, sai kuma ya dakata saboda sanin hali yafi sanin kama, bai manta yadda akai cakwakiyar gaske ba kafin Nusaiba ta zama mata a gare shi ba sai da mutanen unguwa da kasuwa suka taru su ka kai ruwa rana sannan Nusaiba ta shigo gidanshi da sunan matar aure. Haka kowace rana sai ya tuna kalaman da tai mai na kashedi da kuma kalmar za tai zaman jiran wa'adinta a gidansa sai dai kar ya yi murna don ya same ta a cikakkiyar budurwa hakan ma wani tsani ne na zuwa wata duniyar sai dai ya saka a ran shi tabbas da tasan shi ne za ta aura da ta bi titi ta raba ma ƙatti budurcinta sun daka wawa! 

Cikin sanyin jiki ya fasa tada ta, ashe tana lura da duk abin da ke faruwa kawai zaune ya ganta kamar yadda yake zaune ta buga mai harara tace,  "Jabeer yaushe ka fara min bincike da shiga cikin lamurrana? Shin ban gindaya maka sharaɗin babu ruwanka da rayuwata ba? Yaushe ka samu saken shiga bigiren da babu ƙwayar hatsinka wajen shuka shi?"

Jikinsa ya kama kyarma ganin da gaske ranta ya ɓaci har idanunta sun sauya kala.
"Kaiii Jabeer !   ina maka magana saboda tsabar wulaƙanci za kai banza da ni? Don Allah ka ga nayi maka daidai da matarka ne? Kowa yasan cewa nafi ƙarfin zama matarka fin ƙarfi da son zuciya ne irin na Gyatumi yasa ya aura maka ni, kuma yanzun ka zo madakata don haka zan maka ku ƙara kotu daga kai har shi Gyatumin domin yanzu na yi ƙarfin da zan iya sakin rassan da za su saki wasu rassan.... Ba zato ba tsammani amai ya wanke mai fuska, daga shi har ita sai suka ruga toilet. 
Shi ya taimaka mata ta gyara jikinta bai ce mata komai ba ya miƙa mata gyalenta ya ja hannunta suka fice ko bata tambaya ba tasan asibiti zai kaita.

Bayan duk wasu aune-aune da akai mata suka maida ma Likitan ya dube su fuska cike da fara'a ya ce,  "Congratulations, tana ɗauke da juna biyu."   Hamdala sosai Jabeer ya yi ma Allah, ita kam ba yabo ba fallasa akan fuskarta sai ma tashi ta yi ta fice ta dubi Jabeer ɗin tace tana zuwa.

Wayarta ta ɗauko ta kira wata number ba a jima ba aka ɗauka,  "Duk duniyar da nake na jiki sai na ji duniyar ba tai min adalci ba domin tai min shamaki da kasancewa da ke Sahibata." Cikin farin ciki ta maida martanin  "Ni kaina haka ne sai dai nawa ma yafi naki tsauri, yanzu dai Sahiba na kira ne daga asibiti ne wai ina ɗauke da cikin Jabeer...    "What ! Ci me, gaskiya Sahiba ba zan iya ba, idan kika kama laulayi shike nan sai bayan kin haihu zan dinga bige network, kuma a zo ace baby rigima ba zai barni na sakata na wala ba? Gaskiya da sakel a cire shi yanzun nan Sahiba."  Kawai ta kashe wayar ba tare da Nusaiba tace ƙala ba.

Tsaye tai turus, duk duniya bata da masoyiya kamar Kursis duk abin da ta zama silar Kursis ne duk wani shege da take jan kaya Kursis ta haɗa ta da su. Akwai abubuwa da dama da Kursis ce silar samuwar su gare ta. Shin yanzu ya za tai, cire  cikin za tai ta bi umarnin Kursis ko ko ta bar shi? 


To jama'a kun dai ji wata sabuwa kuma.

Haupha.....