Babban Buri:Fita Ta Bakwai
BABBAN BURI
MALLAKAR DOCTOR MARYAMAH IBRAHEEM.
SADAUKARWA GA AISHA IDREES ABDULLAHI {SHATU} MARUBUCIYAR MATAR ABDULLAH.
FITOWA TA BAKWAI
~~~~"Me kuke son nayi masa?", a harzuƙe ya ce "Ba zaki tsawatar dashi bane?."
"In tsawatar masa ku ba iyayensa bane da baza ku tsawatar masa ba?." Cewar Hajiya Inna kenan tana me ɗauke kanta a kansu.
Buga kujerar da yake kai Alh Bello ya yi a harzuƙe kan ya miƙe ya dawo tsakiyar ɗakin cikin ƙaƙƙausar murya ya ce "ALIYU" ba tare daya jira amsawarsa ko akasin hakan ba ya ci gaba da cewa "Wallahi tallahi baka isa ka bijire mana ba, auren ɗaya daga cikin ƴaƴanmu tamkar ka yi ka gama ne , so kake mu zuba ma idanuwa a haka ba aure ne?, Shekarun ka nawa duniya?,mu badan komai muke son haɗa wannan auren zumuncin ba sai don riƙo da wasiyyar Mahaifinmu.
Ɗago da rikitaccin idanuwansa ya yi ya zuba a kansu waƴanda suke fess amman lokaci ɗaya suka rikice suka koma juwur saboda ɓacin rai, "sai yanzu kuka tuna da wasiyar?, to a karo na biyu iname ƙara tabbar maku da cewa ni ALIYU ɗan Aminu jika da Sulaiman Wurno wallahi tallahi ba ƴar dazan aura daga cikin ƴaƴanku, idan kuka kuskura kuka ɗaura wannan auren zaku sha mamaki na , zan baku mamakin da da wuya idan antaɓa bawa wani mahaluƙi shi".
Cewar Haidar kenan yana me tattara kayan sa domin barin ɗakin taron.
Kallo suka bisa dashi lokacin da yake ficewa daga ɗakin, ko wannensu zuciyarsa sai faffatniya nake yi basu taɓa zaton zai bijirewa umurninsu ba, sai gashi lokaci ɗaya abu ya rinciɓe masu.
Itama Hajiya Inna miƙewa ta yi ta fice daga ɗakin ba tare data ƙara cewa dasu komai ba.
Har bacci ya fara ɗauka ta a gurin da nake kwance sai dai jin kamar numfashin mutum yana fita da ƙarfi da ƙarfi ya sanya ni miƙewa da sauri ina rarraba idanuwana a cikin ɗakin.
A kansa na sauke idanuwana wanda shi lokacin nasa idanuwan a rufe suke sai faman sauke ajiyar zuciya yake yi.
Namiƙe kenan saiga Hajiya Inna ta shigo , cin karo da abinda ke faruwa ya sanyata nufar gurinda ƴar ƙaramar freezer take a jiye a cikin ɗakin ta ɗauko ruwan swan ta ɓalle murfin ta miƙa masu.
Ƙarɓa ya yi ba tare daya ce komai ba ya kafa kai sai da ya tadda fiye da rabinta sannan ya ajiye gorar yana me kwanciya a kan kujera.
Kusa dashi Hajiya Inna ta ƙarasa sannan ta ɗaga kansa ta ɗaura a kan cinyarta ta fara shafa masa sumar kansa.
Magana ta fara yi masa ƙasa ƙasa "me yasa ka dinga gayawa iyayenka duk maganar data fito daga cikin bakin ka?", "Iyayenka ne hwa waƴanda kaf duniyarnan baka da kamar su".
A hankali ya fara magana "Hajiya Inna baki san zalunci waƴannan mutanen ba ne, fuska biyu ne dasu, da zan gaya maki abinda suka yimin dake kanki na tabbata ba zaki ƙara kallonsu da idanuwan ki ba, amman na barwa rana ɗaya wannan , akwai ranar dazan fyeɗe su su dukansu, idan abinda na yi maki ya ɓata maki rai kiyi haƙuri dan Allah."
Ganin nayi Hajiya Inna na faman share hawaye sai kuma can ta ce "Allah ka jiƙqn bawanka Aminu , Allah ka bayyana min ɗana Aliyu ko hankalina zai kwanta , Allah ka dubeni da idanuwan rahma ya Allah."
Shine ya ci gaba da sharce mata hawayen fuskan tata kan ya ce "ki kwantar da hankalinki Hajiya Inna insha Allahu Baba Aliyu yana gabb da bayyana, ƴan kwana kinnan saina dinga ji a jikina kamar ina kusa da wani muhimmin abu a tare dani, na kanji kamar Babana ne nake tare dashi".
"Nima haka nake ji , ji na keyi kamar ina tare da Aliyu nane ƴan kwana kinnan."
Saurin sulalewa na yi na fice daga ɗakin iname tunanin maganganun su Hajiya Inna cike da al'ajabi.
Kitchin na nufa muka ɗaura abincin rana muna saukewa muka ɗaura na dare.
Yau kam da wuri nake son na koma gida domin nasan gobe ranar aiki ce, da dungu dungun safiya zan fito.
5pm muka kammala abinda muke yi na harhaɗa kayanta nayi sallama da mutanen gidan sannan na nufi sashen Hajiya Inna nayi mata sallama.
Kamar yadda ta yi hidima dani jiya haka ma yau sai da ta shaƙeman kula da alale sannan ta bani ₦500 ta ce na yi haƙuri dasu.
Godiya nayi mata sannan na kama hanyar gidanmu ina tafe ina tunanin halinda muke ciki dani da iyayena da ƴan ƙannan mu.
*ASALIN LABARINA......*
Sunana khadeejah Aliyu mahaifiyata Aminatu haifaffiyar ƴar garin Sokoto ce a ƙauyen ƙiri mahaifinta malamin gaske ne wanda a gurinsa mahaifina ya yi ɗaukar karatu tun yana ɗan shekaru ashirin a duniya har yau , bamu da labarin dangin mahaifinmu gaba ɗaya da dangin mahaifiyarmu muke tinƙaho sune na uwa sune na uba.
Mahaifina ba wani me kuɗi bane hasalima bashi da komai sai dai rufin asirin Allah.
Bayan aurensu da mahaifiyata ƴan abinda ya samu ya shigo cikin birnin Sokoto ya siyi dan madai dai cin gida me daki biyu da kitchin da banɗaki a ciki ne muke rayuwarmu.
Mukanyi kwana biyu ko fiye bamu ɗaura girki ba a gidanmu hakan ya sanya min sha'awar nemawa kaina aiki kona goge gogene .
Gashi inada burin naga ƴan ƙannena sunyi karatu sosai sai dai rashi ya sanya burin nawa ya saduda, to idan ma ba *RAI DA BURI* ba waƴanda ke neman na sawa ciki ina batun wani burin karatu.
To a haka dai muke tamna ƙulla har Allah ya nufi na samu aiki a gidan margayi AS Wurno , wannan aikin ba ƙaramin taimaka mana yake yi ba, kullum dashi muke ci muke sutura bugu da kari kuma nayi lalurar karatun ƴan ƙannena.
Za mana a gidan babban rufin asirin mune duk da idan rashin mutuncin ƴan gidan idan ya tashi baka jin sanyi a gurin kowa, wannan duk baya damuna matuƙar duk wata zanji lumus a hannuna.
Wannan tafiyar da mahaifinmu ya yi zuwa ƙiri muna sa ran ta kasance alkheree a garemu domin kuwa Mama ce taga abin yaƙi ci yaƙi cinyewa take ce masa mezai hana yaje wa Malam Hassan yaga ko zai amince a sayar da gonorta da ta yi gado a gun mahaifiyarta, a haka ya shirya yaje, tau muna dai addu'ar Allah yasa a dace.
*Wannan kenan!.*
Yauma kamar kullum bayan mun kammala komai da yazamo mana al'ada da daddare , naje kwanciya sai dai me? Haka na dinga juyi bacci yaƙi daukata da zaran na rufe idanuwana Shalelen Hajiya Inna nake gani lokacin da yake kwankwaɗar ruwa.
Lokaci ɗaya tausayinsa dana Hajiya Inna ya ɗarsarmin a cikin zuciya, zuciyata cike take da sonjin cikakken abinda ke faruwa sai dai ta yay .
Haka naci gaba da waswasina da tunane tunane na mafi yawa duk a kan Shalelen Hajiya Inna ne, bansan lokacin da ɓarawo ya sace ni ba......
Gobe zamu ci gaba.......
ƳAR MUTAN BUBARE CE!
Maryamah