Zulum Ya Fitar da Miliyan 476 Ba Da Tallafin Karatu Ga Ɗalibbai 15,374

Gwamna Zulum ya ci gaba da cewar, abubuwa da dama kan abin da ya shafi yadda ake bi don neman ilimi gwamnatin tasa tallafin ta ciki yadda abubuwa kan zo da sauki matuka. Shima shugaban kungiyar daliban Jihar Sugun Abba yayi godiya ga gwamna Zulum bisa ga wannan tallafi da ya bayar ga mambobin su wadda a cewarsa wannan abin a yaba ne matukar gaske.

Zulum Ya Fitar da Miliyan 476 Ba Da Tallafin Karatu Ga Ɗalibbai 15,374
Zulum Ya Fitar da Miliyan 476 Ba Da Tallafin Karatu Ga Ɗalibbai 15,374
Gwamnan Jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ya amince da ware zunzurutun kudi kimanin Naira Miliyan 476.64 don bada tallafin karatu  (scholarships) ga wasu daliban Jihar kimanin 15, 374 dake karatu a manyan makarantun karo ilimi a bangarori da dama cikin Nijeriya.
Farfesa  Zulum ya ce zai taimakawa sha'anin karatu gaya wajen ba da dama ga matasa da kokarinsu na neman ilimin zamani wadda hakan zai rage irin illolin Boko Haram a Jihar musamman wajen yaudarar matasa don shiga cikin su sakamakon zaman banza da karancin ilimin zamantakewar yau da kullum.
Gwamna Zulum ya ci gaba da cewar, abubuwa da dama kan abin da ya shafi yadda ake bi don neman ilimi gwamnatin tasa tallafin ta ciki yadda abubuwa kan zo da sauki matuka.
Shima shugaban kungiyar daliban Jihar Sugun Abba yayi godiya ga gwamna Zulum bisa ga wannan tallafi da ya bayar ga mambobin su wadda a cewarsa wannan abin a yaba ne matukar gaske.
A cewar sa lalle sun shaida cewa, mai girma gwamna ya kudiri niyar farfado da harkokin ilimi a jihar ta Borno.