Gwamnan jihar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal a wata hira da gidan rediyon Amerika sashen Hausa(VOA) ya yi da shi ya rika ambaton kalmar hijira a wurin da yakamata ya ambaci Miladiyya kusan sau bakwai.
Tambuwal a hirar da aka yi da shi domin karin haske ga takarar shugaban kasa da ya fito yake son zai yi a 2023, wurin fadin cancantarsa ne a yukkansa na baya ya bijiro da wannan sauyin da ba a taba jinsa ba, a tsarin kalandar musulunci da miladiyya.
Kalandar musulnci ita ce ke dauke da Hijira a yanzu tana shekara 1443 a yayin da Girogoriya take dauke da miladiya a yanzu tana 2022.
Tambuwal a sauyin da ya furta cikin kalamansa ya ce "tun a hijira 2003 ina majalisar tarayya, aka zabe ni karo na biyu hijira 2007, aka zabe ni karo na uku hijira 2011.
"hijira ta 2007 na zama mataimakin mai tsawatarwa a majalisa hijira 2011, na rike mukamin da shi ne babban mukami wanda shi ne yafi kowane matsayi a majalisar tarayya, na zama gwamna a hijira ta 2015 na sake zama gwamna a hijira ta 2019," a cewarsa.