Abin da Gwamnan Sakkwato ya fadawa jami'an Hisabah 130 bayan kaddamar da hukumar

Abin da Gwamnan Sakkwato ya fadawa jami'an Hisabah 130 bayan kaddamar da hukumar

 

Gwamnatin Sakkwato ta sake farfadowa da hukumar Hisbah a jihar in da ta dauki jami'ai 130, maza 118 da mata 12 don gudanar da aikin a hukumar.

Gwamnati ta bayar da mota biyar da babura 20 don saukaka aiki ga hukumar a lungu da sakon birnin jiha a burin da ake da shi na tsaftace jihar ga aiyukkan badala da sabo.
Gwamnan Sakkwato Dakta Ahmad Aliyu a bayaninsa wurin kaddamar hukumar ya bayyana yadda yake burin hukumar ta zama don kwalliya ta biya kudin sabulu.
 
"Na kaddamar da hukumar Hisbah da muka kara dawo da ita jihar Sakkwato, da nufin magance matsalolin
 rashin da'a da suka addabi jihar.
 
"Na bukaci sabuwar hukumar Hisban da ta tuna cewa cin zarafin mutane da ba su ji  ba su gani ba, baya cikin dalilan da suka sa aka kafa ta. Na kuma umarci  jami'an hukumar da su yi aiki bisa doron dokar da ta kafa hukumar, su kuma tabbatar da cewa aiyukan su ba su ci karo da kundin tsarin mulkin kasa ba.
 
"Kafa Hukumar Hisbah ba shi da manufar maye gurbin hukumomin tsaro da ake da su, sai dai za su tallafi harkar tsaro ne domin kare lafiya da dukiyoyin al'umar jihar.
 
"Jami'an hukumar za su yi aiki ne bisa doka, wacce ta ba su damar yin kame, daga bisani su kuma mika wanda ake zargi ga jami'an 'yan sanda domin gurfanar da shi a gaban kotun shari'ar musulunci," kalaman Gwamnan Sakkwato.
 
Ahmad Aliyu ya kara da cewa za su cigaba da bibiyar aiyukan hukumar domin tabbatar da cewa sun bi shimfidaddun dokoki da ka'idoji wajen gudanar da aiyukan su.
 
"Domin tallafawa hukumar wajen gudanar da aiyukan ta, mun samar mata da motoci da babura da kuma wadataccen ofis. Karin akan wannan kuma, nan ba da dadewa ba, za mu bude ofisoshin hukumar Hisbah na kananan hukumomi 23 na jiha.
 
"A nan ne, nake kira ga al'umar jihar Sokoto da su ba hukumar da jami'an ta hadin kai wajen sauke nauyin da ya rataya akan su."