Shugabar Mata ta ƙungiyar DYFAT tayi Allah Wadai da yima 'yan gudun hijira ciki a Katsina

Shugabar Mata ta ƙungiyar DYFAT tayi Allah Wadai da yima 'yan gudun hijira ciki a Katsina

Hajiya Halima Mas'ud, shugabar mata ta kungiyar Dikko Young Foundation (DYFAT), ta yi Allah Wadai tare da nuna takaici akan yanda maza sukayi lalala da wasu mata a Katsina. 

Katsina Post ta samu cewa ƙungiyar DYFAT ce ta ceto matan daga hannun ɓata garin maza kuma ta damƙa su a hannun hukuma a nan cikin birnin Katsina. 

Da take jawabi akan lamarin, Hajiya Halima Mas'ud ta nuna takaici ganin cewa wasu daga cikin matan yan gudun hijira ne. 

Hajiya Halima ta ci gaba da cewa, “Abin takaici ne jin wannan lamari mai tayar da hankali, musamman ga kananan yara wasu kuma yan gudun hijira.

Tace kungiyar DYFAT ba za iya jure wa irin wannan ta’asar ba a cikin al’umma, sannan tace dole ne a tabbatar da tsaro ga ‘ya’yanmu mata, kuma dole ne a hukunta wadanda ke aikata irin wadannan laifuka". 

Sannan Hajiya Halima ta gode ma shugaban Gidauniyar Gwagware Foundation, Alhaji Yusuf Ali Musawa bisa gudummuwar da yake basu da rawar da ya taka yayin da aka ceto matan. 

Tace Alhaji Yusuf Ali Musawa ya chanchanchi yabo ta yanda yake kula da al'amarin ƙungiyar su ta DYFAT babu dare babu rana.