Tinubu Ya Amince da Yi Wa Ma'aikata Karin Albashi

Tinubu Ya Amince da Yi Wa Ma'aikata Karin Albashi

 

Gwamnatin Tarayya ta sanar da yin ƙarin albashi ga ma’aikatanta da kaso 25% zuwa kaso 35%. Ma’aikatan da gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Tinubu ta yi wa ƙarin albashi sun haɗa da masu karɓar albashi na bai-ɗaya na CONPSS, CONRAISS, CONPOSS, CONPASS, CONICCS da CONAFSS.

Jaridar NTA ta ce hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labarai na hukumar kula da albashi ta ƙasa, Emmanuel Njoku, ya fitar a ranar Talata, 30 ga watan Janairun 2024. 
Hakazalika gwamnatin tarayya ta yi ƙarin albashi ga ƴan fansho da kaso 20% zuwa kaso 28% a kan albashinsu na yanzu.
 Emmanuel Njoku ya bayyana cewa ƙarin albashin zai fara aiki ne daga ranar, 1 ga watan Janairun 2024. A kwanakin baya ne dai gwamnatin tarayya ta yi ƙarin albashi ga ma'aikatan makarantun gaba da sakandare da ɓangaren lafiya. 
Wannan ƙarin albashin dai na zuwa ne ana a yayin da ake shirin bikin ranar ma'aikata ta duniya a ranar Laraba, 1 ga watan Mayun 2024.
Gwamnatin tarayya ta sha samun kiraye-kiraye daga ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC) a kan ta yi wa ma'aikata ƙarin albashi saboda tsadar rayuwar da ake fama da ita, sakamakon cire tallafin man fetur.