Sanya Sunan Sarkin Yakin Kontagora A Sakamakon Zaben Fidda Gwani Cin Mutunci Ne- Inji Alkalamin Sarkin Yaki

Sanya Sunan Sarkin Yakin Kontagora A Sakamakon Zaben Fidda Gwani Cin Mutunci Ne- Inji Alkalamin Sarkin Yaki

Daga Awwal Umar Kontagora, Minna

Sakamakon bayyana sunan Hon. Shehu Sale Slow dan majalisar wakilai mai wakiltar Rijau da Magama da shugaban karamar hukumar Rijau, Hon. Bello Bako ( Mayanan mai Sudan) da uwar jam'iyyar APC ta kasa tayi ya janyo wasu bata garin yan siyasa na yunkurin tada zaune tsaye a yankin ta hanyar baiwa kafafen yada labarai labarai marasa inganci.

Tsagin APC na karamar hukumar Rijau da Magama, na cewar Dr. Mahmud Shafini ne ya samu nasarar zaben fidda gwani a jam'iyyar, yayin jam'iyyar ta mika sunan Hon. Shehu Sale Slow a matsayin dan takarar majalisar wakilai, da Hon. Bello Bako a matsayin dan majalisar jiha, mai makon Tsalha Uba.
Bincike ya tabbatar da cewar babu wani hatsaniya ko rigima a yankin kan zaben fidda gwanin da ya gabata, balle zargin cewar wani yayi anfani da matsayinsa dan canja sakamakon zaben.
Alhaji Mu'azu Bawa, Sarkin yakin sarkin Sudan, wanda shi ne zababben mataimakin shugaban jam'iyyar a yankin arewa ta tsakiya, cikakken dan siyasa ne da ya taka rawa a harkokin siyasar jihar tun daga 2003 har zuwa yanzu.
Abdumajid Mas'ud, Alkalamin sarkin yaki, ya bayyana cewar masu anfani da sunan sarkin yaki dan yarfe da batanci daman ba ma su son zaman lafiya ba ne.
Alkamin ya kara da cewar, mu a kasar Rijau da Magana a bangaren siyasa a jam'iyyar APC muna zaune lafiya, abin mamaki ne wasu su rika baiwa kafofin yada labarai rahotannin da ba gaskiya ba suna yadawa ba tare da yin bincike ba.
Idan an ce an gudanar da zaben fidda gwani a karamar hukumar Rijau da Magana, me ye ingancin shi, sannan dole sai an yi batanci ga mutane masu daraja sannan za a samu biyar bukatar siyasa, ya kamata wadanda ake anfani da su wajen yunkurin tada hargitsi a kasar Rijau da Magama su sani hukumomin tsaro na kallon su.
Dan haka ina kara jawo hankalin yayan jam'iyyar APC a kasar Rijau da Magama, da mu hada kai, mu fuskanci babban zaben da ke gaban mu, batanci ko yiwa zaman lafiya zagon kasa ba zai kai mu gaci ba. Sarkin yakin mai Sudan, Alhaji Mu'azu Bawa mutum ne mai kishin jam'iyya, mutum ne mai kishin kasar Rijau da Magama, duk wanda uwar jam'iyya ta kai sunansa ga hukumar zabe shi ya samu nasara kuma ya cancanci wakiltar jam'iyya a babban zabe mai zuwa.