'Yan Majalisar Tarayyar Nijeriya Da Gwamnoni Sun Sanya ƙafar Wando Guda Kan Dokar Zaɓen Ƙato  Bayan Ƙato

Abdullahi ya ce da zaran shugaban kasa ya sanya masa hannu zai canja yanda ake gudanar da zabe a jihohi da tarayyar Nijeriya. An sa kafar wando daya tsakanin gwamnoni da 'yan majalisar tarayya kan dokar zaben kato bayan kato Sanata Adamu Aleru tsohon gwamnan Kebbi ya ce an yi dokar ne domin cigaban dimukuradiyyar kasa, an yi haka ne da kyakkyawar niyya. Gwamnan Kogi Yahaya Bello ya ce gwamnonin suna ganin yakamata a kawo wata mafita wadda tafi wannan dokar ta kato bayan kato.

'Yan Majalisar Tarayyar Nijeriya Da Gwamnoni Sun Sanya ƙafar Wando Guda Kan Dokar Zaɓen Ƙato  Bayan Ƙato

Majalisar tarayyar Nijeriya ta duba tare da amincewa da gyare-gyaren dokokin zaɓe bayan kwamitin da aka naɗa ya kammala aikinsa.
Dokar ta baiwa hukumar zabe damar fitowa da yanda take son hada sakamakon zabe, haka an amince da yin zaben kato bayan kato a dukkan kujerun da a a yi zabe a kowane mataki.
Majalisar dattawa da wakillai sun aminta da kudirin ya zama doka tun watan Juli a zamansu daban-daban amma sun amince a kafa wani kwamiti da zai duba in da gibi yake don gyarawa, yanzu an tabbatar da gyaran na kwamiti karkashin jagorancin Yahaya Abdullahi da matallafinsa Akeem Adeyemi.
Abdullahi ya ce da zaran shugaban kasa ya sanya masa hannu zai canja yanda ake gudanar da zabe a jihohi da tarayyar Nijeriya.
An sa kafar wando daya tsakanin gwamnoni da 'yan majalisar tarayya kan dokar zaben kato bayan kato Sanata Adamu Aleru tsohon gwamnan Kebbi ya ce an yi dokar ne domin cigaban dimukuradiyyar kasa, an yi haka ne da kyakkyawar niyya.
Gwamnan Kogi Yahaya Bello ya ce gwamnonin suna ganin yakamata a kawo wata mafita wadda tafi wannan dokar ta kato bayan kato.
Gwamnonin PDP suna ganin bai kamata wata jam'iya ta yi wa wata kaudi da shigar shigula kan yadda za ta yi zabenta.