Matashi Mai Sana'ar Daukar Hoto Ya Zama Kwamishina A Jihar Kebbi

Matashi Mai Sana'ar Daukar Hoto Ya Zama Kwamishina A Jihar Kebbi

Daga Abbakar Aleeyu Anache.

Gwamanatin Jihar Kebbi karkashin jagorancin Dr Nasir Idris Kauran Gwandu ta rantsar da Ibrahim Muhammad Photos Diri a matsayin kwamishina.

Gwamnan kebbi Dr Nasir Idris Kauran Gwandu ya nada Ibrahim Photos Diri mai sana'ar Hoto a matsayin kwamishinan Digital Economy.

Ibrahim Photos Diri mai sana'ar Hoto dai dan asalin karamar hukumar Sakaba ne ya samu kwarewa da jajirccewa wajen sana'arsa ta daukar Hoto.

Ana sa ran Kwamishinan ya yi amfani da basirarsa wajen bunkasa harkar digital a jihar Kebbi.