Tambuwal Ya Naɗa Shugaban Hisbah A Sakkwato Gwamnan jihar Sakkwato Aminu WaziriT

Tambuwal Ya Naɗa Shugaban Hisbah A Sakkwato Gwamnan jihar Sakkwato Aminu WaziriT
Tambuwal Ya Naɗa Shugaban Hisbah A Sakkwato
Gwamnan jihar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal  ya naɗa shugaban hukumar Hisbah ta jihar Sakkwato.
A takaradar da Sakataren gwamnatin jiha Malam Sa'idu Umar ya sanyawa hannu ya ce gwamnan ya aminta da naɗa muƙamai kamar haka: Grand Khadi Muhammad Tambari Yabo mai ritaya a matsayin shugaban Hisbah na jiha, sai Dakta Umar Muhammad Boyi babban darakta hukumar Hisbah ta jiha.
Haka ma ya naɗa  Malam Yahayya Muhammad Boyi (Sarkin Mallaman Sokoto) shugaban hukumar ilmin Larabci da addinin musulunci ta jiha.
Naɗin zai soma aiki nan takeba da ɓata lokaci ba.