Mahara Sun Kashe 'Yan Sanda Bakwai A Zamfara

Mahara Sun Kashe 'Yan Sanda Bakwai A Zamfara

Mahara Sun Kashe 'Yan Sanda Bakwai A Zamfara

Daga: Mansur sani Dankure 

Wadanda ake kyautata zaton yan bindiga ne sun kashe a kalla yan sanda bakwai a wani harin kwanton bauna a kusa da kauyen Zonai a gundumar Magami a yankin Gusau Local Government Zamfara State. 

Mazauna yankin sunce yan sandan yayin da suke kan hanyar su ta dawowa daga aiki cikin ayarinsu a ranar Litinin,  a dai dai check point kusa da kauyen Zonai akan titin Gusau-Magami-Dansadau yayin da gungun yan ta'addan suka budema ayarin motocin yan sandan wuta. 

Mazaunan garin sunce abun bakin cikine garemu musamman mu yan garin Magami saboda yan sandan suna matukar taimako wajan magance mummunan rashin tsaron da ake fama dashi. 

A takaice kasancewar su a hanyar yana ba matafiya karfin gwiwar bi ta hanyar. Matafiya da yawa aka kashe wasu kuma akayi garkuwa dasu a wannan hanyar mai tsawon kilo mita 50, hakika wannan abun bakin cikine kamar yadda mazaunin ya bayyana mai suna Halliru. 

Mai magana da yawun rundunar yan sanda ta jahar zamfara SP Muhammad Shehu har zuwa hada wannan rahoton ba'asamu dama jin ta bakinshi ba. 

Duk da haka mun samu damar zantawa da jami'in hulda da jama'a na Asibitin kwararru na Yariman Bakura, Auwal Usman Ruwan Dorawa yace yan sandan da aka kashe an kawosu Asibitin ne a ranar Talata da misalin karfe 8:00 na safe.