Mijin mai juna biyu yakamata da Kwartonta a Otal

Mijin mai juna biyu yakamata da Kwartonta a Otal
Mijin mai juna biyu yakamata da Kwartonta a Otal

Daga Aliyu Adamu Tsiga
Wata matar aure dake ɗauke da juna biyu dubunta ta cika yayinda mijinta ya kamata da kwartonta da suke mu'amala a Otal.
Rahotanni sun bayyana cewa, mijin da ke zargin matar tasa da aikata alfasha ya kama ta dumu-dumu  a tare da wani mutum Otal suna tsaka da more junansu.

Majiyoyi sun bayyana cewa matar, mai ɗauke  da cikin 'yan watanni, ta daɗe  tana yin tarayya irin ta  aure a tare da shi farkan nata.
An bayar da rahoton cewa mijin yana jin jita -jitar sharholiyar da matar ta shi ke yi ​​kuma ya yanke shawarar daukar irin wannan matakin da yakai da kama matarsa hannu da hannu a wurin da aka sanar da shi matarsa na zuwa yin sharholiya.
Mijin, a wannan lokacin, ya sami kira daga mai ba shi labari. Daga nan sai ya kutsa kai cikin dakin ya kama matarsa ​​mai ciki a cikin aikata abinda bai kamata ba da wani.

Kamar yadda Zuma times Hausa ta kawo mijin ne ya riƙa tura hotunan cin amanar da matarsa ta yi masa a kafofin sada zumunta na zamani.
Majiyar ba ta faɗi gari da sunayen waɗanda lamarin ya faru da su ba, sai dai sun buga hotunan matar da farkanta a saman gadon da suke zaune a Otal.