'Yan Bindiga Sun Kashe Wani Basarake Mai Ƙima a Jihar Zamfara

'Yan Bindiga Sun Kashe Wani Basarake Mai Ƙima a Jihar Zamfara

 

'Yan bindigan daji sun kashe hakimin Yankuzo, Alhaji Hamza Abdullahi Kogo, na masarautar Tsafe a jihar Zamfara. 

Channels tv ta rahoto cewa 'yan ta'addan sun farmaki Basaraken ne yayin da yake kan hanyar komawa yankinsa daga wani taro da ya halarta ranar Jumu'a da misalin karfe 8:00 na dare.
Wata majiya daga yankin ta bayyana cewa maharan sun harbi Basaraken kuma ya samu raunuka sosai lokacin da suka yi yunƙurin garkuwa da shi. 
Daga nan aka garzaya da shi babbar Cibiyar lafiya ta tarayya dake Gusau, babban birnin jihar daga baya Allah ya masa cikawa ranar Asabar da daddare.
Garin Yankuzo nan ne mahaifar hatsabibin ɗan ta'addan nan, Ado Aleiru, wanda Masarautar Yandoton Daji ta naɗa masa rawanin Sarauta a watan Yulin wannan shekara da muke ciki. 
Da yawan mazauna garin Yankuzo sun bayyana cewa garinsu bai taɓa fuskantar harin 'yan bindiga ba tun da aka fara fama da matsalar 'yan fashin jeji a jihar Zamfara, arewa maso yammacin Najeriya. 
Har zuwa yanzun da muka kawo muku wannan rahoton, hukumomin tsaro a jihar ba su ce komai game da kisan babban basaraken ba, Lindaikejiblog ta rahoto. 
A watannin da suka shige mataimakin gwamnan Zamfara, Sanata Hassan Nasiha, yace shirin tattaunawar lafiya da 'yan ta'adda ta fara haifar da ɗa mai ido a kokarin dawo da zaman aminci a jihar.