Amfanin Ganin Likitan Fisiyo Kai Tsaye

Bincike da dama sun nuna cewa ganin likitan fisiyo kai tsaye domin ciwon jiki da gaɓɓai na iya rage wa likitan ƙashi da sauran likitoci aiki da kaso mai tsoka.
Ganin likitan fisiyo kai tsaye na nufin zuwa sashin fisiyo kai tsaye ba tare da zuwa sashin likitan tiyatar ƙashi ko likitan bai-ɗaya da farko ba, musamman domin ƙorafin ciwon jiki da gaɓɓai kamar ciwon wuya, ciwon baya, ciwon gwiwa da sauransu.
Ganin likitan fisiyo kai tsaye na da alfanu kamar haka:
1. Rage kashe kuɗaɗe akai-akai domin sayen magungunan ciwon jiki da gaɓɓai.
2. Rage tsawaitar zuwa ganin likita.
3. Kauce wa illolin shan magungunan rage ciwo, kamar ciwon ƙoda da kuma yanjo ko tayar da gyanbon ciki (olsa).
4. Ɗaƙile sababin ciwo tun da wuri. Likitan fisiyo na ganowa tare da magance ciwo daga tushe. Amma magungunan rage ciwo suna iya rage ciwo ne na wani lokaci kawai ba tare da magance sababin ciwon daga tushe ba.
5. Kauce wa tiyata / aiki: Ganin likitan fisiyo da wuri kafin fara shan magungunan rage ciwo na taimakawa daƙile sababin ciwo kafin ya ta'azzara har ya kai ga yin tiyata.
6. Kauce wa nakasa: Idan ciwo ya daɗe tsawon lokaci ba tare da an gano kuma an magance sababinsa ba, to zai iya nakasa sashi ko gaɓar.
Likitocin fisiyo ƙwararru ne da za ka iya gani kai tsaye domin matsalolin da suka shafi ciwon jiki da gaɓɓai, shanyewar hannu ko ƙafa, da duk matsalolin da ke nakasa gaɓoɓi da sassan jiki.