Sokoto: Abin Da Ya Sa Ba Za Mu Gudanar Da Zabe a Rumfuna 8 Ba---Kwamishinan Zabe

Sokoto: Abin Da Ya Sa Ba Za Mu Gudanar Da Zabe a Rumfuna 8 Ba---Kwamishinan Zabe

 

INEC Ta Fara Rabon Muhimman Kayan Aikin Zabe 

 
Shirye-shirye ya kankama sosai na zaben shugaban kasa da na majalisar tarayya da za a yi a ranar Asabar, 25 ga watan Fabrairu. 
Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta fara rabon kayan zabe masu muhimmanci zuwa ofishoshinta na kananan hukumomi.
Daukacin hukumomin tsaro da suka hada da na yan sanda, NSCDC, SSS, hukumar kula da shige da fice da sauransu suna sanya ido kan yadda ake rabon kayayyakin, zai gudana.
Kwamishinan hukumar zabe na jihar Sakkwato Dakta Nura Ali a tattaunawa da manema labarai ya ce sun raba kayan da suka fi muhimmanci a harkar zabe kamar yadda shugaban hukumar na kasa ya umarta domin ganin ranar Assabar an fara zabe da karfe Takwas na safe kamar yadda aka shardanta.
"Na'uarar mu ta BVAS muna da ita a kammale guda  dubu 3 da 999, lokacin da muka yi gwajinta mun samu biyar suna da matsala amma an gyara an karo mana wasu don jiran ko ta kwana, za mu raba su a gobe(Alhamis)".
"A Sakkwato muna da rumfar zabe 3,991, sai dai an soke rumfa 8 saboda ba wanda ya yi rijsta a wurin, ka ko ga ba za mu kai kayan zabe a wurin ba, tun da ba wanda ya nuna yana son yin zabe a wurin.
"Muna aiki da jami'an tsaro a Sakkwato dukkansu don tabbatar da tsaron dukkan rumfunan zabe, da ikon Allah zabe zai gudana cikin lumana," a cewar Dakta Nura Ali.
Ya ce a gaskiyar magana ba wasu kalubale da muke fuskanta, tun da CBN za su ba da kudi gare mu issasu ba wani abu.