Sokoto: Ma'aikatan gwamnati na bore a kan kin biyan su albashin watan Fabrairu da Maris

Sokoto: Ma'aikatan gwamnati na bore a kan kin biyan su albashin watan Fabrairu da Maris

Gamayyar kungiyoyin ma’aikatan jihar Sokoto a jiya Talata sun roki a biya su albashin su na watan Fabrairu da Maris.

Kungiyar, karkashin jagorancin Ibrahim Musa, ma’aikacin Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari, SSCOE, ta yi wannan kiran ne a wata ganawa da manema labarai a Sokoto.

Musa ya ce ma’aikatan jihar na bin bashin albashi har da na watannin baya da ba a biya ba.

A cewarsa, akwai bukatar a kwarmata batun bisa wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na jihar ya fitar, inda ya ce gwamnatin jihar ta biya daukkanin albashin ma’aikatan gwamnati na watan Fabrairu ta bankuna.

“Muna son sanar da jama’a cewa furucin da Kwamishinan ya yi na cewa gwamnatin jihar cewa ba ma bin ta badhin albashi, yaudara ce.

“Saboda kalaman rashin gaskiya ne ya sa muka zo nan ne domin mu hada kan mutanen Sakkwato don su sa mu a addu’a domin gwamnati ta samu ta biya mu hakkokinmu.

"Mun ji labarai da yawa game da albashinmu amma ga kwamishina bari faɗa wa al'umma gaskiya ba , kan wani muhimmin al'amari mai mahimmanci na ceton rai kamar Albashi, ba za mu lamunce ba," in ji shi.

Musa ya kuma yi kira ga Gwamna Aminu Tambuwal da ya ci gaba da rike mutuncin sa ta hanyar biyan dukkan ma’aikatan gwamnati albashin watan Fabrairu da Maris kamar yadda ya saba.