Ya nemi matarsa ta yi masa sabon aure kafin ya sake ta
Wata mata mai matsakaicin shekaru, Amina Aminu, a ranar Talata ta gurfanar da mijinta, Umar Muhammad a gaban Kotun Shari’ar Musulunci da ke zaune a Magajin Gari, Jihar Kaduna, tana neman a raba aurensu.
Amina wacce ke zaune a Kaduna ta nemi hakan ne bisa zargin cewa mijin nata yana shan sigari a dakinta kuma ba ya son ’yan uwanta, kamar yadda manema labarai suka kalato.
"Na tunkari wannan kotu ne ina neman saki saboda mijina ya ki canza halayensa, ba zan iya rayuwa tare da shi ba.
"Zan biya shi N50, 000 da ya biya a matsayin sadakina shekaru biyu da watanni biyar da suka gabata don fansar kaina daga auren.
"Na ba shi dama sau da yawa don ya canza amma ba zai taba yin hakan ba." a cewar matan a gaban Kotu.
Muhammad, da ake ƙara ɗan kasuwa ne da ke zaune a cikin garin na Kaduna, ta hannun lauyansa, Nazifi Shehu, ya buƙaci kotu da ta amsa bukatar mai karar na saki.
Shehu, ya roki kotu da ta umarci wacce ta shigar da karar da aura masa sabuwar mata.
Ya ce Wanda nake karewa yana son matarsa, Allah ya albarkace su da yarinya ‘yar wata tara, sun yi iya ƙoƙari don ganin ta dawo gidan mijinta amma duk da hakan ya ci tura.
"Ya kamata ta samo masa wata matar sannan ta ɗauki nauyin dukkan kuɗaɗen da za a kashe na aure", in ji lauyan.
Alkalin kotun Murtala Nasir, bayan ya saurari bangarorin, ya dage sauraron karar zuwa ranar 12 ga watan Agusta don yanke hukunci.
Ya umarci mai shigar da karar da ta nemi shawarar waliyinta kafin ya raba auren wanda a cewarsa shi ne kadai zabin da ya rage ga kotun.
Rana ce kawai za ta bayyana yanda za ta kaya a tsakanin ma'auratan, da suke da bambancin ra'ayi a zamantakearsu.