'Yan Bindiga Sun Jikkata  Jami'an Immagration 6 a Sakkwato

'Yan Bindiga Sun Jikkata  Jami'an Immagration 6 a Sakkwato

'Yan Bindiga sun Kai farmaki a shingen jami'an shige da fice(immigration) dake kauyen Mammansuka a karamar hukumar Gwadabawa jihar Sakkwato' in da suka harbi mutum shidda nan take biyu suka rasu aka tafi da sauran asibiti.
A cewar shedun gani da Ido Wanda yake direba ne ya ce Maharan sun zo saman babura da yawa a ranar Jumu'a bayan sallar Magariba kai tsaye suka farma jami'an da harbi bayan sun jikkata mutum shidda, biyu sun rasu  suka tafi da wasu ba tare da sanin dalilin hakan ba.
Mammansuka tana cikin manyan kasuwar sati-sati  da ake ci  wadda ke kan hanyar  Sakkwato zuwa Illela har kasar Nijar.
Majiyar ta ce ba a San dalilin da ya sa aka Kai harin ba ganin jami'an ba su takurawa mutanen gari sai dai Baki da ba su da izinin shiga Nijeriya.
Jami'in hulda da jama'a na hukumar a yankin Illela  Bello Muhammad ya tabbatar da faruwar lamarin sai dai a lokacin da aka kira shi yana asibiti ya ce zai kira daga baya.
Da wakilimu ya sake kiran shi bai samu wayarsa ba.
Matsalar tsaro ta sake dawowa a jihar Sakkwato in da kullum sai an kaiwa al'umma hari in da aka kashe wasu a sace wasu a jikkata wasu duk da kokarin da mahukunta ke fadin suna yi a harkar tsaron jiha.