Turji ya tilastawa ƙauyukka 20 barin gidajensu bayan kaddamar sabbin hare hare a Sakkwato
Daga Abbakar Aleeyu Anache.
Sabbin hare-haren ‘yan bindiga da aka ce wasu magoya bayan Bello Turji ne suka shirya, ya tilastawa mazauna kauyuka 20 barin gidajensu a jihar Sokoto.
Yanzu haka dai mutanen kauyen da suka rasa matsugunansu na samun mafaka a garin Gatawa dake karamar hukumar Sabon Birni.
Wani mazaunin garin, Malam Saminu, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata hira da aka yi da shi ta wayar tarho da jaridar Punch Newspapers inda ya bayyana cewa rikicin ya biyo bayan sake fuskantar barazana da cin zarafi daga daya daga cikin manyan yaran Bello Turji.
Kauyukan da harin ya shafa sun hada da Makira, Shabanza, Katsalle, Dan Kura, Garin Tunkiya, Dama, Dan Tazako I, II da III, Gaugai, da dai sauransu.
Wannan tashe-tashen hankulan da ake fama da shi ya sake nuna halin da ake ciki na rashin tsaro a yankin Gabashin Jihar Sakkwato, inda ake ci gaba da kai hare-hare duk da ayyukan da sojoji ke ci gaba da yi da nufin dakile ‘yan fashi da kuma dawo da zaman lafiya a yankin.
managarciya