'Yan Bindiga  Sun Tafka Babbar Ta'asa a Jihar Zamfara

'Yan Bindiga  Sun Tafka Babbar Ta'asa a Jihar Zamfara

Wasu ƴan bindiga sun yi garkuwa da wani darakta a ma’aikatar kuɗi ta jihar Zamfara, Malam Sabiu da matarsa ​​da ƴaƴansa biyu. 

Jaridar The Punch ta samu labarin cewa lamarin ya faru ne a daren ranar Talata, a rukunin gidaje na Damba da ke Gusau, babban birnin jihar. 
Wani mazaunin yankin mai suna Auwalu Garba, ya ce ƴan bindigan sun shiga gidan Sabiu da misalin ƙarfe 1:30 na daren ranar Talata. 
A cewarsa, ƴan bindigan waɗanda ke ɗauke da manyan makamai, sun je gidan Sabiu ne kai tsaye da isar su unguwar, wanda hakan ya nuna kamar umarni aka ba su. A kalamansa: "Lokacin da suka isa unguwarmu, ba su yi harbi ba, ba su kuma shiga gida ba. Kai tsaye gidan Sabiu suka nufa inda suka fasa ƙofar, suka shiga ɗakin barcinsa suka sace shi da matarsa. 
"Daga baya suka koma wani ɗaki suka yi awon gaba da yara biyu sannan suka koma daji." 
Garba ya ce daga baya ƴan bindiga sun sako matar Sabiu bisa dalilan rashin lafiya. Ƙoƙarin jin ta bakin kakakin rundunar ƴan sandan jihar, Yazid Abubakar, ya ci tura, domin an kasa samunsa ta layin wayarsa.