DUHU DA HASKE: Fita Ta 27
DUHU DA HASKE
Na
*Jiddah S mapi*
*Chapter 27*
~Da mugun gudu take driving akan titin, hanan ta rufe ido ganin kamar zasu kife, yazeed yana kallonta a tsorace yadda take gudu, a hankali ya ɗaura hanunshi kan waist nata ya riketa gam ganin zata kifar dasu akan titin, a gefen hanya tayi parking kawai ta juyo ta zubawa yazeed ido, cikin sanyinshi yake kallonta, bai taɓa ganinta cikin irin wannan halin ba, buɗe baki yayi zaiyi magana tayi saurin haɗa bakinta da nashi, cikin wani irin yanayi me wuyan fassara take shan bakinshi kamar zata cinyeshi tana hawaye masu zafi, hanan dake bayan motan tana kallonsu a hankali tasa hanu a marfin motan ta buɗe ta fita, taxi ta tara ta tafi gida, yazeed da kyar ya kwace kanshi tana kokarin karayi yace "stop it meesha, ki danne zuciyarki kinji?"
cikin kuka tace "ba zan iya ba"
kankameshi tayi tana kuka tana jinshi yana shafa bayanta alaman tayi shiru, hanan har kofa aka ajeta ta shiga gida a hankali take tafiya kamar mara lafiya, momy ce a falo tana kallo tana ganinta haka ta tashi da sauri tace "hanan ina sauran ƴan uwanki? meya faru kika dawo ke kaɗai ina suke?"
a hankali tace "suna hanya"
zata kara wata tambayar kawai ta wuce, binta tayi da ido sannan ta kalli kofa.
yazeed da kyar ya samu ya lallashi ameesha sai ajiyan zuciyan kuka take saukewa, saukar da ita yayi daga jikinshi ya zaunar da ita a kan kujera yaja motan hanunshi cikin nata yana matsawa a hankali yana driving, da haka har suka isa gida, momy tana ganin sun shigo tace "ameesha meya sameki kikayi kuka?"
shiru tayi, a hankali ta raɓa gefen momy ta wuce sama, bataga fuskan tambaya bama a wajen yazeed shima ya tafi, kallon kofa tayi bataga su Imran ba, a hankali ta koma ta zauna tayi tagumi ta kashe tv.
Abdool cikin kuka yace "ku yafemin dan Allah ku yafemin"
suna kuka suma sun kasa sakinshi, cikin kuka ya fara faɗa musu duk abinda ya faru da abinda yasa yace tanada taɓin hankali a kotu, kankameshi Imran yayi yace "na san ba zaka taɓa tafiya ka barmu haka kawai ba, na sani yaya"
kuka sukeyi sosai, a hankali ya zame yana share hawaye yace "muje na maidaku gida"
girgiza kai fahad yayi yace "babu inda zan koma ina tare da kai"
Imran yace "nima ina tare da kai"
yace "amma meesha..."
Imran yace "anty ameesha tana cikin fushi ne amma kafi kowa sanin tanada sauƙin kai, zata sauko itama ta dawo muci gaba da zama tare"
jikinshi a sanyaye
baba yace "wannan da take tare dashi fa?"
ba shi kaɗai ba har fahad da Imran saida gabansu ya faɗi, tabbas ameesha ta samu wani wanda ta bashi yadda fiye da yadda ta bawa man, gashi sunfi kowa sanin yadda suka shaƙu, baba yace "ba komai kuzo muje ciki insha Allah komai zaiyi daidai"
shiru sukayi su duka suka shiga ciki, ammi sai murmushi take musu.
Ameesha tana shiga ɗaki ta faɗa kan gado ta janyo blanket ta toshe bakinta da fuskanta ta fara kuka, hanan tana kallonta ta kasa lallashinta, yazeed yana shiga ɗaki ya fara kallon kanshi a madubi, a hankali ya shafa lips nashi na kasa wanda tafi sucking sannan ya lumshe ido, a hankali ya buɗe yayi murmushi me sanyi, koda yake tare da rohi a kullum sai sunyi haka amma bai taɓa jin yadda yake ji a yanzu ba.
zaune take akan kujera tana juyawa gabanta desk ne da system akai, sanye take da riga me haɗe da wando tayi kyau sosai domin dark navy blue ne kayan, gashinta tayi parking nashi ta kame da ribbon na kayan me kyau, babu hula akanta, gefenta glass cup ne da pure apple drink a ciki, kafa ɗaya ta ɗaura akan ɗaya idonta sanye da babban baƙin glass, murmushi ne kwance akan fuskanta tana kallon system ɗin, tashi tayi daga zaunen da take ta ɗau glass cup ɗin ta fara taku da takalmi me tsinin dake kafarta, kurɓa tayi sannan ta maida cup ta zuba hannayenta akan desk ɗin tana daga tsaye tana kallo tace "my abdool kana ganin zaka tseremin ne?"
girgiza kai tayi tace "no ba zaka taɓa yin haka ba, kasan me yasa?"
murmushi me sauti tayi kana tace "sabida tunda kazo wajena kana nemana nasan akwai abinda ka shirya, shiyasa nayi connecting camera ɗin dana jima dasa maka a wannan zoben dake karamin yatsanka da system ɗina, kana nan kana shirya yadda zakayi nima ina shirya komai nawa, a wannan karon dole wasa na ya canja ta yadda zan mallaki Abdool ni kaɗai ba tareda kowa ba, gashi kai baka kallo na amma ni ina ganin duk wani mostinka, happy marriage life Ammi"
tafa hannu tayi tace "hakika baba megadi yaci amana, kuma ni manal ina hukunta maci amana koda kuwa shiya haifeni"
dariya tayi sosai sannan tace "zan bari ammi ki gama cin amarcinki da sabon mijinki kafinnan na hukuntashi tunda shine yake faɗawa ameesha komai, sannan Abdool ka sani lokaci kawai nake jira amma dole zaka dawo, idan ma baka dawo ba, zanyi amfani da maganata na karshe wato dana rasa gara kowa ya rasa"
waya ta ɗauka ta kira wani number tace "ku bata waya"
murmushi tayi sannan tace "sannu mama nasan sun azabtar dake dayawa kiyi hakuri ki yafemin soyayya ne yasa nayi hakan, inaso na baki wani zaɓi guda biyu na farko zasu sa miki wayar a voice note Inaso ki rinƙa kuka kina cewa Abdool dan Allah ka kyaleni ban san komai ba gameda mutuwan ummanka ka manta tare muka zauna da ita ne? ka manta irin soyayyan dake tsakanin family ɗinmu ne? dan Allah kada ka kasheni abdool, zaɓi na biyu shine idan bakiyi hakan ba zan kashe ɗaya a cikin waɗannan biyun ameesha ko fahad"
da sauri mama dake cikin azaba tace "dan Allah, dan Allah manal kada ki cutarmin da kowa a cikinsu harda Abdool ɗin na yadda zanyi"
tace "yawwa ko kefa, kada ki damu kinfi kowa sanin ba zan cutar da abdool ba sabida ina sonshi zan aje wannan ne sabida tsaro ba dan tsoro ba"
tace "kuyi recording yanzu ku turomin ta watsapp"
katse wayan tayi ta zauna tana cigaba da jujjuyawa akan kujeran tana kallon saman ɗakin, bata jima sosai ba suka turo mata voice, murmushi tayi jin komai ta faɗa kamar yadda tace "my abdool kai nawa ne har abada"
Ameesha har kwana uku bataga su Imran ba gaba ɗaya ta shiga damuwa duk da taso ta danne amma ta kasa, kullum saita leƙa ɗakinsu taga ko sun dawo amma shiru, Abba yace tayi hakuri zasu dawo, yauma tana zaune tayi tagumi ta raa meke mata daɗi, ga tv a buɗe amma bata kallon tv, momy ce ta zauna gefenta tace "ameesha inata magana baki jina"
a hankali tace "na'am"
momy tace "zama cikin damuwan ya isa haka mana ƴata kullum kina tagumi"
shiru tayi idonta yana cika da hawaye, gani tayi yazeed ya fito da trolley a hanu yana turawa cike da kayan su Imran, kallonshi tayi shima ya kalleta yace "tashi muje mu kai musu kayansu tunda sunki dawowa wajenki"
da gudu ta haye sama ta ɗauko hijabi, yayi murmushi yana binta da ido, yasan tana kewansu sosai shiyasa yayi mata wannan dabaran dan taje ta gansu, ta fito da hijabin me kyau maroon dogo tasa, tayi kyau sosai tace "muje"
tare suka fita momy tayi murmushi ganin dabaran da yayi, mota suka shiga yaga yadda take farin ciki, shago ta kalla tace "mu tsaya na siya musu chocolate?"
yace "okay"
ya tsaya ya bata kuɗi dayawa yace "siyo musu"
tana fita ya fara dariya, wanda ake fushi dasu kuma za'a siya musu chocolate? wani abu sai ameesha, bayan ta siyo ta dawo ta zauna, ya fara driving yace "ni ina nawa?"
ɗaya ta mika mishi an rubuta you are the best a jiki, tace "ga naka"
yace "ɓaremin"
ɓarewa tayi ta mika mishi, yace "to ai ina driving ko dai rohi zan kira tazo ta bani?"
wani irin takaici taji daya kira sunan rohi, kawai ta fara bashi yana ci yana dariyanta har suka isa gidansu, fitowa sukayi tare ya rike trolley ita kuma ta rike ledan, sallama sukayi sannan suka shiga, Imran da fahad da ammi suna falo suna kallo, da alama sun saba sosai yanzu domin da ganin yadda suke zaunen zaka gane, suna ganinta suka sunkuyar da kai kowa yaki yadda ya kalleta, a fusace taje wajen ammi tace "ammi na kawo miki chocolate sannan na kawo musu kayansu duka"
yazeed ya gaida ammi, tayi mishi alaman amsawa, ta kalli ameesha dake huci tana kallon su Imran cikin missing nasu da tayi, duk sunki su kalleta suka gaida ya yazeed ya amsa da sakin fuska, Abdool da yake sauri yana fitowa riga a hanu wayarshi a kafaɗa yana magana yace "gani nan baba yanzu zan fito yanzu.."
shiru yayi da suka haɗa ido da ameesha da sauri ta ɗauke kai ta tashi ta watsawa su Imran kayan tace "idan kunga dama ko a hanya karku kara yimin magana"
tace "muje ya yazeed"
fita sukayi sai kuma tace "mu koma na faɗa musu wani abu"
komawa sukayi tace "Imran kaine babba amma shine ko gaisheni ba zakayi ba?"
a hankali yace "ina wuni"
tace "kaika sani"
hararan fahad tayi sannan suka tafi ko kallon inda man yake batayi ba, da haka suka koma gida"
man cikin sanyin jiki yace "meyasa baku gaisheta ba?"
Imran yace "ni wallahi tsoro ma anty ameesha take bani yadda gaba ɗaya ta zama wani boss"
murmushi kawai yayi yace "Ammi mijinki ya dameni wai dole saina fara zanen gidaje yanzu haka ya tara mutane a wani gida wai zanje nayi zane yanzu idan naga dama ba sai na zauna naki zuwa ba?"
murmushi tayi mishi har hakoranta suka bayyana, fita yayi dan dama abinda yakeso yaga tanayi kenan a kullum.
kamar da wasa kullum sai ameesha ta ɗauki wani abin koda mara amfani tasa yazeed a gaba wai ya kaita zata kaiwa su Imran nasu ne, tunda yasan kewansu take kuma ba zata iya zama babu su ba baya musu a duk sanda tace ya kaita kaita yake idan ta gansu su dawo, duk da ba wani magana take musu ba sai ammi kawai takewa magana, suna haɗuwa da abdool amma bata ko kallonshi bale tasan yana wajen, yauma tana rike da manyan leda ta shigo yazeed yana waje yana waya, zama tayi akan kujera tayi hamma domin bacci ta fara ji tunda wuri haka, batama kula akwai mutane a wajen ba, Abdool yana zaune a kasa yana zanen gida, su Imran suna kallo domin su koya, ɗaga murya tayi tace "ammi"
baba ne ya fito yace "a,a ameesha yaushe kikazo?"
tace "yanzu baba ina ammin?"
yace "gata a nan idonki rufe ne kika shigo?"
buɗe ido tayi sai yanzu ta kula ashe duk suna falon, ɗauke kai tayi daga kallon Abdool sannan ta ɗau ledan ta aje a wajen ammi tace "gashi ammi bari yazeed ya shigo ku gaisa saimu tafi"
Imran yace "ina wuni anty ameesha"
ciki ciki tace "lafiya"
fahad saida ya ɓoye kanshi a bayan man sannan yace "ina wuni"
tace "lafiya"
yazeed ne ya shigo ya gaida kowa harda man sannan ya gaida baba kafin suka tashi zasu tafi baba yace "ameesha"
tace "na'am baba"
yace "baki gaida Abdool ba"
a hankali tace "ina wuni"
kafin ya amsa ta kama hanun yazeed sun fita, shiru yayi zanen yana nema ya gagareshi, Imran yana kallonshi ya tashi ya tafi ɗaki, shiru yayi ya kwanta yana tunani kala kala a ranshi, manal itace wacce ya fara jin asalin tsananta a ranshi, baba ne ya shigo ya biyoshi tunda yaga ya tashi, yace "abdool hakuri zakayi duk abinda kaga ya faru Allah ya riga ya rubuta karka damu ameesha dole zatayi fushi domin batasan dalilinka ba kuma taki yadda ta saurari kowa kayi hakuri ka kwantar da hankali me hakuri yana tare da Allah kaji?"
a hankali yace "to na gode"
yazeed ganin bataso ma ana ɗago mata maganan Abdool ɗin yasa baya mata magananshi koda sun fito daga gidan.
washe gari ameesha tana kwance a ɗaki tana bacci taji karan shigowan message, ko bacci take idan har kunnuwanta sun jiyo mata karan message tashi take ta duba dan may be nemanta ake da gaggawa, tashi tayi da sauri ganin ance "kije watsapp akwai sako"
gani tayi unknown number ne ya turo mata sakon, buɗe data tayi da sauri yaje watsapp, ta zubawa message ɗin da suke shigowa ido har suka gama shiga kafin ta duba wanda taga new number, gani tayi an turo voice note da sauri ta buɗe ta kure volume tana ji, a wani irin firgice ta diro daga kan gadon ta fita da gudu tama manta wandon dake jikinta ko cinyanta bai rufe ba, ga rigan ma ɗan karami, jin sautin kukan mama tana cewa kada Abdool ya kasheta a rikice tace "yazeeeeeed hanaaan, abbaaaaa, momyyyyyyyy kuzo"
ita kanta batasan yadda akayi ta sauko daga stair ba ta zauna daram a tsakar falon, duk suka fito cikin tashin hankali jin yadda take ihu, voice ɗin ta kara mayarwa baya tayi musu playing, dafa kirji hanan tayi tace "what? Abdool ne kenan ya ɓoyeta?"
cikin tsananin ruɗewa ta tashi zata fita da gudu yazeed ya riketa, fizgewa ta fara tace "ku barni naje na sameshi ya sakemin mamana ni ya kamani"
yazeed ganin tana fizgewa ya kankameta a jikinshi yace "tsaya zamuje yanzu"
yace "hanan kawo hijabinta muje"
hanan da gudu ta haura stair ta ɗauko hijabinta dana ameesha ta fito, sa mata yazeed yayi akan karamin wandon jikinta sannan ya riƙe hanunta yace "muje"
momy dama da hijabi a jikinta ta bisu tareda Abba, a motan yazeed suka tafi, a hanya sai kuka take ta kasa yin shiru.
manal wacce ta tashi daga bacci yanzu ta tashi cikin mika tace "oh my god safiya me kyau, kyayyawan rana"
murmushi tayi ta sauko daga gadon ta ɗauko system nata ta buɗe, tana gani wani me baƙin kaya yasa mask ya rufe fuska ya kwantar da gawan mama yasa bindigan a hanunta sannan ya juya babu wanda ya ganshi ya hau mashin nashi ya gudu, murmushi tayi tace "good job"
ciki ta shiga tana kallon Abdool dake bacci a gefensu Imran cikin natsuwa yake baccinshi, a hankali tace "my handsome husband I love you so much, am sorry zaka ɗan shiga matsala kaɗan but karka damu manal naka tana tare da kai, banson kayi nisa ne dani, gara kana prison zan rinƙa zuwa kullum ina kallonka, zuba ido tayi tana kallo tana murmushi.
ganin motarsu ameesha tayi parking a kofa ta waro ido tace "boom"
ameesha ce ta fito tun kafin motar ta gama tsayuwa, yazeed yace "ameesha"
faɗuwa tayi a kasa ta kara tashiwa tana ganin gawan dake kwance ta kara faɗuwa, da rarrafe ta isa wajen tana buɗe fuskan, a mugun firgice tace "ya kasheta, ya kasheta wallahi, wallahi ya kasheta"
yazeed ya kasa fitowa a motan momy ce ta fito da gudu tana rike ameesha da take neman zama karamar mahaukaciya, hanan tazo itama tana riketa, fizgewa tayi da gudu taje ta fara bubbuga kofan tana cewa "Abdool!!! Abdoolrahman ka buɗe kofan nan"
su abdool dasu Imran duk suka fito suna rige rigen buɗe kofan, ameesha tana ganinshi ta rikeshi tace "saida ka kasheta ka samu kwanciyan hankali? kazo ka kwanta kamar bakayi komai ba"
dukan kirjinshi take, ya kasa gane me take nufi, sai yanzu idonshi ya kai kan mama dake kwance a wajen da bindiga a gefenta, ture ameesha yayi yaje da gudu yana duba mama, da sauri yace "mama? mama?"
su Imran sukazo suma suna bubbugata ta tashi, man yace "Anty ki buɗe ido mana abdool naki ne anan, ki buɗe ido ki kallemu kinga mu duka ne anan"
ganin bata buɗe ido ya ɗau bindigan yana kallo cikin shock, a lokacin ƴan sanda suka karaso domin manal ta tura musu sako da address, tana daga zaune tana kallonsu, zai aje bindigan sukace "hanu sama"
hanunshi ya ɗaga sama yana kallonsu, karɓa bindiga sukayi sannan sukace "waye ya aikata wannan laifin?"
ameesha dake kuka sosai tace "shine"
voice ɗin da aka tura mata ta kunna musu duk wajen sukayi shiru harda ammi da takeji suna saurare, ankwa akasa mishi a hannu aka sashi a bayan mota suka tafi dashi, ya rasa me zaiyi kawai yayi shiru yana bin kowa da ido.
ameesha ta sume a wajen, yazeed ne ya shiga da ita, da kyar suka samu ta farfaɗo, cikin tashin hankali take bama tasan time ɗin da aka fita da mama ba, tana kwance bata cikin hayyacinta, ammi tayi shiru tana kallon ameesha dake yin abu kamar taɓaɓɓiya, har su Abba suka dawo bata nutsu ba saida hanan ta rinƙa yimata karatun kur'ani a kunne sannan ta fara nutsuwa, su Imran dasu fahad suna zaune ne kawai suma basa cikin yanayi me daɗi
_jiddah Ce..._
managarciya