Aurar Da Marayu: Shaikh Rijiyar Lemu Ya Gargadi Ministar Tinubu

Aurar Da Marayu: Shaikh Rijiyar Lemu Ya Gargadi Ministar Tinubu
 
Sheikh Sani Umar Rijiyar Lemo ya yi martani kan cece-kucen da ake yi game aurar da marayu mata a Niger. 
Shehin malamin ya caccaki Ministar harkokin mata, Uju Kennedy-Ohanenye kan matakin da ta dauka game da shirin aurar da matan. 
Rijiyar Lemo ya bayyana haka ne a cikin wani faifan bidiyo inda ya ce wannan ba hurumin ta ba ne kuma bata daga cikin Musulmai ko kabilar Hausawa da za ta san al'adunsu.
  Sheikh Rijiyar Lemo ya ce a lokacin da aka hallaka iyayensu(marayun da za a yiwa aure) da sauran mutane a Arewacin Najeriya ba ta yi musu jaje ko tallafa musu ba, ba ta damu da su ba sai yanzu za ta tsoma bakinta kai, bayan ba ta da ilmi kan addini da al'adun Hausawa. 
Ya bukaci shugabannin musamman Musulmai a wannan gwamnati da su taka mata birki saboda ba za su amince da akida da suka sabawa addini da al'adu ba.
"Wannan Minista ba Musulma ba ce kuma ba jinsin Hausa/Fulani ba ce ko ƴar Arewa ba,  ba ta san al'adunmu da addininmu ba, wannan ba aikin  aka dauke ta ta yi ba." "Lokacin da ake hallaka iyayen yara a Zamfara da Katsina da Kaduna da ita kanta Neja ba ta tallafa musu da abinci ko kudi ba, kuma ba ta yi musu jaje ba."
"Amma yanzu tana cewa kada a kuskura a taimaka wurin auren ƴaƴansu, wannan ta shiga hurumin da bai shafe ta ba, saboda bata san al'adunmu da addininmu ba." - Sheikh Sani Rijiyar