Farfesa Isah Ali Pantami--- Kogi ne Matattarar Ilimi---- NUC

Farfesa Isah Ali Pantami--- Kogi ne Matattarar Ilimi---- NUC

Daga Habu Rabeel, Gombe.

Babban sakataren hukumar kula da manyan jami'oin Najeriya Nigerian Universities Commission (NUC) Farfesa Abubakar Adamu Rasheed, shi ya bayyana Farfesa Isa Ali Pantami, a matsayin Kogi Matattarar Ilimi bisa ga bai wa da fikirar da Allah ya yi masa.

Farfesa Abubakar Rasheed, ya bayyana hakan ne a wajen wani taro na Mataimakan Shugabanin jami'oin gwamnati na Najeriya da aka gudanar a babban birnin tarayya Abuja a ranar 21 ga watan Yuli na wannan shekarar, yace ya jinjinawa Farfesa Pantami akan bai war sa.

Yace yasan Farfesa Isah Ali Pantami, sosai haziki ne domin akwai wata rana da za'a yaye dalibai a jami'ar Tarayya ta garin Minna Shugaban Najeriya Muhammad Buhari, ya tura shi ya wakilce shi amma ganin Pantami na garin a lokacin yace shi yafi da cewa ya wakilci shugaban kasa a matsayin sa na Ministan Najeriya.

" A wannan wakilci na Pantami ya cika da mamaki domin yadda ya gabatar da mukala a wajen ko wa ye ne iyaka kenan"

Farfesa Rasheed, ya kuma ce wata rana Dansa ya gaya masa cewa yana mamakin Pantami, idan ya karanta takarda sau daya sau biyu duk yawan ta zai hadda ce ta.

Ya kara da cewa tun kafin ya Zama Farfesa Isa Ali yake da bai wa ta musamman har zuwa yanzu da ya zama Farfesan farfesosi.

A cewar sa ba kowanne Farfesa ne zai yi kamar Pantami ba dan haka daga yanzu ya zama Distingushed Professor.

Ya kuma ci gaba da cewa a mukalar da Isah Ali ya gabatar  sanda kowa a wajen ya kwankwadi ilimi ya koshi domin ya fito da tsari na zamani kan tsare-tsaren darussan da ake koyarwa a jami'oin kasar nan zuwa hanya ta zamani.

Sakataren, ya yi amfani da wannan damar ya kara jinjinawa Farfesa Isah Ali Pantami kan mukalar da ya gabatar da ka ba tare da wata takarda a hannu ba duk wanda ya halarci taron ya san Farfesa ya ma wuce kogin ilimin.

Sannan sai ya hori shugabanin jami'oin da cewa su tattara bayanan na Pantami waje guda a buga a ko a turawa mutane kai tsaye a email din su dan su dinga nazari akai suna kara samun ilimi.

Daga nan sai yace kowanne Malami a jami'a yana alfahari da Daliban sa masu hazaka amma shi Farfesa Pantami Daliban ilimi ne a ko'ina suke alfahari da shi.

A bangaren bunkasa tattalin arziki ta hanyar sadarwar zamani Babban Darakta na Galaxy Back bone Farfesa Muhammad Bello Abubakar, ta bakin Maitaimaka masa a bangaren sadarwa Tasiu Mohammad Pantami yace arzikin Najeriya ya bunkasa sosai 

Yace Isah Ali Pantami, Minista ne da ba'a taba yin kamar sa a tarihin Najeriya, kuma ya bar tarihin da ba za'a taba mantawa da shi ba.