Home Uncategorized Dangote ya yi ritaya a matsayin shugaban kamfanin sa

Dangote ya yi ritaya a matsayin shugaban kamfanin sa

7
0

Aliko Dangote ya yi ritaya daga matsayin Shugaban Kwamitin Gudanarwa na kamfanin sukari mai suna Dangote Sugar Refinery PLC,  wanda hakan ya kawo karshen jagorancinsa na tsawon shekaru 20 a kamfanin.

Jaridar PUNCH ta rawaito cewa ritayar tasa za ta fara aiki daga ranar 16 ga Yuni, 2025, bisa wata sanarwa da sakataren kamfanin, Temitope Hassan, ya sanya wa hannu a ranar Laraba.

Dangote, wanda ya kasance shugaban kamfanin tun daga shekarar 2005, ana danganta masa gagarumar nasara wajen mayar da Dangote Sugar jagora a kasuwar masana’antar sukari a Najeriya, ta hanyar gudanar da manyan ayyukan fadada kamfani da kuma karfafa tsarin shugabanci mai nagarta.

Sanarwar ta bayyana cewa a lokacin shugabancinsa, kamfanin ya aiwatar da muhimman Ayyukan Haɓaka Noma a Jihohin Adamawa, Taraba da Nasarawa, don bunkasa samar da sukari a cikin gida da rage dogaro da shigo da kaya daga waje.

Sai dai an nada Arnold Ekpe, wanda ke matsayin Darakta Mai Zaman Kansa, a matsayin sabon shugaban kamfanin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here