Tinubu Ya Samu Matsala a Arewa, Zulum Ya Shirya Yaƙar Dokar Sake Fasalin Haraji 

Tinubu Ya Samu Matsala a Arewa, Zulum Ya Shirya Yaƙar Dokar Sake Fasalin Haraji 
 
Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno ya yi Allah wadai da dokar sake fasalin haraji da Shugaba Bola Tinubu ya kai majalisa. 
Babagana Zulum ya ce sabuwar dokar ba alheri ba ce ga jihohin Arewa da wasu jihohin Kudu, yana mai nuna adawarsa da dokar a fili.
"Mun yi tur da wannan dokar da aka kai majalisar tarayya, zai kawo koma baya ga Arewa, da jihohin Kudu maso Kudu, Kudu maso Gabas, Kudu maso Yammma. 
"Wannan ba adawa ba ne, wannan wani abu wanda mu a ganinmu zai kashe Arewa gaba daya, saboda haka mun kira Shugaba Bola Tinubu ya duba wannan lamari. 
"Mu abinda muke so yanzu, maganar dokar harajin nan, kar a yi." 
Farfesa Babagana Zulum, ya nuna damuwarsa kan yadda shugaban kasar ke hanzarin ganin majalisar tarayya ta zartar da sabuwar dokar sabunta haraji. 
"Akwai kudurin dokar man fetur da aka kaiwa majalisar, yana nan kusan shekaru 20 kafin aka zartar da shi, me ya sa ake hanzarin zartar da dokar harajin? 
"Mu muna cewa ayi hankali a duba, a tabbatar cewa wannan abun ko mu bama nan yaranmu za su amfana." Gwamnan ya nuna cewa ko da majalisar tarayya ta amince da dokar, gwamnoni ba za su iya biya ba, inda ya ce ko an biya yanzu to nan da shekara daya zai zama masifa. 
A yayin da ya jaddada cewa sabuwar dokar harajin za ta jawo koma baya ga Arewa da wasu jihohin Kudu, Zulum ya yi kira ga 'yan majalisar tarayya. 
"Wannan abun bai nuna cewa muna adawa da gwamnati ba, wannan abun ra'ayinmu ne domin zai mayar da mu baya kamar yadda muka gani.