Sakkwato akwai karancin masaya dabbobi----Alhaji Isa Unno
Alhaji Isa Unno daya daga cikin diloli masu sayar da raguna a babbar kasuwar dabbobi ta jiha wadda ake kira Kara ya bayyana cewa a yanzu kasuwar tana da karancin cinikin dabbobi ga masaya.
Alhaji Isa a tattaunawarsa da Aminiya kan halin kasuwar dabbobi a jiha y ace yanayin Kasuwar Sakkwato ya canja irin yanzu kasuwar da ke kusa ita mutane ke tafiya amma ayanzu ba laifi mutane na shigo cikin kasuwar sai dai ba da yaw aba akwai karancin masaya.
“Amma in kwana uku kamin Sallah z aka samu lamarin ya sauya mutane sun dukufa ga shiga cikin kasuwar domin duk wasu kananan kasuwanni dake kananan hukumomi bas u ci saboda zuwan Sallah.
“Hakan ke sa duk wata hada-hada za ta dawo a kasuwar amma yanzu ana sayen dabbobi amma jefi-jefi kamar ba sallah ke tafe ba,” a cewar Unno.
Da ya juya kan halin da dabbobi suke ciki a jihar Sakkwato ya ce Ragon Layya a wannan shekara yana farawa ne daga dubu 70 zuwa 80 har zuwa sama, Tunkiya daga bakin dubu 50 ne, Shanu dake layya shekara hudu ne zuwa biyar masu wadan nan shekarru za su kai kimanin dubu 700 zuwa 800 su ne masu layya.
Tsadar dabbobi tana faruwane kan tsadar abincin dabbobin da ake fama da shi a kasa da kuma matsalar tsaro domin ba yanda za ka ciyar da dabba da tsada ka zo ka sayar da ita da rahusa, matsalar tsaro ta sanya mutane sun daina kiyo hakan ya sa dabbobi sun katse a kasuwanni.
managarciya