Lukurawa: 'Yan bindiga sun kashe mutane 17 a jihar Kebbi

Lukurawa: 'Yan bindiga sun kashe mutane 17 a jihar Kebbi
'Yan bindiga da ake zargin Lukurawa ne sun kashe mutane 17 a wani hari da suka kai a garin Mera karamar hukumar Augie a jihar Kebbi a jiya Jumu'a domin satar shanu.
Wani da ya nemi a sakaya sunansa ya ce mutanen sun shigo garin Mera da misalin karfe daya na dare suka saci shanun mutane da yawa anan ne mutane suka yi kokarin kwato dabbobin a harbin mai uwa da wabi ne suka kashe mutane 17, an yi wa 15 sallah a lokaci guda a yau Assabar  daga baya aka ga gawar mutum biyu an yi masu sutura suma.
"Mun yi bata kashi da su ne mun jikkata wasu daga cikin mutanen su, sai dai sun tafi da shanu da 'yan uwansu da suka samu rauni, haka muma wasunmu sun samu rauni, an kai su asibiti."
Ya ce garin baya fama da matsalar tsaro yanzun ne da wadan nan 'yan bindigar suka shigo har suka tafi da shanunmu bayan sun kashe al'umma.
An yi sallar jana'izar mutanen wadda mataimakin Gwamnan jihar Kebbi Sanata Umar Abubakar Tafida da Sarkin Argungu Sama'ila Muhammad Mera suka halarta.
Bayan kammala yiwa margayan sutura mataimakin Gwamna ya tabbatar da faruwar lamarin ya kuma mika ta'aziyarsa ga iyalan mamatan tare da alkawalin hukunta wadanda suka yi wannan aika-aikar.
Ya ce gwamnatin jiha za ta yi aiki sosai da jami'an tsaro don tabbatar da irin haka ba zai sake faruwa ba.
Sarkin Argungu ya nemi al'umma su hada kansu a rika bayar da bayani abin da ba a gamsu da shi ba a wajen jami'an tsaro don a tabbatar da an kare jama'a.