Dokar Haraji: Sanatocin Arewa Sun Yi Ganawar Sirri Bayan Kudirin Ya Tsallake Karatu na 2 

Dokar Haraji: Sanatocin Arewa Sun Yi Ganawar Sirri Bayan Kudirin Ya Tsallake Karatu na 2 

Sanatocin Arewa sun yi wata ganawar sirri a ranar Alhamis bayan kudurin dokar sake fasalin haraji ya tsallake karatu na biyu a zauren majalisar dattawa. 

Legit Hausa ta rahoto cewa dokar sake fasalin haraji da Shugaba Bola Tinubu ya gabatar na ci gaba da shan suka, inda dattawan Arewa suka nuna adawa da ita. 
Jaridar Punch ta rahoto cewa sanatocin Arewa sun gudanar da taron ne a dakin taro na 301 da ke zauren majalisar, kuma sun shafe kimanin awanni biyu a ciki. 
Sai dai, ba a bayyana cikakken bayani game da tattaunawar ba, domin shugaban kungiyar Sanatocin Arewa, Sanata Abdulaziz Yar'Adua, ya ki yin magana a kai. 
Sai dai ana tunanin tattaunawar ba za ta rasa nasaba da yadda gwamnoni, sarakunan gargajiya, dattawa da masu ruwa da tsaki a Arewa ke adawa da dokar harajin ba.
A ranar Alhamis, majalisar ta umurci kwamitin kudi na majalisar ya gayyaci gwamnoni, sarakunan gargajiya da sauran masu ruwa da tsaki don jin ra'ayinsu kan dokar. 
Kafin wannan ne aka ce 'yan majalisar sun shiga ganawar sirri domin tattauna batutuwan dokar a sirrance. 
Bayan dawowarsu daga ganawar ne shugaban masu rinjaye, Opeyemi Bamidele (APC, Ekiti Tsakiyar), ya jagoranci muhawarar kan dokokin.