Tinubu Ka Ba Mu Kunya----Shugaban APC  

Tinubu Ka Ba Mu Kunya----Shugaban APC  

Shugaba a APC Ya Rubutawa Bola Tinubu Wasika, Ya ce ‘Ka Ba Mu Kunya’ a Mulki  

  Tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar APC, Salihu Mohammed Lukman ya rubuta budaddiyar wasika zuwa ga Bola Ahmed Tinubu. Daily Trust ta rahoto Salihu Mohammed Lukman ya na cewa ba haka aka yi tsammani daga Bola Tinubu da ya hau mulki a Mayu ba.

Alhaji Salihu Mohammed Lukman ya fadawa Mai girma shugaban Najeriya cewa alamu sun fara nuna gwamnati mai-ci ta fara da kafar hagu. 

A cewar ‘dan siyasar, majalisar gudanarwa watau NWC ta APC ta samu kan ta a irin yanayin da jam’iyyar ta shiga na tikitin musulmi da musulmi. 

Goyon bayan Abdullahi Umar Ganduje da Ajibola Bashiru su ka samu daga shugaban kasar ya jawo shugabancin APC ya na hannun musulmai biyu. 

Business Day ta ce Lukman ya ce zargin da ake yi wa jam’iyyar na maida kiristoci saniyar ware ya jawo rashin jituwa a APC da kuma cikin al'umma. Baya ga haka, tsohon shugaban jam’iyyar ya ce Bola Tinubu ya ki kyale Umaru Tanko Al-Makura ko wani a Arewa ta tsakiya ya gaji Abdullahi Adamu. 

A game da zaben Ministoci, Lukman ya na ganin gwamnatin Bola Tinubu ba ta dauko irin mutanen da za su taimaka mata wajen cin ma manufofinta ba. 

"Abu na uku shi ne yanayin wadanda ka ke ba aiki. Mai girma, a duk lokacin kamfen zaben 2023, daga cikin abin tallata ka shi ne ka iya nemo kwararru."