An Gabatar da Kara kan manyan laifuka 853 cikin wata Takwas a Kebbi

An Gabatar da Kara kan manyan laifuka 853 cikin wata Takwas a Kebbi
 
 
Kwamishinan shari'a na jihar Kebbi Dakta Junaid Bello Marshall a taron manema labarai a satin nan ya sanar da nasarorin da gwamnatin Gwamna Nasir Idris ta samu a cikin wata 8.
Dakta Marshall ya ce ma'aikatar shari'a tana da ma'aikatan shari'a 27 gaba daya amma da shigowar gwamnatinsu Gwamna ya amince a dauki karin lauyoyi a ma'aikatar.
 
Kwamishina ya kara da cewa ma'aikatarsa tana sane da kararrakin manyan laifuka 853 da aka gabatar.
Haka ma akwai wasu shari'u 80 da aka daukaka Kara dake gaban babbar kotun Kebbi, da wasu 70 dake gaban kotun daukaka kara da kotun koli ta kasa. Akwai wasu 200 da mun mayar da su ga hukumomin da abin ya shafa, domin wasu shari'un sun lalace don babu shedu wasu kuma an hukunta masu laifin.
 
Kwamishina Marshall ya jinjinawa Gwamna yanda ya raya ma'aikatar in da ya Sanya kayan zama da Kawo kayan bincike na zamani a laburari tare da Komfutoci na zamani guda 40 da sauran kayan bukata.
Ya ce Gwamnan ya amince da daukar nauyin lauya 10 domin su yi karatun digiri na biyu a jami'ar Ahmadu Bello ta Zariya, an kuma gyara reshen ma'aikatar dake Argungu da Yawuri ya kuma daga alawus na lauyoyi daga miliyan 13.9 zuwa miliyan 70.
 
Ya ce Gwamnan ya biya kudin karatun dalibai 'yan asalin Kebbi dake karatun shari'a a makarantu daban daban, bayan daukar nauyin taron bita da samar da wurin zama ga sabbin ma'aikatan Shari'a da biyan bashin da  alakalai ke bin gwamnatin Kebbi wanda yawan kudin yakai biliyan daya.
Dakta Marshall ya ce suna kan aikin samar da kudirin doka da zai samar da jami'an tsaron jihar Kebbi, za su yi la'akari da bukatar mutane da samar da  tsari kan tarbiya da hakar ma'adinan jiha.
Ya ce ma'aikatar shari'a ta shirya gabatar da kudirin doka 18 gaban majalisar dokoki don yi masu gyaran fuska a Kawo Gwamna ya sa hannu su zama doka.