Tambuwal ya ɗauki matakai domin kawo ƙarshen rashin tsaro a Sakkwato

Tambuwal ya ɗauki matakai domin kawo ƙarshen rashin tsaro a Sakkwato

Matsalolin tsaro da yankin Arewa maso yamma ke fama da shi Gwamnan Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ya yi koyi da takwarorinsa na Zamfara da Katsina wurin daukar matakai da ake ganin za su taimaka wajen magance matsalar tsaron da ake fama da shi a yankin.
Gwamnan a takardar da Kwamishinan yada labaransa Alhaji Isah Bajini Galadanci ya karantawa manema labarai amadadinsa da ya sanya hannu a takardar  ya ce matsalar tsaro da ke addabar jihar Sakkwato abin da ya yi sanadin rasa rayukka da muhali hakan ya sanya za a takaita zirga-zirga a wasu bangarorin jihar.

Ya ce Gwamna ya aminta da sanya dokar kamar yadda tsarin mulki ya ba shi dama ya ba da unarnin da zai soma aiki nan take daga yau Laraba an rufe babbar hanyar karamar hukunar Isa zuwa garin Marnona don haka mutane su rika bin ta karamar hukumar Goronyo zuwa Sabon Birni, manyan motoci masu daukar itacen kuna a daji an dakatar.
Ya ce an dakatar da cinikin dabbobi a wadan nan kasuwanni a kananan hukumomin  Gada, Goronyo,
Gudu, Ilela, Isa, Kebbe, Sabon Birni, Shagari, Rabah Tambuwal,Tangaza, Tureta da Wurno.
Haka ma an dakatar da lodin  shanu   a Gada, Goronyo, Gudu, Illela, Isa, Kebbe, Sabon Birni, Shagari, Rabah Tambuwal Tangaza, Tureta da Wurno. 
Tambuwal bayan ya hana babur daukar mutum uku a lokaci daya, keke nape kar ya wuce daukar mutum uku, ya hana sayar da tsoffin babura a  kasuwannin garuruwan nan Gada, Goronyo, Gudu, Ilela, Isa, Kebbe , Sabon Birni, Shagari, Rabah Tambuwal, Tangaza, Tureta, Achida, Gande, Gwadabawa da Wurno.

Tambuwal bai aminta a rika sayar da man fetur a cikin Jalka, kuma gidan mai zai sayar da Mai da ba zai gaza 5000 ba, mau babura za su rika tashi daga 6 na marece, su fara aiki 6 na safe, wadan nan wuraren Gada, Goronyo, Gudu, Ilela, Isa, Kebbe, Sabon Birni, Shagari, Rabah, Tambuwal Tangaza, Tureta da Wurno.
Gwamna Tambuwal ya ce dokar sufurin a birnin jiha daga 10 dare ta rika aiki don haka ya yi kira ga mutanen jiha su bayar da hadin kai ga dokokin don a cimma nasarar dawo da zaman lafiya.
Ya ce gwamnati na daukar mataki ne domin samar da tsaron al'umma kar maharan su bats komai a jihar.