Gwamnatin Zamfara ta yi Karin haske bisa ga dokar hana zirga zirga da rufe kasuwannin sati sati
Daga Aminu Abdullahi Gusau.
A yaune gwamnatin Zamfara ta yi karin haske dangane da dokar da ta saka na rufe kasuwanin sati sati a duk fadin jihar, da haramta yawo da dare da kuma sayar da man fetur a wajen da a hedikwatar karamar hukuma ba.
Da yake yiwa manema labarai bayani, kwamishin shari'a na jihar ta Zamfara Barista Junaidu Aminu, yace gwamnati Bello Muhammed Matawalle ya saka wa dokar hannu kuma ta fara aiki nan take.
Kamar yanda dokar take, an hana zirga zirga daga karfe shidda na dare zuwa shidda na safe, an hana daukar fasin ja fiye da daya a sama Babur, an kuma hana matafiya ratsa jihar Zamfara daga bakin karfe goma na dare sai dai duk mai motar da ya shaiga Zamfara ya kwana a duk inda ya tsinci Kansa.
Barista Junaidu, ya tabbatar da cewa an kaddamar da kotun tafida gidan ka domin hukunta duk wanda ya karya wannan dokar.
Ya kara yin bayani game da wuni wuri da ake kira garejin mailaina inda ake zargin maboyar yan ta'adda ne, inda yace am bada umurnin duk wanda ke kasuwan ci a wurin ya kwashe kayan sa ko kuma ya hadu da hushin hukuma.
Daga nan sai yayi gargadin cewa masu shiga Daji don sawo gawayi ko iccen wuta suma an haramta masu, saboda suma ana zargin su da kai wa yan ta'adda miyagun kwayoyi da abinci da kuma kayan maye daban daban.
"Saboda haka wallahi mai girma gwamna yace wannan dokar ba sani ba sabo, domin ko waye ya karya ta zai hadu da hushin hukuma, amma akwai wasu ma'aikata da dokar bata shafaba, kamar ku yan jarida, ma'aikatan Assibiti, dana hukumar kashe gobara.
" Ina son mutanen Zamfara su san da cewa duk wayan nan matakai da aka dauka an dauke sune domin kare mutun cin su da dukiyoyin su, ga hannun wayan nan miyagun mutane, idan abun ya saukaka za'a dage dokar".inji Barista.
managarciya