Shugabannin PDP sun lallashi Jonathan kar ya bar Jam’iyyarsu

Shugabannin PDP sun lallashi Jonathan kar ya bar Jam’iyyarsu
Shugabannin PDP sun lallashi Jonathan kar ya bar Jam’iyyarsu

Shugabannin babbar jam’iyyar adawa ta PDP sun ziyarci tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan domin roƙonsa ya ci gaba da zama a jam’iyyar sun lallashe sosai da nuna masa muhimmancinsa a tafiyarsu.
Mukadashin shugaban jam’iyyar, Yemi Akinwonmi ne ya jagoranci tawagar da ta ziyarci Jonathan a gidansa da ke Abuja.

Duk da cewa tawagar ta yi ganawa da tsohon shugaban a cikin sirri, wasu rahotanni na cewa sun tattauna kan rigingimun cikin gidan jam’iyyar da kuma neman shawarwari kan yada za a lalubo bakin zaren ganin yanda PDP ta faɗa cikin rikici a tsawon lokaci, kafin a samu bakin zaren.
Sannan wata majiya na cewa tawagar ta nemi alfarma wajen Jonathan kan kada ya fice daga jam’iyyar, sannan ta nemi ya kasance tare da su da shigar da kansa lamuran jam’iyyar domin ganin sun kai ga nasara.
Jonathan ya ƙauracewa halartar taron PDP da jimawa abin da ake ganin yana nuna rashin gamsuwarsa da yadda tafiyar PDPn take.

Ziyarar ana ganin tana iya sauya wasu lamurra domin har yanzu tsohon shugaban bai taɓa wata magana dake nuna alƙiblar siyasarsa.