Mai Martaba Sarkin musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar ya ba da umarni ga al’ummar musul,mi da su fara duban watan Safar daga gobe Lahadi 29 ga Muharram dai da 4 ga Agustan 2024.
Sarkin musulmi ya ba da sanarwar ne a wata takarda da Wazirin Sakkwato Farfesa Sambo Wali Junaid ya sanyawa hannu ya ce an nemi mutane su dubi watan Safar a Lahadi, duk wanda ya gani ya kai rahoto a wurin hakimi ko uban kasar da ke kusa da shi domin sanar da mai martaba Sarkin musulmi.
Ya roki Allah ya taimake su ga aikin addini da suke yi.






