Hukumar Zabe Na Aiki Da Ta Sadarwa Don Kaucewa Cikas Yayin Tura Sakamakon Zabe A 2023

Hukumar Zabe Na Aiki Da Ta Sadarwa Don Kaucewa Cikas Yayin Tura Sakamakon Zabe A 2023

Farfesa Mahmood Yakubu, Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ya ce tuni hukumar ta dukufa wajen warware matsalolin sakamakon zaben da ka iya tasowa daga gurare marasa hanyar sadarwa.

Shugaban na INEC ya bayyana haka ne a wani taron tattaunawa na kwana daya da ‘yan jarida a Legas a yau Juma’a.
Wannan batu da shugaban INEC ya yi ya biyo bayan rade-radin da ƴan Nijeriya ke yi kan yiwuwar amfani da tsarin tantance masu kada kuri’a, BVAS, a wuraren da ba su da hanyar sadarwa mai kyau, saboda ya dogara da tsarin sadarwa na yanar gizo.
Yakubu ya ce hukumar za ta gana da Hukumar Sadarwa ta Najeriya, NCC, a ranar Talata, kan batutuwan da su ka shafi sadarwar wayar salula da ka iya shafar watsa sakamakon.
Ya ce kar ƴan Najeriya su ji tsoro game da tasirin watsa sakamakon zabe a babban zaben 2023 ta hanyar amfani da tsarin BVAS.
Shugaban na INEC ya ce suna tattaunawa da NCC don tabbatar da cewa za a watsa sakamakon zabe ba tare da wata matsala ba a zaben 2023.
“INEC ta fara aikin gano guraren da babu sabis kuma muna aiki don ganin ba za a sami matsala ba.
“Muna aiki tare da NCC don gano gurare da ba sa samun sabis.
"Muna tabbatar da aiki tukuru domin mu yada sakamakon zaɓe a fadin kasar nan ba tare da wahala ba," in ji shi.