Tallafin Gwamnatin Sokoto a Noman Riɗi ya yi nasara-----Tambuwal

Sakamakon zuba miliyoyin naira da gwamnartin Sokoto ta yi a harkar Noman riɗi a jiha don bunƙasa noman ya sanya manoman farinciki ga abin da suka samu a noman.

Tallafin Gwamnatin Sokoto a Noman Riɗi ya yi nasara-----Tambuwal
Hanyoyin mallakar miji ga matan Hausawa

Sakamakon zuba miliyoyin naira da gwamnartin Sokoto ta yi a harkar Noman riɗi a jiha don bunƙasa noman ya sanya manoman farinciki ga abin da suka samu a noman.

Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya sanar da hakan lokacin da ya ziyarci rumbu ajiya na jihar Sokoto ya ce Sama da shekara ɗaya gwamnati ta yi haɗin guiwa da gonar Turkish in da aka samar da iraruwan riɗin kala uku da yake da nauyin kilogiram dubu 350 aka rabawa manoma a jiha.

An bayar da mota da takin zamani da babura 10 don dai a ƙara buɗa haujin.
Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya ce a bayyane yake kwalliya ta biya kuɗin sabulu ga abin da aka yi kuma gwamnati za ta cigaba da taimakawa manoma musamman na riɗi kamar yadda aka yi a shekarar data gabata.

Ya ce a noman riɗi kafin gwamnati ta shiga ciki ana noma Kadada dubu 10 ne amma yanzu da tallafin gwamnati an noma kadada dubu 34, in aka ci gaba da haka a shekarru masu zuwa za a iya noma kadada dubu 91 hakan zai iya baiwa mutum dubu 100 aiki a kowace shekara a jihar Sokoto.