Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar ya bayyana yadda ake bukatar a rika tura mata jami'ar musulci ta Madina domin su karancin fannin likitanci da wasu fannoni da mata ke da karanci a bangaren.
Sarkin Musulmi a wurin taron kungiyar tsoffin dalibban jami'ar Madina da suka shirya Daura domin samar da gurabun karatu ga dalibbai masu hazaka a jami'ar, ya ce mata ne ginshiƙin cigaban kowace al'umma kan haka bai dace a yi wasa da gudunmuwarsu ba.
Wazirin Sakkwato wanda shi ne ya wakilci Sa'ad Abubakar a Assabar a dakin taro na Makaratar hardar Kur'ani ta Sarkin Musulmi Muhammad Maccido ya ce jami'ar musulunci ta mata zalla a Saudiya yakamata a ƙarfafawa mata su je can domin karanta fannin laifi lafiya ganin yanda ake da ƙaramcin mata a fannin.
Gwamnan Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal yana tare da taron a zuci ya jinjinawa tsoffin dalibban jami'ar Maadina da ta shirya wannan Daurar domin samar da gurabun karatun a jami'ar Madina.
Tambuwal wanda kwamishinan ilmi na jiha Bello Guiwa ya wakilta ya ce gwamnati ta shirya kammala tsarin doka don sauya hukumar bayar da ilmin larabci da addinin musulunci zuwa mataki na gaba kai tsaye ta rika karɓar umarni ga gwamna ba wurin kwamishina ba.
116 suka yi karatun maza 85 mata 31
Mushaffa'u Musa Sakataren kungiyar ya ce kalubale da aka samu a wurin daurar bai fi rashin muhalli ba 'muna bukatar muhalli na dindin, mutum 116 ne suka shiga karatun maza 85 mata 31'.
Ya yabwa gwamnati da ta ba su dama suka yi wannan Daurar da aka samu mutane daga kananan hukumomin sakkwato 23 da wasu jihohi, a cikin mutanen da suka ji sanarwar mu kuma suke da sha'awar shiga jami'ar musulunci ta Madina.
Sakataren ya yi kira ga gwamnatin jihar Sakkwatto ta samar da hanyoyi da mata za su rika tafiya kasar Saudiya domin karatu a can wanda hakan yana da alfanu ga cigaban karatun mata a jiha.