2023: Don Allah 'Yan Siyasa Ku Mutunta Junanku a Lokacin Yekuwar Neman Zabe---Farfesa Mansur Sokoto

2023: Don Allah 'Yan Siyasa Ku Mutunta Junanku a Lokacin Yekuwar Neman Zabe---Farfesa Mansur Sokoto

Sanananen malamin addini a Sakkwato Farfesa Mansur Ibrahim Sokoto ya shawarci 'yan siyasa kan su yi harkokin siyasarsu cikin mutunci da mutuntawa a kakar zzaben 2023.

Malamin ya yi kiran ne a lokacin da yake hudubar sallar Jumu'a ta farko bayan sake gyara masallacin jumu'arsa da Alhaji Ummarun Kwabo ya yi, ya ce don Allah 'yan siyasa ku mutunta juna a lokacin yekuwar neman zabenku, "ku tuna duk da bambancin jam'iyar da kuke da shi ku 'yan uwan juna ne a musulunci, kuma bambancin jam'iya na dan lokaci ne wata rana kuna iya zama abu daya."
Farfesa Mansur ya ce wannan  juma'ar ita ce ta 815 a masallacin nan  tun sanda aka gina shi.
Ya taya Jarman Sakkwato da ya gina masallacin ya kuma jaddada ginar cikin sabon fasali mai kyau. 
"ya a cika alƙawali kan masallacin Jarma  mutum ne mai daɗin zama, yana  da alheri da son aiwatar da shi" a cewar Mansur.
Shattiman Durbawa shugaban kwamitin buda masallacin ya ce Shekara 15 da suka wuce aka gina masallacin yana  daya daga cikin wurare 35 a karkashin kulawar Gidauniyar Jarma UK. Masallacin na da makaranta da gidan marayu.
Shattiman ya ce a kwanan ne za a yi bukin wasu dalibai da suka sauke Alkur'ani su 1500, 800 sun hardace kur'ani gaba dayansa, 
Marayu 7 ne daga cikin wadanda jarma ke kula da su ke cikinsu.
Bukin bude masallacin na hade da aurar da diyan Jarman Sakkwato guda biyu.