Malamai Sun Gudanar Da Addu'o'in Zaman Lafiya A Lokuttan Zaben Nijeriya

Malamai Sun Gudanar Da Addu'o'in Zaman Lafiya A Lokuttan Zaben Nijeriya

 

A  Sakkwato, Majalisar Darikar Kadiriyya, ta Shirya Karatun Kur'ani maigirma, da yin Addu'oin na musamman, domin samun  saukin kuncin Rayuwa, da neman yin zabukka lafiya.

 
Daga Mukhtar A Haliru Tambuwal Sokoto.
 
Ranar litinin 29 ga Rajab 1444AH  20/02/2023, Majalisar Sufayen Dalikar  Kadiriya ta jihar Sokoto, karkashin jagorancin, Khalifa Abdulkadir Jelani Abbas, kofar Atiku Sokoto,  ta gayyaci Daukacin malammai, limamai da sauran mallammai daga Zaurukka,cibiyoyin daukar karatu da ma kungiyoyin Addinin musulunci da ke Sakkwato, uwayen kasa,yan kasuwa,maaikata,Dalibbai,da sauran  Mutanen Gari, inda suka hadu a Masallacin jimu'a, na Mujaddadi Shehu Usmanu Danfodiyo da ke cikin birnin shehu, sun hadu sun gabatar da Safkar Kur'ani maigirma, kana da Addu'oin na musamman daga malammai daban daban da suka halarta tun daga Sarkin Malammai ,Alkalin malammai da sauran limaman jimua da sauran su, domin ganin an yi zabe lafiya an kare lafiya cikin lumana.
Shugaban Majilisar kadiriyya na jihar Sokoto, ne Khalifa Abdulkadir Jelani Abbas Kofar Atiku Sokoto, yayi bayanin cewa abubuwa ukku ne suka sa suka shirya wannan taron , na farko ,"abubuwan da muka tsinci kan mu ciki na tsananin rayuwa,na rashin kudi da tattalin Arziki da Matsin rayuwa" , na biyu Zabukka da ke tafe, Fatar ayi su lafiya akare lafiya,fatar Allah ya zabar muna Shugabanni na gari, ya amintar da mu duk wata fargabar da zata iya Kunnowa, shugabannin da ke saman mulki Fatar Allah ya sa, su safke lafiya, yayiwa sauran jagorori jagoranci. 
"Abu na ukku  rokon daukin Allah akan matsalar tsaro" bayan nan, yayi tuni  cewa akoma ga Allah a dena sabawa Allah domin a yanzu duk wani sabo ana aikatawa dan haka a tubar ma Allah dan samun saukin Allah akan yanayin da ake ciki, kuma a guji cewa wasu shugabanni ne suka jawo muna wannan yanayin "a a mu ne muka jawo ta sabawa Allah da muke yi".